← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 84

Sashe 14

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

buqatar roqo ra'ayina ne"shiru tayi don tasan Aliyu idan yace eh babu mai sashi yace a'a,bare ita da take lallabawa tasan har yanzu lamarinta bai saki zuciyarsa ba Dakin yayi shiru har ta gama kidanta tayi kuma rawarta ita kadai,ba wanda ya nemi jin ta bakinta Aliyu ya rufe da addu'a,ita din ma bata zaton ko sun ce tace dinma zata tsinka wani abu,suka shafa addu'ar ta miqe ta fice ba tare da ta cewa kowa komai ba,samira ta bita da kallo ranta cike fal da kishi saboda komai hassadarta bata gano abun kushewa tattare da fadilan ba Shima kallon gun da ta tashin yayi yana dan mamakin sauyawarta yayi tsammanin za susha artabu ne kamar yadda suka saba a gida sai kuma yaga b sabanin hakan A bangaranta fadila dana sanin zuwanta tayi gun sosai don bai qareta da komai ba sai hanata bacci da ya yi duk yayin da ta runtse ido da niyyar baccin sai hoton fuskar Aliyu ya bayyana cikin duhuwar idanun nata,wata iriyar soyayyarshi ke mamaye ruhunta cikim tsakiyar daren kewa ta kamata ga kadaici da ya hanata sakat,so ne da bata yaba jin irinsa ba a rayuwarta qauna ce ta musamman,hakanne ya zama sanadiyyar karyewar zuciyarta duj yadda takai ga bawa kanta qwarin gwiwa,kuka ne matsananci ya sarqeta,daren tayi kuka mai yawa a kwancan tana tausayawa rayuwarta da makomarta,tasan tabbasa son Aliyu na daya daga cikin jarabobin rayuwarta,tanajin sa a jiki jini jijiya da ruhinta Cikin taimakon Allah bata manta da ambatonsa ba hakan yasa bacci yayi nasarar daukarta ayimin afuwa a danyi haquri da wannan sai Allah ya kaimu gobe Mrs muhammad bello ce [10/16, 12:31 PM] Salma Wa yasan gobe? Written by safiyya Abdullahi musa huguma Kwanakin da suka baya ta yisu ne cikin kadaici da kewa,ita kadai ke wuni a bangaren nata,bata da aiki sai wanka da sallah da shi dama abinci ba gwaninta bane saidai tayi ta jiyo muryar baqin samira da har yau suka qi qarewa,wani lokaci kuma ta kira farida su sha hirarsu Ranar da ta cika kwanaki bakwai a gidan ranar tana kwance a falo hannunta riqe da littafin sahihu muslim mujalladi na daya tana karantawa da yake mayyar hadisi ce ita ta jiyo ana knocking din qofarta ta dora littafim a saman kujerar taje ta bude Anty hauwa ce da yaranta bilkisu kausar Ibrahim sai qaramin su muhammad sai kuma madina qanwar momy da yaronta hamid sai iftihal,farinciki sosai fadila tayi don tasan yau babu wunin kadaici,nan falin ya kaure da hayaniya su suna hirarsu yana na nasu,ta shiga kitchen ta hado musu kayan motsa baki sannan daga bisani ta nufi kitchen don dora girki iftihal da bilkisu suka bita zasu tayata don sune yan manya madina ma binsu tayi aka bar anty hauwa da ragowan yaranta suna kallo fadila tayi tayi madina ta bari amma taqi don haka tare suka kammala komai,tare suka ci a babban plate guda yaran ma aka hada musu anti hauwa ce tace ayi haka kada a bata mata kwanunka,bayan sun gama madina ta hada kan kwanunkan ita da su bilkisu suka gyara mata komai,ganin ba kowa a gun anty hauwa ke tambayarta ina fatan dai baki da matsala da Aliyu ko dan kishiya wannan kam ita ba'a rasa ta da matsala saidai haquri ,dan murmushi fadilam