Sashe 22
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin garden,dakinta ta shiga ta sake fesa turare sannan ta lulluba mayafinta,tunda ta nufo lambun zuciyarta ke dukan uku uku a haka har ta cimmasa,yana tsaye ya goya hannunsa a baya ya juyawa qofar shigowar baya,batasan yadda akayi ya gane ta shigo ba don gurin gaba daya grass carfet ne bare tace yaji takun tafiyarta ne sai ji tayi yayi gayaran murya gayaran muryan sai ya zamo kamar ya mata luguden guduma a qirjinta ,me ya fito dake harabar gida babu lullubi?shiru tayi muryarta na dan rawa tace ka.....kay......kayi haquri"ya dan dauke wuta na dan lokaci kana ya juyo da azama kar mai shirin waftar wani abu,hakan ya sa tayi tsammanin duka zai kawo mata tayi baya da sauri cikin tsautsayi ta taka wani dutse sai kuwa ta tadeta tayi baya luuu zuciyarta na bugawa da sauri don ta gama saddaqarwa sai ya sha qasa,sai kuma ta jita jikin mutum aliyu ne ya sa singalalin hannunsa ya tallafeta ta bude idonta data lumshe tana jiran ta jita ta sha qasa sai ga idonta cikin nasa,ya tsuke mata fuska kana yace meye haka tashi" tayi azamar zare jikintata tana cewa kayi haquri,sai ya harde hannunsa aqirji ganin yadda duk tabi ta duburburce yabi gashinta wanda ya bi wuyanta ya dawo kafadar ta ta dama da kallo lace din ya zauanar mata caras cas yabi lafiyayyar fatarta chaculet,ya dan dauke kansa yabi gefansa da kallo yana jan tsaki a fili WA YASAN GOBE? Sai da ya gama shan qamshinsa sannan yace ina da baqi dame dame kuke da shi a kitchen?cikin dai rawar muryar tace akwai sinasir masa funkaso da miya fried rice sai white rice da miya,ya danyi shiru sanna yace cikin sweet a bamu sinasir da masa sai a hado da white rice tace to har ta juya yace hey! Tadan waigo idonta na kallon qasa yace idan min kawo kiyi knocking kawai ki barsu a bakin qofa ta gyada kai ta wuce Bayan isha'i gidan ua dade ba mowa sai anty hafiza da farida suma suna gama kintsa mata ko ina suka turare shi sannan sukai haramar tafiya,godiya ta musu mai yawa su kuma suka cikata da nasiha ta rakosu tana bawa naty saqo don allah ki kawo min yan biyu tunda kika kaisu gida yaye anty minqi karbosu tace yayanku ma mita yake amma shekaran jiya munyi waya da mama sun kusa dawowa insha allah da haka suka rabu ta dawo ta koma bedroom dinta ta hada ruwan wanka wanda ya wadata da turarukan wanka,bayan ta fito ta shirya kanta ckin wani lafiyayyen material kalar qwanduwar qwai wanda aka masa ado da qyalli silver da ratsin fari kadan kadan ,shima yana daya daga ckikim dinkunan da aka kawo mata jiya riga ne da skert amma wadannan sun kamata sun muma fito da shep din ta sosai,tana gyara kayan kwalliyar dake kan madubin nata ne taji gudar yan kawo amarya jikinta ya saki ta zauna bisa dressing chair Tana kwance bisa kujerar qaramin falonta agogon bango ya kada qararrwar qarfe goma tayi ajiyar zuciya ta gayar kwanciyarta goma da ashirin da biyu qarar intercome ta tada ita daga bangaren aliyu ne hakan yasa ta fahimci hadasu yake sonyi kamar yadda al'ada ta tanadar gabanta ya tsanata faduwarsa ,cikin nutsuwa ta sake feshe jikinta da turare turare ta lulluba mayafi a lallausan gashin kanta wanda bata daura dankwali ba Da sallama ta tura qofar falin nasasu biyun ne suka amsa amaryar na tsaye gaban fridge tana ciro ruwan roba da lemo yayin da gogan ke hakimce bisa kujera two sitter shigar jikinsa ta yanzu ta babbanta da ta dazu duk da dai babbar riga ce yanzu ma a jikinsa ta shadda milk colour ya ajiye babbar rigar a hannun kujerar da yake kai,salima ta dan zubawa fadila ido na yan sakanni sannan ta dauke kai ta dauki plate saman fridge din ta dora kayan fadila ta samu one sitter dake gefansu ta zauna ,saluma ta janyi centre table dan madaidaici gaban aliyun ta dora masata tsiyaya ya masa ta jiye ta koma kusa da shi kan kunerar da yake kai ta zauna,fadila ta saukar da idanunta qasa tana cewa cikin ranta "ni kadaice bani da irin wanna damar me yasa why Aliyu?,na kusa samota na kusa da qarfin zuciyata insha Allah" muryarsa ta jiyo yana fadin kefa mume jira ko?,shiru na yan mintina sanna ya qara cewa"yayi miki kyau" ya ajiye wayar ,saluma tace kawai ka qyale ta ni na gaji bacci nake so nayi,fadila ta dago kai suka hada ido sai kuma kowacce ta dan saki fuskarta fadila tace sannu amaryarmu"itama da dan murmushin a fuskarta tace sannu kuna lpy"a taqaice fadila ta amsa mata da" lau"ta dan saci kallonsa shi lemonsa ma yake kurba idonsa na kan qofa Banko qofar akayi aka shigo samirah ce sanye da baqar doguwar riga babu ko alamar hida bisa fuskarta sai dan kwalun atamfa da ta dauro a kanta wanda tayi masa daurin ture kaga tsiya,ta kama qugu tana cuno baki gaba tace da