Sashe 23
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta da sauri ta bude motar ta koma ciki A hanyar dawowa ne sukayi kacibus da shi kasancewar ta gefansa ne zata wuce din sai tayi tsammanim bai ganta ba don haka ta dauke kanta cikin sauri ta wuce don ta kusa makara ta ajjiye jakar a asit din baya tasa hannu zata kunna motar taji an janye hannun gami da zare key din ta daga kai tq bishi da kallo bai ko kalleta ba ya zagayo sit din mai zaman banza dake kusa da ita ya zauna sosai sannan ya maida qofar ya rufe,ta dan sunkui da kanta ya dan kalleta sannan ya basar don ya lura kamar al'adarta ce hakan,ya tabe baki cikin muryar nan tasa ta isassun maza mai cike da izza ya soma ce mata"ko banza a qarqashin mulki da ikona kike saboda haka u must obeying my statute and order if kina son aikinki,ya dan qara tsuke fuska duk da yawancin lokuta haka fuskar take ya dage kafadunsa sannan yace" I don't know why aka wani tsiri yin aikin bayan ban gaza komai a gidana ba...... Ya dan sha qamshi sannan ya dora firstly ya zama dole kanki shiga ta kamala idan kin tashi fita,sannan ban lamunce da yawace yawace abu na gaba kada ki kuskura na ganki da number din wani qato a waya ko receiving calls ba and d last one kuma mafi girma wanda zai iya causing loosing din aikinki mu'amala da maza,kada ki dauki damar da na baki na fita aiki lasisi ne da na baki da zaki dinga ganin kina da right na yin duk abunda kika ga dama,take note ,yana qoqarin ficewa tace insha Allahu zan kiyaye"duk da ranta a abace yake da irun dokokim da yake kafa mata da ita a karan kanta ai tasan ya kamata,baice komai ba ya cilla mata key din yaja qofar ya fice ya tafi abunsa,ta miqa hannunta ta rufo qofar sannan tabi bayansa da kallo yanayin yadda yake taku kamar zabar masa inda zai taka ake,ranta babu dadi ta ja motar ta fice a gidan ,yanayin motar yana da dadin tuqi hakan ya taimaka mata wajan dawo mata da walwalarta,a hankali temper dinta take sauka sai ta dora da fadin la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalim cikim zuciyarta,da haka har ta qarasa gidan radiyon freedom don can ta tafi sha'awa amma duk da haka akwai wasu privet ayyuka da zata dinga yi da express radio din Yanayin yadda ta samu karbuwa ya sake sa mata interest akan aikin sosai,su biyu ne kawai a office din ita da wata fauziyya kusan za tayi sa'a da fadilan amma ita nada yarinya daya iman,fauziyya shekararta uku da soma aiki da tashar,sosai fadila taji dadin samun fauziyya da tayi wayayya mai faran faran da son jama'a duk da ita miskila ce,wunin ranar tayi shine tare da managing director da wasu ma'aikatan tana arranging din ayyukanta ciki harda tsara sabin shirin da suka qirqiro wanda za'a fara gabatar da shi a asabuwar shekara wanda itace mai gabatar da shirin da taimakon fauziyya ta sake fuskantar yadda abubuwa suke duk da dama tasan da wasu lokacin attachment dinta Kwana biyu tayi tana tsara komai ta mai da kanta busy sosai ta hana kanta sukuni hakan yasa bata da wani lokaci na tunani ,da ta koma gida tayi wanka tayi sallah sai ta samarwa kanta abunci simple ta ci sai kwanciya idan da wuri ta dawo kuma takan yi tilawar alqur'ani tunda dama ta jima da kammala haddarsa tun lokacin da tayi candy,idan ta gama taga tana da wani lokcin sai ta dauki wani aiki da zai taimaketa a office ta yi ko tayi amfani da laptop dinta tayi research na wasu abubuwan masu muhimmanci,a rana ta uku ne da taga komai ya kammala ta nemi hutu na kwana biyu ba wani matsala suka bata tunda dama bata soma gabatar da ayyukan ba cikin shirye shirye dai take,tayi hakanne don a lissafinta ya bata yau itace zata karbi girki ,kuma dama tuni ta shiryawa zuwan ranar Da wuri ta koma gida ruwa kawai ta watsa ta zura doguwar riga har qasa mai hannun shimi ruwan hoda ta saka,ta taje dogon gashinta ta daureshi da ribbom shima ruwan hodar ne,farin hijabi ta saka wanda iyakacin qirjinta kawai ya rufe,ta wuce locker dinta ta lalubi inda ta adana muqullan da bata amfani da su ta debesu gaba daya ta zira farin silifas na fata ta fito,a falonta ta soma tsayawa ta bude fridge ta dauki lemon chi exotic nectar na pineapple da yayi sanyi sosai ta sha ta maida sauran ta rufe sashen nata, TO FADILA SAI INA? Kai tsaye sashen Aliyyu ta nufa gabanta na dan faduwa kadan kadan har ta isa qofan,addu'a fal bakinta ta ke sanya muqullan daya bayan daya take gwadasu har ta dace da na qofar,ta tura babbar qofar ta shiga sanyin a.c ne da daddadan turaren aliyyu ne yayi mata maraba,ta dan lumshe ido kadan sannan ta waresu sosai kamar mai neman wani abu,a hankali take bin kowane sashi na falon da kallo tabbas yana buqatar gyara,bata shakka