tayi tace"ba wani matsala anty lpy lau muke"ta jinjina kai tace to saidai a yita dai haquri don kinsan zaman aure ya gaji yau fari gobe tsumma,tayi mata nasiha sosai tare da bata shawarwari masu gamsarwa fadila sosai taji dadin maganganunta hakan ya sake qara mata qwarin gwiwa da nutsar mata da zuciya Bayan sun idar da sallah ne ta la'asar wajan biyar da rqbi suka soma haramar tafiya,iftihal tace da naty hauwa mummyn kausar nidai anan za'a barni ko?,antu hauwa ta girgiza kai tace a'ah ai ba haka kukayi da mummy ba,bazan iya da wannan rigimarba tate zamu tafi da ke,ta soma diddira qafa tana maqale kafafa tana cewa nidai anan zan zauna mummyn kausar gaskiya,fadila tace da anty hauwa"anty don Allah ku barmin ita mana dama ni kadai zaman ba dadi wlh"anty hauwa ta zaro ido tace"wai rufamin asiri ai mummy bazata iya zama ba iftihal ba ko na barta da kanta zatq zo ta dauki abarta baki ji yadda aka kafa mana sharadi ba kan a bamu mu taho da ita kamar tasan za'ayi haka"jin haka yasa fadila ta haqura Ta tako.musu har waje bakin part dinta yara nata tsalle kowa da packet na chaculet dinsa a hannu ta bawa su anty hauwa turarurruka da qyar ta karba tace ita lpyrsu kawai ta zo gani,ganin suna shirin yin gaba ba tare da sun shiga gun samira ba tace"antu baku leqa gunta ba kun gaisa"anty hauwa tace o'o'o ni kam tun shigowarmu muka gaisa da ita a harabar gida ta rako baqinta sai dai ko madina ita da yara,madina ta tabe baki tace nima bani zuwa anty ina kallo fa sanda muka shigo tana ganinmu tayi saurin sallamar baqin ta juya ciki kema sai da kika kirata kusan sau uku sannan ta amsa miki,sai dai su kausar maza kuje ku gaidata ku fito mu tafi ungoshi bilkisu ga hamida ma aje da shi ai ya wakilceni Suna tsaye suna jiran yaran sai kuwa gasu jiki a salube sun dawo Ibrahim sarkin zuciya hadda guntun hawaye madina na amsar hamid daga hannunsu tana tambayarsu me ya samesu,bilkisu tace anty koromu tayi wai ba mun gaisa a waje ba meye kuma na wani biyota,ibrahim da ya fisu shekara yana kusan 12yrs yace"har tsawa fa tayi mana wai masu qwala qwalan ido sai kallonta muke wa ya sani ma ko turo mu kayi mu cinyeta"iftihal kam fuskarnan a turbune tqma kasa cewa komai,anty hauwa tace ya 'isa haka is ok bata mata rai baqinta suka yi ku wuce muje,sukayi gaba fadila da mamaki ya kamata tana biye da su mamakin samira take sai kace wata mahukaciya yara zata tsaya tana gayawa irin wadannan magan ganun sai ka ce wasu manya,suna gab da get suka ji ana kwararo horn mai gadin ya tashi da azama ya bude wawakeken get din wata farar motace sol qirar range rover ta shigo ta samu gun parking ta tsaya da gudu iftihal ta kwasa tayi bakin motar Ya bude motar ya fito sanye yake da suit masu bala'in kyau baqaqe sunyi masifar yi masa kyau da kwanciya lif a farar fatarsa tas da shi kamar yanzu ma yake ahirin fita aikin ba wai ya dawo bane,iftihal na qarasawa ya cafeta ya daga ta sama ya jujjuyata yayi kissing kumatunta sannan ya direta ta tsugunna da alama gaidashi tayi,madina tayi dariya tace "oh uwar wayon tsiya wai har motocin Abbanta ta sansu wannan yarinya "anty hauwa tace"ke ai iftihal da wayinta aka haifeta don.mummy tace duk cikin jikokinta bata ga mai wayonta ba"da hirar