Sashe 11
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sauraren abinda ke wakana cikin gun dinner din,gajiya tsoro kishi da takaici suka mata taron dagi, tun bata gaji ba har ta sare da zaman gashi ba damar fita bare tayi tafiyarta yabi ya kulle matar,zaman jira na k manin awa uku tayi a motar sannan ta fara hango tawagar aliyu Mrs muhammad bello ce [10/16, 12:29 PM] Salma Wa yasan gobe? Written by safiyya Abdullahi musa huguma Tamakar ya manta akwai wata halitta da ke cikin motar ya shigo abinsa driver yaja motar suka bar gun,ganin haka yasa tayi kamar ta tuna masa su sauketa a gida fa sai taga ai ya ma raina wayonta duk inda zai kaita ya kaita,ganin sunyi hanyar gida yasa ta sake tabbatarwa yana sane kenan A daidai qofar gidansu driver yayi parking yana tsayawa tasa hannu ta bude motar tayi ficewarta ba tare da tace masa kanzil ba haka shima baice komai din ba dama kuma tasan ba cewar zaiyi ba bata kuma dada ta da qasa ba maganarsa,ahankali take tafiya saboda kasala da bacci ga takaici da ya rufeta ya dan bita da kallo yana mamakin haqurin da tayi bata ce masa komai ba ua juya ya bawa nasiru umarnin ya ja motar su wuce Kai tsaye gidansu zainab ta tafi don kwanciya kawai take buqatar yi a halin yanzu,dakin da aka basu ta tura ta shiga wasunsu yammatan sunyi bacci wadanda suka rage kuma kowacce na maqe da waya tana tadi kamar yadda farida tabi sahu itama ganin shigowar fadilan ne ya sata katse wayar ta dubeta tace"ya naga kin jima sosai haka"sai kuma ta danyi murmushi tace"um mace da mijinta meye nawa?",tabe baki fadilan tayi ta jawo jakar kayanta ta dauki towel ta kwabe mayan jikinta tadaura ganin haka yasa farida ta gane tambayarta bata da amsa kenan,ta sake dariya bayan taga shigewarta toilet tace"ya fadila tawa......miskili kafi mahaukaci ban haushi Washegari ummi tayi mother's day,cikakkiyar shigar hausawa sukayi ranar don hatta mayafi na atamfa sukayi,kwatsam sai ga momin Aliyyun a gun da mutanenta sunzo wai za ta yi wa fadila nata kamun,gun yayi armashi sosai don kidan qwarya akayi zalla bayan lecture ga amare wadda aka shafe fiye da awa ana musu inda daga baya kuma gun ya karade da waqoqin da irin nasu mamman shata sani sabulu dan qwairo dan indo audu wazirin dan duna da sauransu suma iyaye aka tuno musu da da tunda dama ranar ta iyaye ce, Washegarin ranar sukayi kuma wuni a gida,wata Washegarin kuma ta zamto ranar daurin aure,daurin auren da ya tara jama'a na ban mamaki garin ranar unguwar ba masaka tsinke,jama'a ne tako ina na nan qasar dama maqwaftan qasashe har da na qetare Misalin takwas na daren ranar daurin auren fadila da farida na durqushe gaban umminsu sanye cikin atamfa super England lemon grean ce da pink sai adon fari dinkin riga da zani an nannade masu jikinsu da wata danyar lafaya fara tas mai dige digen pink a jiki,dan kunne da sarqa sai banguls duk na azurfa ne ,babu abinda ke tashi jikinsu sai wani rantsatstsan qamshin turaren humra yar gasken ta bare barin usuli Da fari ummi kasa magana tayi saboda tausayi da qaunar yaran nata sai jimamin rabuwa da zatayi da su,daga baya ta daurw ta musu yar tunatarwa saboda ita damacan koda yaushe mai dora yayanta ce kan tarbiyyar zaman gidan aure ce,ta kammala nasihar tata da addu'a da fatan