cewa har bedroom dinsa ma na buqatar a kintsashi,ba tare da tsayawa wani dogon nazari ba ta dauko dust bin dake falon ta ajjiye a tsakiyar falon ta zare dan hijabin nata ta jefashi kan kujera ta fara tattare ta fara tattare leda takarda gwangwani da duk wani abu da ya zama datti ne tana jefashi cikin kwandon sharan Tana tsaka da aikin ne taji ana taba qofar alamar an shigo a tsorace ta dago tana tsammanin aliyu ne sai dai kuma maimakon haka sai taga ashe salima ce tayi tsaye a abayanta tana qare mata kallo ,fadila ta tsani yadda matar me mata naci nkallo haka,dama ita tun da can ta tsani mutum mai azabar kallo,to haka saluma ke mata a duk sanda hanya zata hada su ,abinda ita fadila bata sani ba shine kishine taf cike a zuciyar saliman don so tayi ta samesu gaba daya babu mamora kamar yadda taga samira bata da qira sam,saidai ance gwano baijin warin jikinsa ne ita dinma da tayi dogon nazari da tsinkaye da ta fahimci yadda tata qirar take irin matan nan ne masu azabar tsawo da sirantaka sai wani azababben fari da take da shi irin me gauu din nan to duk da babu laifi tafi samirah amma ko kusa bata kamo qafar fadila ba,tsawonta da azabar sirantaka su suka sata take a miqe kamar number 1 ba wani shape sai tsabar iyayi da yauqi Ta kau da kai.daga kallon fadilan ta tabe baki sannan tace"oh nayi tsammanin mai gidan ne ya dawo da naga gun a bude" a taqaice fadila ta amsa mata da"A'a" taci gaba da aikinta,sai kawai salima ta bude fridge ta dau maltina hadi da kunna t.v ta nemi gu ta hakimce,sarai ta gano ba abinda yasa saluma zama a gun banda bin qwaqawafin taga me take yi hakan yasa ta sa key ta bude bedroom dinsa ta shige tare da rufe qofar da muqullin ta ciki,salima tabi qofar da kallo cikin takaici don ba haka ta so ba,nan ta zauna tana ci gaba da shan maltinan tana dakon fitowar fadila wadda batasan ma tana jiran ba Ta qarewa shima bedroom din kallo sannan cikin nutsuwar nan tata ta fare tattare shi shima tana kintsa komai a muhallinsa tanayi tana mamakin kamar babu wasu mata dake kwana a dakin komai a yamutse?towel ne underwear ne comb ne mayuka ne turaruka ne kai tarkace dai wanda da alama a safiyar yau kafin ya fita yayi amfani da su warwatse bisa gadon bedsheet din kansa duk da babu datti amma ya yamutse,kowanne abau ta maidashi inda ya kamata cikin qanqanin lokaci dakin yayi fes komai ya dawo cikin hayyacinsa ta kunna kaskon turaren wuta electric ta zuba irin turaren wutan da take amfani da shi a bangarenta sanna ta wuce toilet Toilet ne qaton gaske wanda yakai girman ciki da falo na mata da yawa yana dauke da duk wani kayan amfanin toilet na zamani,cikin lokaci qanqani shima ya dau haske komai na cikin sa farine sai da ya dawo daidai tamkar ka zuba abinci a qasan ka ci,sai da komai ya mata yadda take so ya wadatu da sanyayyan qamshi sannan ta bude qofan ta koma falon don ta qarasa aikinsa Salima ta bar falon saidai ga gwangwani nan da tasha malt cups da qarin ledojin cake da na wasu tarkacen ciye ciyen nata watse a agun da ta tashin,baki ta tabe cikin ranta tana cewa"Allah ya sawwaqe an san yadda za'a bata amma ba'asan yadda za'a gyara ba sai kace ba mata ba,tana wanna zancan zucin tana kammale falin duk da girmansa kuwa,har kitchen bata barshi a baya ba sai da ta gyareshi ,"haba duk kyan abu ai yana buqatar gyara"inji fadila tana riqe da qugunta ta fada bayan ta gama aikin tana qarewa bangaren kallo yadda ya koma tamkar ba shi ba Aikin ya ja mata lokaci sosai kuma ya gajiyar da ita,tana kimawa bangarenta nan ma dai ba zama din kitchen ta shiga ta kama habarta cikin tunanin me zata girkawa aliyyu wanda zata iya kammalashi kafin kiran sallar magariba ganin gashi hudu tayi har da rabi,abu mafi muhammancin ma bata san choice din aliyyu ba ,sai ta yanke a ranta bari ta fara gwadashi da tuwo ta gani din ta fuskanci wasu mazan ba sonshi suke ba in yaso idan yayi masa shikenan an wuce gurin Tuwom shinkafa ta daura miyar danyar kubewa wadda ta dagargaza mata zallar tsokar kaza sanna ta sa tantaqwashi ya wadatu a ciki,misalin qarfe shida komai ya kammala ta soma mulmula tuwon da yayi fari sol cikim farar leda ya tuqu sosai ya hada jikinsa,sababbin warmers masu kyawun tsari ta dauko ta jerashi a ciki,ta gama ta gyara ko ina kamar bata yi aiki a kitchen din ba,ganin tana da ragowar lokaci yasata ta dora farfesun danyan kifi ragon ruwa maimakon zaman jiran dahuwarsa sai ta hada zobo wanda ta markada wadatacciyar abarba ta zuba a ciki ta hada da citta da kanunfari ta dafa,shima ta zubasu a mazubi ta wanke tukwananta,cikin azama ta shiga toilet ta silla wanka na gano su maman sa'ida fa na son jin qwaqwaf an baza anason aji