Sashe 72
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
2 Kai kawo take a bangaren nata don tuni aliyyu ya sawwaqe mata zuwa nasa bangaren anan bangaren nata yake yada zango har ya kammala yi mata kwanakinta,yayi hakan ne don hanata yin aiki Wanda ta saba da shi Duk ran girkinta sai ta qalqale bangaren nasa da su suke barinshi babu kintsi Amma Duk da hakan bata fasa Duk wa ni shirye shirye na karbar mai gidan nata duk ranar girkinta,yayi mitar yayi fushin har ya gaji,ta Riga da ta saba bazata iya zaman ba,bata jin nauyin da tayi,uban cikinta bai damunta Kuma bai hanata duk wani abu d ya kamata ba,sosai aliyyu ke yabawa j rumta da juriyarta kamar yanzun ma ta kammala komai,sanye take cikin wata gown mai azabar kyau,budaddiya ce sosai daga qugu zuwa qasa,hakan yasa bata takurawa turtsetsen cikinta ba sai damar fitowa ma da ta bashi,yayi das a jikinta,qaramin hannu ne da rigar,ta tattara gashinta a tsakiyar kanta ta daureshi da ribbon Kalmar rigar,fuskarta tayi fayau tayi kyau cikin simple makeup, sai qamshin nan nata take zubawa, Ta jita da niyyar shiga kitchen don dauko banana taji s llamarshi yavshigo parlour din nata hancinsa na sheqar daddadan qamshinta,da sauri suka nufi Kuma kuwa na qoqarin tar bar dan uwansa,shi ya soma nasarar cimmata ya rungumeta ta bata yana sansanar wuyanta cike da farinciki Fuskarta qunshe da murmushi tace"Baka da dawowa gida mijina" "Yauwa matata abar alfaharina"ya mayor mata cikin salon qauna da kulawa,sunfi kusan mint I biyar a haka sannan ta juyo da niyyar amsar jakarsa su qarasa daki,zullewa yayi yana noqe kafada"naqi wayo nan naki,a waysnce fa kike Karya min doka daya bayan daya,bayan na hanaki dawainiya da ni" Murmushi ta saki,ya Dora lebensa a goshinta ya sumbaceta Qoqarin ta rage masa kayan jikinsa take don ya samu yashiga wanka Sam ya hanata ta gajiyar kama hannuwanta ya zaunar da ita gefen gado,tana kallonsa har ya gama ya daura towel ya shige wanka ,tuni ya tadda ta ta fiddo masa da kayan da zai sa ta feshe masa su da turare,ya gama shiryawa tsaf sanna ta taka masa ya fice sallah mas i ita Kuma ta koma ta tayar da tata Sai da ta cika masa ciki da abun ci shi Kuma ya ci ka mata nata da ayaba yana tsokanarta ta zama qanwar monkey, bata kulashi ba sai da ta qarasa cinyewa abarta sannan ta taqarqare ta tureshi ta haye kansa "Wayo jama'a wayo mummy 'yar lukuta maman baby z ta karyani a kawo ag ji"ya fada yana qyalqyala dariyar tsokana,ta turo baki"kyau sai ka gayawa aya zaqinta" "Wayo 'yar matata ki taimakeni ki dagani kada nayi amai "To zan daya ka amm kan sharadi day "Naji fadi indai zaki dag ni nidai"yana riqe da cikinsa yana qoqarin boye dariyarsa hade da yi mata gw lo a fakaice "Ni ka yima gwalo?"ta na nu kanta da danyatsanta gami da shagwabe fuska,dariyar da yake boyewar ta subuce ta fito "A'ah,ni da baby na da yake ciki fa muke wasa"ta kalli cikin nata sai aliyyun ya bata d riya,sai ta sauka tana ce wa"sharadina kamin doki"tuni kafin ta qarasa ya juyo mata bay n nasa"maza hau,kada ki sauka har sai kin gaji da ka ki"ta tattare rigarta tana shirin hawa salima t yi knocking,hakan yasa fadila sakin rig rtata ta koma saman kujera ta zauna,da qyar s lima ta samu ta hadiye wa ni dunqulallen Abu mai zafi