Sashe 31
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
qafa tayi gaba, samira ta kasa zaune ta kasa tsaye tasan halinshi sarai yarjejeniya kuma suka qulla tun kan aurensu kan shi baison wadannan kwashen qawayen nata gashi yau ta saba yarjejeniyar,tana shirin guduwa dakin gadonta ya damqota ya maidata kan kujera,ya kalleta sosai sannan ya jefo mata tambaya"ina kika samo waccar shedaniyar?"ta dake duk da tsoro ne fal cikin idanunta tace"qawata ce fa"ya gane mai takeson yi duniyancin nata data saba don haka ya shirya nuna mata nasa salon,don haka sai ya saketa daga riqon da yayi mata,ya saki fuskarsa ya daga kafadarsa hadi da watsa hannayensa na nuna alamun rashin damuwa da abu kana yace"good....verry good tunda qawarki ce kinga abun zai zo min da sauqi kenan ko?,dama gani nayi tamun inason aurenta aikinga zaman naku zai miki dadi tunda kun fuskanci juna, bata san sanda tayi zumbur ta miqe ba tana zazzare idanu ba baki na rawa tace"iyi...mme...me kace"ya daga mata gira sannan yace"abinda kunnen ki suka ji shi nace"ya juya yana niyyar barin dakin,hankalinta a tashe ta riqoshi kasancewar tasan halinshi *fada da cikawa*ya dubeta fuska a turbune yace"meye haka"don Allah ka rufamin asiri wlh bazan qara ba kasan wace kubra kuwa?"ya sake dage kafada hadi da cewa"ni ina ruwana da koma wace ce tunda kin kawo min ita har gida ni kuma na gani kuma ta yimin"ya zare hannunsa yayi ficewarsa,yana jiyo kururuwarta sai ya tuna haukan da tayi masa sanda zai dawo da salima,murmushi ya subuce masa ba tare da yayi niyya ba,yasan cewa shikenan yayi abinda zai rabasu kenan har abada ba tare da ya wahal da bakinsa ba,(samira irin mai rawar kan tara qawayace ko wa qawarta ce kare da doki ga son birga da burgesu ita dole sai an san mijinta wani ne,kaya komai tsadarsa suka gani a gunta tofa take zata basu ko nawa aka siya musu ko na aliyyun ne kuwa,indai zata burge tofa magana ta qare,gata da saurin daukar maganarsu don yadda take jin zancansu nata jin na mahifanta haka ne yayi silar lalacewarta,wannan ne yasa aliyu ya rabata da kowacce qawa amma da yake akwaita da kafiya taurin kai da naci sai ta sake wasu sababbi wadanda aliyyun bai sansu ba) Kai tsaye ya wuce sashen sa tun daga falin ya ga canji komai fes ya koma hayyacinsa,daddadan qamshin girki ya cika falon nasa,bedroom ya zarce ya daura alwala ya nufi masallaci,kan ta kammala aikin ta gama gajiya tubus don kuwa aikine ya gama taruwa ya cakude ita kanta wani gun cike da qyanqyami ta daure ta gyarashi to ina kuma ga aliyyu Take tasha alwashin zata yiwa tufkar hanci don badaqalar data tarar a bedroom din tasa ta isa,tuni ta gane cewa fushinta bashi da amfani don yadda komai ya qazance ta sani cewa da duniya zata gani ba iya su samira kawai za'a zaga ba harda ita,don ba wanda yasan mekw gudana tsakaninsu,ta sake gayawa zuciyarta lallai ibada tazo yi ibada kuma mai wahala wadda itace tafarkin shiga aljannarta kuma ta dade da sani aljanna bata samuwa daga zaune ba tare da ka tashi kayi aiki tuquru ba kuma dole ka ninka haqurinka(wannan sune daya daga cikin lafuzan umminsu garesu ko yaushe,uwa ta gari kenan) Aliyu bai shigo ba har sai da yayi sallar isha'i don haka tuni ta gama komai har ta jere a dining taje tayi wankanta ta shirya tsaf cikin dark blue din shadda doguwar riga wadda aka mata surfani mai kyau tun daga sama har qasanta ,hankalinta dai na kan taliyarta don haka ta nufi table din saidai wayam don ko plate din babu,ta juya ta shiga kitchen acan ma a bude ta tadda tukunyar wayam Ta san babu wanda ya cinye abincin sai shi don ba wanda ya shigo din,wata dariya ta subuce mata data tuno yadda ya shigo dazun rai a hade yayi wani kicin kicin da shi ashe harda yunwa itama ta taimaka wajen dinkewar fuskar tasa,ta hade kwanunkan ta dauraye ta maida su muhallinsu cikin ranta tana cewa"babu rabona nasha ice cream Tana bisa carfet ta bude babbar robar ice cream din tana diba a hankali tana kaiwa bakinta lumshe ido take don babu abinda take jin dadin shansa kamarshi din,wayarta ta duba jin qarar shigowar text _kizo ki bawa mutane abinci_"haka taga an saka,ta duba sunan Aliyyu salim maitama kamar yadda yayi mata serving din ta ranar da bata da lafiya"ta miqe hadi da dauke ragowar ice cream din ta maida cikin fridge ta koma daki ta fesa turarenta na blue lady ta hada da asaal brush perform ta nade kanta da da farin hijabi ta zari wayarta ta fito hadi da kulle gun ta,a hanya suka hadu da salima ta rako baquwa suna tsaye da alama magana suke ganin fitowarta duk sai sukayi shiru suka bita da kallo ganin haka yasa tace musu salamu alaikum sanda zata giftasun,baquwarce kawai ta iya amsawa itama can xiki kamar wadda akayiwa dole,suka ci gaba da kallon nata har ta shige bangaran aliyun sai a sannan suka dauke idonsu baquwar ta saki ajiyar zuciya tace "tab gaskiya salima tahir na janjanta miki don wannan kam banga ta inda zaki ci nasara akanta ba,saidai ban sani ba ko ta bangaren farar fata"salila ta kai mata duka hadi da cewa"banason iskanci sadiya kota farar fatar ai sai na yi yaqi da itan ,dadin abun ma miskilancin mai gidan bai bari ki gane wa yafi so cikinku ai da tuni inaga na dade da kamuwa da ciwo yanda nake bala'in a son my dear "ta fadi tana dafe qirjinta"(abunda bata sani ba aliyyun irin mazan nan ne wadanda ke nunawa mace qauna wadda kan bawa mutane mamaki har adinga zaton kunya ce basu da ita ko mallakesu akai sunyi sake da damar da ya basu tun farko har ta subuce musu)sadiya ta dafa kafadarta tace"to Allah ya bada sa'a don ko nice a matsayinki gaskiya bazanyi wasa da aliyyu ba"salima ta juya ido tace "ashe kin fara gano gaskiyata Mrs muhammad ce [10/16, 1:42 PM] Salma *wa yasan gobe?....* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* Ku tayani duba jama'a na taho da sauri na ina neman littafina na *wa yasan gobe*zan muku typing na nemeshi na rasa Just for fun ga wadanda suka ji haushina *wa yasan gobe?....* Loading.......... *WA YASAN GOBE?....* *PART 2*