Sashe 63
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
jin qaunarsa na yawo cikin jinin jikinta,shiru tayi masa har ya qara cewa "me ya hanaki yun bacci a irin wannan lokacin fadeelah?" Nan ma shirun ta sake yi masa,saidai ita kadai tasan yadda take ni'imtuwa da jin muryarsa mai tsada "nasan kika jina fadeelah,kuma bana tantama abunda ya hanani bacci shi ya hanaki....,sau da qauna ne ke dawainiya damu baki daya,tunaninki shi ya hanani sakat kamar yadda na san cewa tunani na shi ya hana miki yin bacci,da zaki ganni a yanayin da nake ciki zaki tausayamin,da zan iya ciro zuciyata kiga dumbin qaunar ki da ta cikata fadeelah da nayi,na tabbata da sai kin min addu'ar Allah ya rage min,jin shirun yayi yawa yasa yace "hello,are you there?" Ya duba phone dinshi tana nan bata yi hanging up ba,ya sake maida wayar kunnensa yana cewa "please fadeelah say something ko zan samu relief,am sorry fadeelah and I said it really" tsananin mamaki ne ya mamaye fadila,shin da gaske ne ba mafarki take ba aliyyun ne kuwa?aliyyu salim maitama? Aliyyunta?,mafarkinta na kullum,burin zuciyarta,shike gaya mata wadan nan tsadaddun kalamai?....kalaman da ta dauki tsawon shekaru tana dakon jinsu?irin qaunar da ta jima tana lalubenta daga gun aliyyun,shin da gaske ne a yanzu ta samesu?,eh...yes ta samesu but he didn't deserve ya samu amsarta a arha har irin haka,now its her turned,its her field to play her game..... Muryarsa ta tsinto cikin sanyi yana cewa"fadeelah I know you gave me happiness and I gave you a reason to cray,u gave me your care and I stabbed you from behind,am sorry for having given you nothing in return for you having given me everything am sorry kiyi haquri....." kasa jure ci gaba da jin kalamansa tayi,tasani ko iya wannan ya isheta,ta samu qauna daga gun aliyyun,ta samu soyayyarshi,ya kawo mata kansa yana begging dinta ta bashi soyayyarta.....,tuni ta katse wayar wani dadi na nuqurqusarta,ta sani tabbas zai kuma gwada kiranta saboda haka ta kashe wayar gaba daya,cikin zaqi da gardin kalaman da aliyu ya kasheta da su bacci yayi awon gaba da ita tamkar dama au take jiran ji,bacci ne mai cike da mafarkan aliyyun a yanayi daban daban,shi kam tsai yayi da wayar a hannunsa cike da al'ajabin yaushi mace ke kashe wa waya?,tabbas ya sake yarda fadilan tana da wani matsayi da babu wata 'ya mace da ta kama koda gefanta Tunda ta kashe wayar bata kunnata ba sai washegari sha daya na safe tana shirin tafiya office sha daya na safe,cikin shadda take pinch sai maiqo take dinkin doguwar riga aka mata,cif cif rigar tayi mata kamar a jikinta aka dinkota,ta bude sosai daga qasa rigar,tana cikin yafa orange mayafinta sumayya na koda kyawun da tayi"wallahi anty kyawunki na daban ne Allah kuwa ba don wai nayi ziga ba,ko bakiyi kwalliya ba kyanki fitowa yake,zanso yaya yaga wannan kwalliyar" Harararta fadilan tayi"ke dai kin shiga tara,tuni rabi'ah ta dade a school ke kin zauna kanzagi kinqi fita,to bazai ga kwalliyar ba,sumayyan ta qyalqyale da dariya hadda kwanciya saman gadon"wallahi anty kiyi a hankali kada amiki qwace don har yau yayin ya aliyyu ake ba'a dena ba,kullum Allah ne da kullum wallahj dai ya fatattaki 'yammata,kada ki dauka qananu,a'a wlh anty hadaddu masu ji da kansu 'ya'yan manya kuma",fadila ta tabe baki kishi na cin ranta duk datasa haka dinne amma sai tace "dawar wani