aliyu "gani" wani banzan kallo ya jefeta da shi sanna yace "ga gurin zama nan ko ina idan kuma bai miki ba.....ya nuna mata qofa da hannu ,sai da ta qarewa ko ina kallo sanna ta nufi kujerar da aliyun ke kai kusa dashi a daya side din ta dora qafa daya kan daya tana girgizata harara salima ta makawa samirah itama kuwa batayi jinkiri gun ramawa ba,taja tsaki sanna taci gaba da jijjiga qafarta,hara rarta aliyu yayi ya kalli qafar da take jijjigawa ta fuskanci abinda yame nufi kuma tasan ba magana zai.mata ba don haka ta sake zumbura bakinta sannan ta sauke qafar tata Godiya ya far yiwa Allah sanna ya dora dukkaninku a qarqashin iko na kume kuma tsarin Allah ne shi ya tsara hakan kamar yadda yame da ikon tsara rayuwar ko wane bawa nasa to ma gode masa akan duk yadda yayi da tawa rayuwar "daganan ya dora da yi musu gargadi da jan kunne sannan ya tunasar dasu tsarinsa na zama a bangarensa mai girki ta biyoshi"salima ta kanne masa ido tave" dear ani dama na nasan da wanna tsarin naka tuntuni saidai kawai ya zamto kamar tunasarwa a gareni"murmushin shima ya mayar mata yace "yes" Zuciya ta kawowa samirah iya wuya sai da ta tanka" a banza ai wai talaka ya girmi sarki dolen mutum yanzu shinr qarami ko yaqi ko ya so"cikin fusata salima tace " ke nifa ba dake nake ba,ban gayyatar irinku a zancena don ni idan banda qaddara ba ma baki kai matsayin ma ki zama kishiya ta ba wlh don ko yar wanke wanken gidammu ta fiki kwarjini sai kuwa samira ta nuna ta da yatsa tace" don kutumar uban mutum ya qara gaba mana don ni duwa wuce dole ne a zauna da ni zama daram wlh "sai suka so su kacame Cikin wata gigitacciyar tsawa aliyu ya dakatar da su sannan yace kowacce ta bace masa agun ba zasu haddasa masa ciwon kai ba haka kawai"salima ta miqe ta shige bedroom dinsa samira kuwa ta fice tana gungunin a qyaleta wlh taci uwar mata,ita kuwa fadila abun nasu tsorata ta yayi don bata taba ganin fadan kishiyoyi ba hasaluma ma ba'a taba yiwa umminta kishiya ba gidansu daga ita sai farida sai muhammad ko a tsakaninsu ba fada suke ba don haka tun ma kafin ya kammala bada umarni su fice din ita tuni ta riga su fita yana juya lamarina ranta Ransa abace ya shiga dakin duk yadda taso lallashinsa yayi banza da ita ta san halinsa tun ba yau ba kuma bata manta da shi din ba don haka da taga yayi banza da ita yana shirin shiga wank sai ta qyaleshi sai da ya fito yana shirin kwanciya sanna ta langabe a jikinsa tana bashi haquri,ya dan kalleta ya basar sannan yace matuqar kika ce haka zaki dinga biye mata kunayi a cikin gidana to na rantse babu wadda zan saurarawa acikinku,idan banda raini ma a gabana? Ta sake marairaicewa tana cewa "Allah na lura ita wannan kanta na hayaqi ne da kamar dayar ce da babu ruwana da ita,su auremin mijin kuma suce bazanyi kishi ba" shi sai a lokacinne ma ya tuna da fadila baima san sanda ta fice a dakin ba donsanda yake musu jawabin ka ta na sunkuye ne sai ya tuna rana shigen irin wanna da ya hadasu ita da samirah ba wanda ta kula a ranar ma ahi ko samiran harta wuce" ya kauda wannan yace mata" am telling uh indai kina son zama da ni cikin kwanciyar hankali" "baza'a qara ba dear" Ganin yadda yaqi sakin jiki da ita yasa ta dinga masa wasu abubuwa wanda suka sa ala dole ya ajjiye fushinsa abinka da dama wanda yake cikin wani hali nan ya bada kai bori ya hau aka tuno da tsohuwar zuma don salima dama idanunta a goge take ta wannnan bangaren to haka shima aliyyun yake dalilin da yasa saliman ma ta kasa auren kowa kenan tayita naci har sai data dawo masa Mrs muhammad WA YASAN GOBE?....... Written by safiyya Abdullahi musa huguma Cikin kwanakin amarci kawai ake ta ballewa a gidan ,salima wayayyar gaske ce ko da wani lokaci tana manne da A.s maitama samira kuwa ta kasa tsaida hankalinta gu guda,yiwa salima itada da aliyyu labe kuwa ya zamo.mata kamar ibada mintina kadan sai ka hangota tana ta safa da marwa tsakanin sashenta da na Aliyu,fadila baiwar Allah lissafinta yafi ga kwanakin da zata soma shiga office da kuma ranar da zata zamo itace ranar girki a gareta Kwana uku kenan da tarewar salima fadila ta soma zuwa aikinta ya kama ranar laraba,shiga tayi ta hausawa atamfa ce dinkin riga da zani wadatattu yayin da tayi lullubi har kanta cikin yalwataccen mayafi komai nata cikin kamala yake da nutsuwa haka nan halittarta take kamar wata babbar mace duk da shekarun nata qana na ne,ta bude sabuwar motarta fara qal wadda bata taba shigarta ba saiyau,ta zauna a sit din zaman driver ta kunnata ta wana ta sosai sanna ta sauke hannunta daga kan key din ta hada tafukanta ta soma addu'a ,sai da ta gama tana shirin tasar motar ta tuna da hand bag dinta data manto kan gadon