alkhairi a garesu,umma A'i yayar ummi ta leqo tana cewa su fito angwaye nata jira fa,wani kukan suka sake saki suka ruqunqume ummin suna neman yafiyarta,tace ta yafemusu burinta kawai su zauna da mazajanasu lafiya kada taji kada ta gani shine farincikinta,ana riqe dasu amma suna waiwayowa suna kuka idanunsu a kanta kamar zasu qwace su dawo,itama sai ta kasa jurewa suka sata qwalla duk sai suka karyar da zuciyar kowa sai muhammad shima ya dauki masa kukan da ya bawa mutane tausayi kasa zama yayi yabi yan uwan nasa yana ta kuka kowa ya tausaya mai saboda tunda ya taso suna tare da su ya saba su ya saba gani gashi yau an dauke masa su duka biyun Cikin wata arniyar mota qirar sail akace a shiga da fadila suna qoqarin sa farida a dayar ta riqeta gam tace bata yarda ba saidai a hadasu a mota daya,ganin da gaske take yasa suka sasu a mota gudan,lokaci guda motocin suka tashi suka kuma jeru reras bisa titi tamkar motocin rakiyar shugaban qasa,duk da cewar darene amma duk inda suka bi sai sunja hankalin mutane saboda kyawun motocin,kai tsaye yahaya gusau suka fara nufa inda anan gidan farida yake,a nutse suke shiga gidan saboda ba yara ko daya sai manya da yammata tun la'asar aka kai yara suka gama gani aka dawo da su gida tsarin gidan farida gwanin sha'awa ya burge jama'a da dama atsare ginin yake kana kallonsa kasan sai da aka sa nutsuwa aka fidda masa fasali Sai da suka ajiyeta a bedroom dinta su umman abuja(itama qanwar abba ce)suka sata tayi addu'o'i sannan sukayi haramar tafiya,fadila na nanuqe da farida har yanzu kukan suke sunqi sakin juna harsai da umma a'i tq fusata dama akwai lafiyar fada ta hau sababi tace"ku kunga bamason isknci,kanku aka fara aure ai kowa da haka ya sabatun dazun ake fama da ku ki fito kin noqe to kada ki sake na qaraso dakinann baki fito mun tafi ba"suka sake rushewa da kuka ganin lallai dai rabuwar za suyi,mama sadiya(abokiyar wasan abbansu ce)tazo ta kama fadilan tana rarrashinta tafito da ita tana jiyo kukan faridan kamar yadda itama take jiyo nata Cikin nasarawa G.R.A motocin suka kutsa qofar wani katafaren gida suka tsaya,kewaye yake da dogayen kuma qawatattun katangu da fitulu masu tsananin kyau makeken get wanda saboda tsananin girmansa sai kayi tsammanin qofar shiga garice suka tsaya,duk yawan motocin sai da kyakkyawar harabar gidan ta lamushe su,sai ma suka tashi yan tsurut harabar wadace ta take da haske tamkar rana sai ka rantse da Allah rana ce ba dare ba "Kai jama'a yanzu kamar ba za'a mutu ba?,wannan gidan dai.....inda ni kadai na shigo wlh ihu zan sak na ce gidan yankan kai nazo,kamar ba mutuwa a duniya?"kakarsu fadila hajja gana mahaifiyar abbansu ke wannan santin,su kam me za suyi idan ba dariya ba ,sai da suka nufi sashen fadilan masu yaba kyau da tsaruwar gidan suka dadu,ginine wanda kaf garin kano baifi ka qirga masu irinsa da hannu ba,ginin part hudu ne sai boys quarters makeken lambu swimming pool gun wasanni kala kala,basketball table tennis,football boxing,tokwand da sauransu baya ga haraba biyu da gidan ke dauke da shi harabar farko dakin mai gadi da parking space take dauke da shi,sun dan tarad da jama'a a gidan acan part din samira suna jira a kawota,ba abinda ke tashi sai kida da yan uwanta suka ware mai barazanar