da ya tokare mata maqoshi,a duniya ta tsani ta bude ido taga fad ila dauke da cikin nan a jikinta,ji takeyi da ta dunga ganin Fadila da shi ta gwammace ta bude ido ta taga baqin kumurcin maciji Babban Abu na gaba d ke tayar mata da hankali,so qauna kulawa m su nauyi da take gaji gu aliyyu akan Fadila da cikinta,ta sani tayi sake Kuma ta barar da damarta,ta kuma bar kari tuni ran tubani dumbin kulawa da tarair ya babu wadda bata Samu ba guri Aliyyu,tuni y bana mata hanya qwaya daya da zata sake samun damar mallakeshi shine ta hanyar cika masa gida da yara amma sai ta gaza yin hakan,ta watsa masa qasa a ido,a yanzun tana jin shiryawa yin hakan,ta shirya kaw r da duk wani Abu da zai zama mata shamaki tsakaninta da Aliyyu,Samira ba matsalarta bace lamarint mai sauqi ne bata dameta ba kamar yadda Fadila ta tsole mata ido....... (09063329635 SMS only pls) *Mrs Muhammad ce [12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed *WA YASAN GOBE?......* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *part 3* 2 Ta qaraso falcon tana qaqalo murmushin dole "Uwar biyu"ta sima ce wa da fadilan "Maman biyu"fadilan ta mayar mata,ta kalli aliyyu dake zaune saman carfet ta zube a gabansa tana masa nacin kallo,qaunarsa na fisgrta tana ara mata qaimi kan qudirinta "Dear barka da warhaka"fuskarsa sake ya amsa mata,ta turawa Fadila flask kamar koyaushe"ga wainar fulawa nan nasa an miki, itakam Fadila abun na daure mata kai,babu Ragnar Allah da zata fito ta fadi ba tare d Salima ta kawo mata wa ni abun ba,fara'a da kulawa take nuna mata,sai dai dan jarida da lawyer ba wasa bane,can qarqashin murmushinta fara'arta da kulawarta fadilan na tsakulo wa su yanayi boyayyu kan fuskar saliman,Saidai ita taimakon da Allah yayi mata cikin nata ba mai cite cite bane idan har taci ayabarta ta jiqa zobonta ta share to shikenan "To na gode"kawai fadilan tace, ta Daki remote ta qaro sautin t.v tare da maida hankalinta kai,saboda jin wani kishi na taso mata yadda aliyyu ke hira da salima cikin sakin jiki ta soma ka ranta "hasbunallahu wa ni'imal wakeel",Samira ce ta shigo gamida ce wa"sllama" kanta tsaye ta nufi kusa da Fadila ta sauna don Neman magana,ta kalli aliyyun yayi da shi din ma ita yake kallo ,cikin ransa yana fadin"can za mutum sai Allah"baar doguwar Riga ce a jikinta kanta babu ko kallabi,d slipper sonta ta shigo har tsakar falo ,hannunta Kuma ga ragowar miya da maiqo nan,ya sake fadin "yanzun haka qila ta taho har nan kenan" "Gani,ina zaune zan fara cin abinci ka kirani,har na fara ci naga waccar ta taho bace Gwara na haqura da abincin inzo inji kake faruwa kada ayi b bu ni,ko a yimin munafurci a cuceni ganin bani gun"sai Kuma ta maida kanta gun Fadila dake gefanta"ummm,anata mana Kallon banza ko"ta sani sarai da ita yake don ta saba gaya mata haka,wai tana mata Kallon banza tana ganin zata haihu sau tari dariya Samira ke bata idan ta fadi haka,don ita dai bata ga wa ni Kallon banza da take musu ba,sai bata fiya damuwa da shirmen ta ba,bata da qullaci kanta tsaye take magana,haka idan zata ai kanta kanta tsaye take fadi ba boye boye Maganar aliyyu ce ta dau ke hankalinta daga kan fadilan "Jibi insha Allahu zamu wuce umra,za muyi sati biyu da yarda Allah"sai ya bude