Sashe 68
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
iya shiru ba sai kowa ma ya ji,kuma....." Dai dai nan aliyyu ya turo qofa ya shigo,da sauri ya qaraso a rude ganin hawaye kan fuskar fadilan,dagota yayi ya rungume yana goge mat fuskan"me ya faru ?,doctor me kika yiwa mata ta?"ya fadi cikin hade rai,dariya sa'adah tayi "farinciki ne yayiwa matarka yawa,don ance lafiyarta qalau shine don shagwaba take kuka"ta miqa masa takardar magunguna "wadan nan zata dinga sha,but gaba buqatar hutu da kulawa sosai,idan an gama lallashin ku rufe min qofar office din sir,zani inyi round na marasa lafiya,ta sanya lab coat ta fice tana musu dariya" Ko cikin motar kanta na langabe ne jikin sit,gaba daya jikinta yayi sanyi,sai ta ruda aliyyun gaba daya ya kasa driving din dole yayi parking din motar yana tambayarta,murmushi ta saki"am fine my haidar" duk da haka sai da ya sanyata cikin jikinsa sannan ya samu ya iya ci gaba da tuqin,ga zatonta zai maidata ne gurin aiki amma sai taga yayi nassarawa da ita,cikin rashin fahimta take dubansa "nayi zaton zaka maida ni ne office ko tunda ban tashi ba"ya girgiza kai "no fadeelah,yau gidammu zamu koma" da sauri ta dubeshi "gida haidar?,bada izinin su uncle abba ba?" "Shshshshsh!" Yace "nafi kowa iko da ke fadeelah,na gaji da rashinki,na qosa kiyi haquri kawai idan naje gidan ni zan sanar musu,zan fahimtar da su ba laifinki bane,bare ma ba zasu ce komai ba I know" Ta zumburo zata sake magana "tuni ya sanya bakinsa cikin nata ya hanata cewa komai,saura kadan sitiyarin ya kubce masa Allah ya taqaita ya kamo shi Da kanshi ya bude mata part din nata don babu key din a a lokacin a hannunta,sai zumbure zumbure take ita a dole fushi takeyi da shi,shi kam dariyarsa ma yake lokaci lokaci,bai damu ba tunda burinsa ya cika,fridge ya nufa ya ciro ruwa duk da babu sanyi kasancewar wutar bangaren a kashe take,ya jawo gabanta ya durqusa,ya jawo ledar magungunan ya ballo mata,ya bude gorar ruwan sannan ya kalleta "haa" yace da ita,shiru ta masa sai da ya sake cewa "bude bakinki"nan ma tayi shiru,sai ya dire ruwa da maganin kan center ya miqe yana shirin core rigarsa yana cewa "tunda kin zama kurma inada muqullin bude bakinki" a razane ta dubeshi,bata san lokacin da tace "me zaka yimin?"yadda ta razanar da kuma yanayin yadda tayi maganar shi ya bashi dariya,ya tuntsure da dariyarsa yana maida rigarsa da ya soma cirewa har fara qal din vest dinsa ta soma bayyana,ya koma gabanta ya tsugunna yana cewa "ashe dai matsoraciya ce,baki shirya fadan ba amma kika takaloshi,oya bude bakin"bata ko sake musawa ba ta bude ya sanya mata magun gunan sannan yasa maya ruwan a baki har sai da ta hadiye Ya miqe ya cire mata mayafin da dankwalinta,ya zare mat sarqa da dan kunneta duk tana kallonsa,ya debe qafafunta ya maida saman kujera ya dora mata pillow sanann ya harde hannayensa a qirjinsa yana duba agogon dake manne a bango "oya,maza kwanta kiyi bacci ko na one hour ne don maganin yafi saurin bin jikinki,after one hour sai ki tashi kiyi sallah ok?" Cikin shagwaba wadd ta ruda aliyun tace"amma dai kasan ban kyauta ba ace daga zuwa gun aiki ace na dawo gida na ko?"sauje hannun nasa yayi ya dawo gaban kujer ya tsugunna har yana jingina gwiwoyinsa jikin kujerar,ya koma serious sosai,yasanya tafin hannunta cikin nasa,sosai ya sa qwayar idonsa atata "fadeelah" kallon cikin idonsa tayi,yadda taga ya zama serious