iftihal da suke suka qarasa gurinsu ,cikin motoci fadila ta dan rabe bayan wata mota tana ganinsu tana kuma jina binda suke cewa,ya dago yana masa sallamarsu.lokacin da yake tambayar iftihal"ashe tare kuke mummyn yara"anty hauwa ta mayar masa ta sigar da ya fada" mummyn yara tun dazu tazo kuma yanzu zasu koma"ya juyo yana kallin madina yadan hade rai yace"au da waccar kima zo"anty hauwa dake danne dariya tace"eh duk tare muke"tasan yar tsamarsu da Aliyu don tun ranar da take fadin ita babarsa ce tunda qanwar mummy ce bata san yana gun ba suke yar tsama ya daina sakar mata Ya miqawa su ibrahim hannu suna musabaha haka halayyarsa take dama yana dan tsokanar ibrahim din kasancewar sunan kakansu ne shi kuma ibrahim na murmushi ya karbi hamid daga hannnun madina yana duban anty hauwa yace ba wanda ya rakoku ne?,anty hauwa tana dube dube tace tare da fadika muke ina tayi ne?,fadila data dora hannayenta saman motar tana game a wayarta har dankwalin kanta ya zame bata sani ba ta dago jin an ambaci sunanta idanunta suka fara sauka kan aliyu cikin sa'a suka hada ido harara taga ya balla mata wani abu taji ya caki zuciyarta ta lumahe idanunta am ta kasa budesu wani sinsa taji na mamayar zuciyarta da gangar jikinta kamar ana zira ra mata ruwan sanyi bugun zuciuarta ya sake qaruwa,bata san me tayi masa ba yake harararta,sai tq sunkuyar da kanta tana kallon yatsun qafarta dake saye cikin slippers,sai da iska ta watso mata gaahin kanta gefen fuskarta sannan ta gane ma'anar hara rar da aliyu ke mata don bata manta ba rabi'ah ta taba fada mata ya aliyu baison yawo a waje ba dankwali idan ya ganki kuwa kin shiga uku,da sumauri ta jawo mayafin data yafa ta lullune kanta sosai Duk daga idon da zatqyi a rayuwarta ta kalli aliyu sai taji an qara manna mata sonshi ji taje kallomsa ma kawai jaraba yake zamewa rayuwarta sai dai koda tayi niyyar qin kallon nasa sai ta kasa jure haka domin zuciyarta bata lamunce mata ba,ba abinda ke sata nishadi irin kallon kakkyawar qayatacciyyar fuskar tasa To fadila za mu wuce sai an kwana biyu kuma,cewar anty hauwa tana dan murmushi ta taso daga jikin motar da niyyar sake yi musu tattaki suka sake hada ido da shi sanda tayi niuyar satar kallonsa wata hararar mai zafi ya sake watso mata wadda ta sata tsayawa daga nan cak,yaram suka taho suna kama hannunta suna cewa anty bye bye,itama ta daga musu hannu tana dan murmushin yaqe tana cewa"bye"sai kuma iftihal ana su taho ta ja tunga ta tsaya ita allan katafar ba zata bisu ba aliyu dake karbar takaddu daga hannun nasuru ya juyo yana tambayar meke faruwa anty hauwa ta masa bayani,kallo daya tak yama iftihal din tabi bayansu jiki na rawa Bata sake sha'awar kallon inda yake ba don ta gaji da ganin wanna hararar tasa da kallon qiyayya da yake jifanta da su sai ta juya da sassarfa don barin gurin "ke"taji dakakkiyar muryar Aliyu,batason irin wannan kiran sam don haka tayi banza bata juyo ba bata kuma amsa ba kuma bata daina tafiyarta ba ya sake daga murya yace"dake nake"sai ta tsaya cak saboda tsoron da ya bata muryarsa ta canza tayi fakare tana jin yadda zuciyarta ke bugawa,da tsawa yake mata magana bayan ya sha gabanta"ki baki isa a kira ki ba kenan
Chapter 14 · 0% Book details