karkarar wani abincin wani kuma gubar wani"ta dauki wayarta dake gefan sumayyan zata fice sumayyan nata sheqa dariya,text ne taji ya shigo hakan ya sanyata dakatawa daga yunqurin fitar da takeyi,number din da aliyyu ya kirata ne jiya Tun shidan safe saqon ya shigo "if u can't see the tears in my eyes,I beg you feel the pain in my heart....fadeelah na rantse I will do anything and everything just to take away all d hurt that you feel,please na roqeki give me and let me set thing straight,am sorry once again fadeela and I love you I really love you...."gaba daya ya zare mata dukkan kuzarinta,jikinta ya saki,maimakon fita sai ta koma bakin gado ta zauna,sumayya daketa leqen wayar tana qumshe dariya tace "anty lafiya dai ko?" Ta saki ajiyar zuciya gami da dauke idonta daga kan screen din wayar "lafiya lau me kika gani?"sumayya ta kada kai tana cewa "gani nayi kin shirya zaki fita kin dawo kin zauna,jiya kuma fa anty naga cikin dare baki yi bacci ba ko" hararar fadila ta sake aika mata tana kada kai cikin zuciyarta tana cewa "lallai na yarda ba qaramin illa soyayyar aliyyu ta yimin ba,a fili sai kuma tace "naji to sai kuma akayi yaya?" Ta fada tana ci gaba da jifanta da hararar wasa,miqewa summayan tayi tana ci gaba da qunshe dariyarta tace "k'n,uhmmmm,a'ah anty ni bance komai ba daga wannan,amma dai anty kiyi a hankali saboda yayammu gwarzo ne kuma gwani ne,he is hero,zai iya saaaaaace zuciyarki ba tare da kin sani ba" Pillow dake kan gadon ta jawo ta jefi sumayyan da shi tana cewa "ban guri mara kunya" gocewa tayi ta fice da gudu tana dariya,sake mai da kanta fadila tayi kan saqon taa sake karantawa,ba shakka aliyyu shu'umi ne,so yake ta qarfi da yaji ya wargaza mata duk wasu makaman yaqinta,ya shirya tunkararta da duk wasu makamansa wanda tana tsammanin indai haka ne mawuyacine ta iya kubuta daga kaifinsu,duk ya kashe mata jiki kamar yadda ya saba ta qarfin tuwo ta gayyato dauriya sannan ta samu ta fita,ta tadda momi da sumayyan a falo,ta yiwa momin sallama,sumayya tace "a dawo lafiya anty.....momi dama inason baki labarin abinda na gani dazu,wata soyayya ake mai fada fada aciki"ya fada tana satar kallon fadila dake qoqarin ficewa daga falon fuskarta dauke da murmushi,a sace fadilan ta watsa mata harara mai nufin gargadi a fakaice ta qarasa ficewa,sumayyan nata qyatunta tace "na fasa anty kada ki hanani kudin ankon".......... *Mrs muhammad ce* [10/16, 2:13 PM] Salma *WA YASAN GOBE?....* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 3* Qarfe hudu dai dai ta kammala sallar la'asar dinta a masallacin mata da nan cikin gidan radiyon,ta goge kyakkyawar fuskarta da hoda,ta murza dan qaramin turarenta na (asaal brush perfume)wanda bata rabo da shi cikin jakarta saboda dadin qamshinsa gashi kuma qaramine baya da cika guri,ta saba jakarta bisa kafada sannan ta dauki wayarta ta nufi office dinsu don ci gaba da aikin takaddun programme dinta na gobe da ta baro ta taho yin salla Ta tura qofar ta shiga kasancewar babu kowa ciki fauziyya ta tafi yiwo wani aiki a a ministry of education shi yasa bata damu da yin wani sallama ba, Taja takardun gabanta bayan ta zauna ta dora daga inda ta tsaya,sosai yanayin tsarin programme din na gobe ke burgeta muhawarar da za'a tafka cikin shirin,lokaci lokaci takan saki murmushi gami da gyada kai,hakanan cikin jikinta ta dinga jin