hakan yasa ta bawa maganar tasa muhimmanci "duk duniya babu mai haqqi a kanki daya kaini,bana so ki dinga sawa ranki damuwa kan binda yake mai sauqi ne,su momi sun ajjiyeki ne don ku sasanta kanmu da kanmu ba tare da kowa ya shiga ciki ba,sannan ni na sake gane kuskure na,to yadda suke so din duk ya faru,me kuma ya rage?uumm?,sai mu dawo gidan mu fadeelah mu shimfida sabuwar rayuwar auratayya wadda zata kuma farantawa iyayemmu rai,ina kuma fatan zan samu goyon baya daga gareki?" Sosai take gyada kai "insha Allah mijina,na yi maka wannan alqawarin" ta dam zamo daga saman k ujerar ta durqusa itama a gabansa "ka yimin afuwa ranka ya baci,ya saki qayataccen murmushi "ba komai baby na,bakya taba yin laifi a guna"ya sumbaceta sanna ya maidata ya kwantar saman kujerar,"kiyi bacci sosai,banda cewa zaki tashi kiyi aiki,gidanki babu dattin komai,don kullum sai na share miki shi"tana daga kwancen ta qwalalo ido "shara?kuma da kanka?"murmushi ya kuma saki"kina mamaki ne?,kinfi gaban haka,mene ke baki bani ba a rayuwarki fadeelah?"itama murmushin tayi "haqqina ne ai In maka har fiye da hakan" "jiniina kai yayi cikin zuciyarsa yana godewa Allah,babu shakka yayi gamo da katar da mace ta gari,wanda samuntabke matuqar wuya a wagga zamani "ina sonki my baby fadeelah har bansan adadi ba,ina alfahari dake,ina alfahari da kasancewarki cikin rayuwata"ta rufe fuskarta da tafin hannunta "ina sonka haidar dear,nima kuma ina alfahari da kasancewar ka miji a gareni har abada"wani dadi yaji ya kama shi,ya sake sumbatar bayan hannun nata yave "na gidewa Allah fadeelah,sai na dawo,zansa nasiru ya kawo miki motarki ,sannan zan daukar miki excuse gurin aiki su baki hutu na sati"bata ce komai ba don bata son ta kasance mai yawan musu da shi,bare itama zata so hakan,don tana buqatqr lokaci da zatayi wasu 'yan gyare gyare,sabida haka kai kawai ta gyada masa tana satar kallonsa ta tsakanin yatsunta har ya fice,wani annushuwa da farinciki da kwanciyar hankali mara misali taji yana ratsata Ta janyo wayarta ta nemo number din farida,bugu daya ta dauka tamkar dama tana jiranta ne,cikin ihu take cewa "yeyyyyyy sister yaushe kuka dawo haka babu labari?"cikin murmushi fadeelah ke cewa "wayyo Allah zaki kashemin dodon kunne mana,cikin satin nan ne,kiraki nayi dama nace miki ki turo min mai gyaran jikin nan don Allah"wani ihu faridan ta sake saki cikin dariya "kai mutuniyata,wallahi da labari,tafiya tayi kyau mune winners ko?" "Kai....faridaaaa....sai yaushe zaki girma ne don Allah?" Tayi qasa da murya "kai sister,rowar story zaki mun kenan don Allah?"dariya ta bawa fadilan don tasan farida akwai son jin tsurku "hab abokin kuka ai ba'a boye masa mutuwa,zaki sha labari har sai kin gaji kin toshe kunnuwanki" "a'ah nasan halinki fa sister,zaki dai bani wanda kika ga dama,yanzu zan mata waya na gaya mata"tayi dariya "yauwa ko da yamma ne sai tazo,sau nake ta fara yimin yau don gaskiya nag ta iya" "kai sister sosai ma,ko sau daya fa ta miki sai kinga kin canza gaba daya,akinta da kyau sai tsada,bayan gyaran jiki har kitso da qunshi ma ta iya sosai" "to yayi,ina humairata,Allah sarki aishana,nayi missing dinta a lot" "Yanzu babanta ya fita da ita sitting room yayi baqi"hamma ta kubcewa fadilan har sai da faridan taji "idan sun shigo kice ina gaidasu ita da abban nata,ni zan kwanta" Dariya farida ta saka "tabdi lallai sister,kai saidai na zo kawai" Katse wayar fadila tayi taba murmushi don tasan halin farida bata qi su kwana suna abu guda ba......... *Mrs muhammad ce* [12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed *WA YASAN GOBE?...........* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 3* 2 Doctor sa'adah ta kammala rubuce rubucenta,ta dago ta kalli aliyyu "masu qaramin ciki kamar hakan suna buqatar daga qafa adinga sassauta mata gaskiya" Zaro ido yayi kamar yaro"what?!,su waye Duke da ciki?"cikin mamaki ta sake dubanshi "oh,baka sani ba.....anyway kaji a bakinta,ga magunguna nan ,ba za'a yi birede a gaba na ba,idan kun tafi nurse zata zo ta kulle qofa"tayi haka ne don tasan za'ayi budurin yadda tasan alin da son yara na masifa A hankali ya duqa gabanta "da gaskene Fadeelah kina da ciki?"cikin jin kunya ta gyada kai,sai ya hade fuska tsam,ciki tsawa tace"don me yasa zaki boyemin kyautar da Allah yayi min?shin ban can can ci in sani bane?" A Dan tsorace ta kalleshi,sai Kuma taga ya rungumeta "am sorry dear,banji dadi bane da kika boyemin,kunya Daren jita na cutar da ke,da wa ni Abu ya faru daku keda baby na bazan yafewa kaina ba Fadeelah,bazan gaji da roqamiki rahamar Allah ba,bazan gaji da roqarmiki albarkar ubangiji ba,ke din wa ni alkhairi ce a tartare da ni ,bani d halin da zan miki godiya don tayi kadan,bansan da me zan saka miki da shi ba fadeelah,Abu day dai da na sani kin zama mahadin rayuwata Fadeelah,na tabbatar idan babu ke rayuwata bata da amfani" Ga mamakinta sai taji ya fashe da kuka sosai,tabbas rabo ajali,rabo ne mai zafi ashe tsakaninsa da fadilan,hawayene sosai ke sauka bisa fuskarsa,hakan ya sake nunawa fadila yadda Aliyyu ke tsananin son yara,ita din ke share masa hawaye tana lallashinsa "Allah shi ya cancanci ka godewa bani ba,ni da kai duka bayinsa ne yadda yaso haka zamu gani" Baiyi qasa agwiwa ba Kuwa ya kama"alhamdulillah"ba qaqqautawa "Allah ka yimin dukkan wata ni'ima a rayuwata,Allah ka bani ikon saka maka ta hanyar yi maka da'a da biyayya da bin dukkan wani umarni naka" Addu'ar d aliyyun y dinga yi kenan gwiwoyinsa kafe a qasa hannayensa a sama,ba fita daga asibitin ba sai da ya yiwa doctor sa'adah albishir din Kujerar umrah,fadilan ma ha ata tafiya yayi ya kafe sai dai ya dauketa,sai da tasa masa kukan shagwaba sannan ya bari,roqarsa ta dinga yi cikin mota don Allah kada ya fadawa kowa Girgiza kai yayi"mummunan labari ake boyewa,ban miki alqawari ba ruhina,na dai yarda bazan fada ba amma Duk wanda ya tambayeni zan fada masa"ba yadda ta ita haka ta qyaleshi,motsi kadan yace"sannu,yaya?" Tun tana amsawa har ya soma bata dariya, Marairaice masa tayi kan sai ya kaita gida taga umminta,dole ya kaita ganin tanason sa masa kukan nan nata da ba yaso,tayi Sa'a kuwa ta tadda Farida tazo,wayyo dadi gun Fadila ba'a magana,humaira nata rarrafe abunta,yarinyar ta sake kyau kamanninta da fadilan ya sake fitowa,sai ta sake shiga zuciyarta,Fadila na shirin daukarta ummi tace"Allah yasa ta yarda da ke 'yar nema,wai nan qiwa fa take"sai kuwa ta ba su mamaki don luf tayi abunta jikin Fadilan Can jimawa saiga 'yan biyun Anty hafiza,tunda cikinta ya tsufa ya Ahmad ke tarkatosu gun ummin lokaci bayan lok ci musamman weekend dob mamansu ta huta, ummi ce ta kalleshi"gayamin kwana nawa za suyi,don bazasu zo tafiya amira rigima ba"yayi murmushi"anjima ma zan dau ke su,idan natashi daga kasuwa,naji tana gobe can gidansu za'a kaisu za suyi taro"