fasa kunnuwa ganin haka hajja gana ta hana su koda guda suyi ta shiga gidanta da addu'o'i bakinta wai ni Allah wannan gida naki fadila idan baka da qarfin imani zai iya saka ka manta Allah "gaba dayasai da hajja gana ta sake sa kowa dariya a gun duk da suma sun lalace ne gun kallon tsaruwar gurin nata falone two in one wanda kan ka shigo main falo akwai varender a farkon sashin sannan ka tadda falon,dukka falukan sun qawatu da kayan qyale qyale na falo babba da qaramim falon kowanne ansa masa abinda falo ke buqata ba abinda aka rage masa,acikin main falon anan daga hannun damanka matattakala ce masu fadi guda hudu zaka taka ka haye gun dining wanda ke daume da wasu hadaddun labulaye masu kacar kacar anan qofar kitchen s dinta take wanda duk wayewarka sai quyancinka ya fito,gaban gun dainin kadan wata yar qoface mai kyau ta glass wadda ke dauke da corridor shimfide da lallausan carfet da hadaddun labulaye dakunan bacci ne guda uku daya furniture ne yan Saudi pink da purple daya dakin kuma yan italia ne ash da pinch yayin da daya dakin kuma aka malaleshi da carfet da manyan tuntuna aka zagayeshi da labulaye masu shegen kyau aka rarrataye mata kayan kaba da kumbuna tamkar jeran qauye sai wani dan gado irin na qauye mai rumfa amma wannan an zamanantar da shi kowanne daki da toilet dinsa sai public toilet dake varender da kuma wani a falo,daga kitchen akwai qofa da zaka zagaua bayan part dinka(ventilation)wanda akayi dan qaramin lambu da wata rumfar bunu sai yar qaramar qorama da aka qirqira da doguwar kujera ta siminti qwaya daya,a falo aka ajiyeta,ido kam ya raja'a da kallom kyawun gidan,sanyi a c da qamshin freshener ya game ko ina ga qamshin sabunta,gidan ya kaure da hayaniyar yammata dake ta zuba santi da yiwa kansu fatan samun koda makamancin wannan gidan ne, Wata hayaniya da suka ji ta kunno kai gidan ya saka su yin shiru suna sauraron daga ina take?,guda ce da aka cakudata da kirari iri iri hafe da habaice habaice"taka lpy uwar gida sarautar mata,isaahshiyar mace a gidan aliyu maitama ,eh anqi Allah yaso,qaryar mahassada ba zasu iya da ke ba wallahi sama ta yiwa yaro nisa saidai ya tada kai yayi kallo,an buga da ke an barki wlh yarinya ko yar sankin santanbul ce kinfi qarfin ta kara da ke saidai tayi iya nata salon ta haqura," hakane ya tabbatar musu masu rakiyar samira ne mama sadiya suka hana kowa fita har suka qaraci ahewarau da shegantakarsu suka shige da ita,zuwa wani lokaci kuma sautin sabon kida na kujerar tsakar gida ya karade gidan tamkar wani club,Allah ya kayuta abinda suka ce kenan Qarfe tara aka soma kwashe yammatan ana maida su kafin tara da rabi gidanta babu kowa,kadaici ya kama fadila,tsoro ya cikata,bata jin sautin komai sai hayaniya da kidan yan uwan samirah,zuciyarta tayi rauni sosai tunanin irin zaman da zatayi a gidan take,Aliyunta bai sonta,kishiyarta kuwa salon da ka rakota da ahi ya tabbatqr mata ba zaman lafiya tazo ayi da ita ba,hawaye ya balle mata zuciyarta kaar tayi tsalle ta fito saboda zullumi da radadin da take mata Horn din motoci ya sake cika gidan,ta daga kanta ta kalli agogon bangon dake falon sha daya na dare ya nuna mata ba shakka angone da abokansa suka shigo zuciyarta ke gaya mata haka,sannu taji hayaniyar jama'ar