tamkar ana kallonta,cak ta tsaida rubutun,kan ta kai ga yin komai an zuro hannu an zare takaddun,tabi hannun da kallo har zuwa fuskar wanda ya gabatar da aikin,aliyyu ne tsaye qyam a agaban teburin nata,sanye yake da shadda ruwan madara(milk colour) dinkin yarbawa,rigar iyakacinta gwiwa hakanan hannun rigar shima gajere ne iya gwiwar hannu,sai manyan aljihu gefe da gefe,wandon dogo ne,kanshi babu hula sai kyakkyawar sumarshi dake cike da gayu da tsafta,idanunsa na saye da gilashin nan nasa fari qal wanda tana iya hango fararen qwayoyin idanunsa dake zube fes a kanta Kallonta yake sosai ba tare da yace komai ba,da azama ta miqe hadi da ture kujerar da take kai baya,tasa hannu zata dauki jakarta gami da qoqarin ficewa daga tsakanin table din,taku uku yayi ya tsare mata hanyar ficewar,baya tayi da sauri saboda ganin yadda yayi gab da ita kamar mai shirin fadowa jikinta,ganin ta sake yin baya ya sanya shi sake shigowa cikin shima,da haka har ya danganeta da bango,sosai take jin fitan numfashinsa wanda ke cakude da qamshin turarensa Ya dage sai ya sanya qwayar idanunsa cikin nata,saidai sam taqi yarda hakan ya faru,lumshe idanunsa yayi gami da nufar bakinta kai tsaye yana mai kwadayin tsotsar tattausan lips dinta,tuni ta gano manufarsa ta sunkuya ta qasan table din ta zille,bai san hakan ya faru ba sai da ya jishi ya dangane da bango,da sauri ya bude idanunshi,can ya hangota har ta dora hannunta kan handle,cikin zafin nama irin na cikakken da namiji ya haura ta saman table din don sai yafi masa sauri,taku hudu ya isa gareta,lokacin tuni har ta sanya qafarta waje Jawota yayi har sai da ta fado jikinsa uasa hannayensa ya rungumeta,da qarfin tuwo take son qwatar kanta saidai hakan ya gagara,batasan wani yazo gilmawa ya gansun a hakan saboda qimar da take da ita agun dukka ma'aikatan gidan ba zata so hakan ya faru ba,ta kuma kasa bude baki balle tace ya saketa sai kawai hawaye ya balle mata,Allah ya taimaketa sai ua dauketa cak ya dawo da ita cikin office din hadi da murza masa maqulli ya kullesu Kujera ya janyo ya dora ta akai yana maida numfashi,tsaye ya sake yi a kanta ya zube hannayensa cikin aljihun wandonsa yana sake qare mata kallo kai kace ranar ya soma ganinta,ita kuwa tana zaune sai qananun hawaye take,ya sake taku biyu ya matso gabanta cikin wata iriyar cool voice yace da ita "fadeelah pls stop craying,I can't take it anymore,I know shirun wanda aka ma laifi yake nufi...I know,ki hukuntani kawai fadeelah kimin hukuncin da kike jij shi zai sa temper din da kike ji game da ni zai tafi,zan iya dauka,nasan duka girman laifi na ne ya jawomin,amma fadeelah kinja bakinki kinyi shiru,kinqi cewa komai kwata kwata why?,please(ya hade tafukan hannayensa)ko zagina ne kiyi fadeelah indai zakiyi magana indai kuma hakan shi kadai ne hanyar da zai saki ki huce,ko duka na ne ma kike so kiyi indai shine zai saki ki huce am ready fadeelah" Ko daga kai ta kalleshi bata yi ba balle yasa ran zata ce wani abun,hakan take masa ko wani lokaci,ya tsani shirun nan nata,yana ci masa tuwo a qwarya,ya fuskanci babu ta yadda za'ayi su fuskanci juna babu ta yadda za'ayi ya samu abinda yake buqata matuqar ya barta taci gaba da yin shirun bayan kullum bai cikin nutsuwarshi duk ta sanadiyyarta....duk ta sanadiyyar qaunar da yake mata,bayan kk yaushe bashi da wani muradi sai nata,ta riga da