Sashe 51
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
cikin ya maida qwayar idanun nasa cikin nata,ya karanci ta tsargu don haka sai ya waske ya bata rai hadi da janyo warmer yana budewa gami da cewa "no ni banga yayi full ba,don banga ya daga ba" ta marairaice tuni qwalla har ta cika mata idanu "I swear idan ka qaramin zanyi amai wlh Allah haka cikina yake" da mamaki can qasan ransa ya tsaya da abinda yake din,dama akwai mata masu irin wadannan halittar cikin?,ya riga da ya saba da matansa masu tumbi Ya koma ya jingina da kujerar da yake kai yana cewa "ok remove dis items,but be careful with your wound,dama neman mafita taje don haka da rawar jiki ta tashi ta soma gyara gun ,cikin kitchen kitchen tafi minti biyar tana dafe da qirjinta idanunta a lumshe kafin yanayinta ya daidaita "me ya sauya shi haka" can qasar zuciyarta take tambayar kanta *Mrs muhammad ce* [10/16, 2:00 PM] Salma *WA YASAN GOBE?...* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *part 2* Ta dade kafin ta baro kitchen din har yanzu yana dining area bisa kujera yana danne dannensa a waya,a falon ta tsaya ta jawl computer din ta ta tafi da gidanka(laptop) ta bude tana shirin kunnawa "hey stop" taji ya fadi cikin wata iriyar murya mai kama da ta mai jin kasala,kasaqe tayi tana jira taji mai zaice "shutdown ur system yau ba daukan lecture,kin mance wound dake fingers dinki ne?" Sai ta rasa mai zata ce tana ganin ai hannunta bazai hanata lecture ba koda guda daya zata iya yi,amma da yake mutum ce ba mai son jayayya ba don haka ta kashe din ta koma ta zauna hadi da zubawa sarautar Allah ido Tana zaune ya shiga ciki yayi wanka ya shiryo cikin kayan sanyi,kan kujerar dining din dai ya koma ya zauna,babu dadewa kuma door bell ta kada,ya dubeta sannan yace "put your hijab" mayafine yafe a jikinta bayan kayan sanyi masu kauri da tasa,nan ma dai bata tanka komai ba ta koma daki ta dauko hijabin,ko da ta dawo su biyu ta tarar shi da doctor yungpho,ta samj kuje daya ta zauna doctor yungpo mutumin china na gaidata cikin harshen turanci Suna gefanta doctor ya gama duk hwaje gwaje da tambayoyinsa,ya dago yana duban aliyyu "sir,sanyin garin mu na son taba ka gashi kana kwanciya a inda zai iya affecting health dinka,ya kamata ka kula saboda kada yayi maka yawa ya zamarmaka illa" "ok" aliyyun yace, "sannan ciwon cikinka ciwon marasa aurene me yasa ya taso maka a yanzu bayan kana da aure?...." da sauri aliyyun ya katseshi yana satar kallonta duk da kanta baya fuskantar gun amma hankalinta na gurin haka nan kuma ta dago wani abu duk da ya katse doctor din Magunguna doctor yungpo ya bashi yana shirin hade kayansa aliyyu yace ya bashi pain killers" ya hada masa duk cikin magungunan,fitarsa babu dadewa aliyyu yasa ta bashi ruwa yasha magungunansa,tamiqa masa ita kuma ta wuce kitchen da zummar dora abincin rana tunda taga alamun da qyar idan yau zaya fita Sai tsintar aliyyun kawai tayi cikin kitchen din ya damqota yayo waje da ita,saman kujera ya zaunar da ita yana ware mata sexy eyes dinsa kamar wata qaramar yarinya "idan kika sake jangwale ciwonki I will wash it again budewa zanyi in sake wankewa no pity ok?" Tayi qasa da kanta tana kallon yatsan nata mai ciwon,muryarta so cool tace "lunch zan hada mana ne" "we don't need" ya fadi yana juyawa "wo hoho Aliyyu.......Aliyyu...." fadila ke fada cikin zuciyarta,ya sata hutun dole kenan?....... Babu karatu babu girki?.....fine" ta fadi tare da yin kwanciyarta saman three sitter Wunin ranar tana zaune ita dai sai gani tayi an kada qararrawa da rana an kawo musu lunch hakanan da daddare,coffee kawai ta faki idonsa ta hada,shima tana dire masa ta bar bedroom din don kada yace zai mata fada,sai da ta kintaci kamar yayi bacci sannan ta koma,cikin sanda ta salallaba ta hau daya side din tana jan bargon zata rufa taji ance "good" ta zaro ido tana shirin sake jin mai fada,jin yayi shiru bai sake cewa komai ya sanyata jan bargo ta lulluba tana addu'o'inta cikin zuciyarta tana yiwa kanta dariya,wato ita mai wayo taqi shigowa ta gudu sai yayi barci ashe idanunsa biyu,ta saki ajiyar zuciya wadda ba don kwanciyar kai da qafa sukayi ba da zai iya jiyota Yafi awa biyu yana yaqi da zuciyarsa,qamshin turarenta ke ban banta masa tunani,ya rasa wace iriyar masifa ce,sosai ya san yana cikin wani hali amma baisan me yasa ta sanadiyyarta yake samun kansa cikin wannan halin ba,sunsha zama haka shi da salima idan ta masa laifi don ya hukuntata,suna daukan tsawon lokaci a haka ba tare da kuma ya damu ba,saidai ita ta gaji ta hanyar gyara laifin da kuma bashi haquri,ya runtse ido,da qarfi yake son tilastawa kansa sai yayi bacci,da qyar wani wahalallen