wa ni file dake Ajjiye kusa da shi ya ciro passport guda biyu ya miqawa salima da Samira,wani uban ihu da tsalle samiran tayi sai gata ta dire a gaba aliyyu,ta ruqunqumeshi,tuni har ta shafe masa ragowar miyar hannunta "Da gaske don Allah sweet aly,za muje saudiyya,wayo dadi zamu keta hazo"sumbatun murna ta dinga yi,don kafin aurensu ya mata alqawarin fita honeymoon da ita har ta saka rai sosai don bata taba barin nijeria ba,sai Kuma ta barar da damarta Salima ma murnar take yayin da Fadila tayi kamar Batasan me ake ba,don ta tsammaci zai miqo mata nata passport din tunda yana guri sa,a hankali ya maida idanunsa kanta bayan fitarsu,ko motsi bata yi ba tana zaune a inda take kamar yadda taqi furta komai "Babyyyy"ya kira ta ta juyo ta kalleshi,sai Kuma qwalla ta ciko idanunta,ya miqe tsam ya iska Kujerar da take kai "Baby.......kuka?"kamar jira dama take sai kawai ta rushe da kunya "Subhanallahi"yace ya kwantar da ita kan cinyarsa,a hankali ya dinga shafa gashin kanta da yasha gyara yana jin sautin kukanta na sauka a kunnensa,bai hanata ba don yasan ba yin kanta bane sai da ta gama ta qoshi har tana sakin ajiyar zuciya sannan yace mata"baby me ya faru erhmmm?" "Shine zakayi tafiyarka umra kai da kayan ka wato ni a barni a gida ko?" Murmushi ya saki mai dan sauti,ai kuwa sai ta sake qufula "Dariya ma kake mini?ai dole Kayi dariya saboda yanzu bani da mamora kenan"sai ta kuma sakin kuka,masifa ta hau zazzaga masa da bala'i,shi kam ma sakin baki yayi yana kallon dan qaramin bakinta daketa zazzaga masifar yarda qoqarin qwacewa daga jikinsa,sai ya hanata ya matseta a jikin nasa har sai d ta gaji don kanta tayi shiru,sai Kuma ta dinga sakin ajiyar zuciya alamun ta fara sauka Yana dagota yaga tuni Ashe bacci ya dauketa,murmushi ya saki ya dagata cak ita da uban cikinta ya kaita bedroom cikin dabara ya suya mata kayan bacci ya gyara mata kwanciyarta sannan ya dawo parlour ya gyara gun d suka ci abun ci ya hada kwanukan ya wanke mata su tas,don yasan matuqar suka kai safiya saita wanke kafin ta hada breakfast *Mrs Muhammad ce [1/28, 7:56 PM] My Mom: *WA YASAN GOBE?.....* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *part 3* 2 Lokacin da ya dawo tuni ta Dade da yin nisa cikin barcinta,ya jima zaune yana kallonta,ba qaramin tausayinta yake ji ba haka nan d wannan uban cikin nata da yafi watanninsa girma "Har yau Baki gama sanin irin matsayin d kike d shi cikin zuciyata ba Fadeelah,sadai na sani lokaci zai ci gaba da nuna miki"ya fada a filing,bayanta ya koma ya kanta bayan ya janyota jikinsa ya sake tofesu da addu'o'in tsari na kwanciya barci,hannunsa daya na saman cikinta yana shafawa a hankali yana jin qaunar abinda ke cikin nata yana sake ratsashi Qarfe goma su na falon zaune abinsu,Garin na lullube ne da hadari kadan don haka babu batun rana,sanyin a.c da qamshi mai taushi ne ke ganshi a falon,tun dazun ya tsura mata ido yana dariya qasa qasa,tun safe yake dawainiya da ita,wqnka,shiryata,bata ayabarta amma taqi yarda ko daya su hada ido,kunyar abinda tayi masa jiya ke cin ranta,tana ganin ta zaqe da yawa ta gaya masa maganganu da ya cancanci yayi fushi d a ita amma yaqi maimakon haka ma sai ya buge da yi mata hidima da dawainiya d ita Zuwa can ya