bacci mai cike da mafarkai yayi awon gaba da shi Kwana uku tayi babu cas babu as,duk abinda ta dauka zata yi sai yace "stop it,hatta da shara kuwa kawai akan dan yatsanta guda daya,saidai ta faki idonsa ta kimtsa inda taga bai dace ace ana barshi haka ba,da zarar kuwa yazo yaga alamun hakan zai zuba mata ido wanda ta fassara shi da *eyes punishment*,sai ta sunkui da kanta kawai ta wuce sum-sum-sum ta bar gun,kwana biyu yana gida yana jinya babu inda ya fita,sai a rana ta ukun ya koma kan ayyukansa Sosai itama ta rungumi karatunta tana jin dadinshi matuqa ta bashi mahimmanci mai matuqar tasiri don ta sani zai sake jawo mata qwarewa da kuma daukaka ta fannin aikinta,hakanan tana sake samun goyon baya da qwarin gwiwa daga gidajen rediyoyin da take mu'amala da su,su kansu ko yaushe suna fadi mata yadda sukayi missing aikace aikacenta masu cike da inganci da juriya _*SANADI*_ Cikin nasarori masu tarin yawa dukkan wani shirye shiryen bikin bude kamfanin suka kammala,cikin watansu na uku da sati na uku a qasar ta sin,wanda cikin lissafin da fadika keyi kwanaki goma daka iya zuwa a gaba koma sati guda wato next week zasu iya komowa gida,tun sati uku da suka gabata ta kammala naga coarse din ta kuma fita da sakamako mafi kyau duk cikin daliban Tuni ya sayi injina masu kyau ya aiko da su gida ta container din max air wanda na wasu kamfanoni ne da yakeson budewa idan ya dawo gida a kano cikin rukunin kamfanoni dake sharada industrial area Tsaye take a kitchen sauri sauri take ta kammala girkinta saboda yau tayi late sosai,sanye taje cikin trouser na mata sai rigar sanyi in and top ta saqa ce irin saqar turawa,yar cikin har gwiwa take mai gajeran hannu ta saman ce iya qugu mai dogon hannu,wuyan rigar yankan *V* shape ne,ta taje baqi sidik din gashinta mai sheqi ta sake shi ya sauka gadon bayanta,kanta na saye da hular sanyi na mata mai wadda a jikinta yaje saqale da teddy's qananu,shigar dark pink tayi tayi masifar yin kyau kamar wata black American Hankalinta sosai yayi gaba,ta bada duk wani attention nata kan girkinta don hatta dan siririn mayafinta da tadan yafa da hular kansu sun zame don haka ko shigowarsa bata ji ba,fresh milk shi din ma ya shigo dauka hade da ruwa don busy din da tayi yau ya sanya ta mance bata ajjiye masa ba yadda ta saba,wani strong abu yaja hankalinsa sosai game da ita,sai ya koma jikin freezer din ya jingina ya harde hannayensa saman qirjinsa kamar yadda ya harde qafafunsa yana bin duk wani moments nata da kallo Sosai ta tsorata lokacin da ta juyo zata dauki ragowar markadaddun kayan miyan da ta sanya a fridge saboda ganin mutum a tsaye unexpected,tsananin tsoro ya kamata tayi baya zata qwalla qara don rudewa ma bata barta ta kalli fuskarsa ba sai kuma ta taka bawon doya ta zame tana shirin shan qasa saboda santsin tiles da doyar ga kuma ruwa Gaba daya taji ya rungumeta tsam cikin jikinsa yayi hada bakinsa da nata don hanata yin ihun,zaro ido tayi,cikin yan sakanni ya soma kashe mata jiki saboda yadda yake sarrafa bakinsa cikin nata tamkar ya samu sweet qamshin turarenta na dada ingizashi,cikin lokaci qanqani ya soma burkice mata har ya fara bata tsoro duk da ita din ma tana cikin shauqin abinda yake matan,wannan shine karo na farko da ta soma hada jikinta da wani da namiji a rayuwarta Caraf tayi qarfin halin riqe hannunsa jin yana qoqarin shiga wani fage,sai lokacin da ta hada hannuntabda nasan sannan ya soma dawowa saitinsa,cak ya tsaya da abinda yake yi din,cikin sauri ta 6ashi daga jikinsa tana maida botiran rigarta hadi da maida gashinta baya wanda tuni ya hautsine,kunyan da tsoro suka hanata tsaiwa ina zata boye?,bedroom nasu ne su biyu duka,kitchen gashi a ciki,gudu gudu sauri sauri ta nufi qofar ventilation da niyyar ficewa "Hey you" taji aliyyu wanda ke jingine jikin kantar kitchen yana maida numfashi yace "cak ta tsaya ita bata qarasa ficewa ba hakanan bata juyo ba "duba girkinki it burns",sai a lokacin ta tuna doyarta data dora *mrs muhammad ce* [10/16, 2:02 PM] Salma *WA YASAN GOBE?...* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *part 2* Verry slowly ta juyo kanta a qasa ta kashe gas din ta sulale ta fice ya bita da ido,sirrintacciyar ajiyar zuciya ya saki jikinsa a mace ya juya ya dauki abinda ya kawoshi Tamkar sirikinta haka ya koma mata gaba daya taqi koda kallonsa a haka ta zuba masa abinci ta miqa masa taja kujera ta zauna tana wasa da nata abincin sai jagwalgwalashi take da spoon baice da ita komai ba har kammala nasa,sai da ta miqe tana shirin hade kwanukan ta maida kitchen taji yace "baki isa ba sit and eat" ya tabo mata abinda taqi jini wato ace taci abinci,ta langabar da kai cike da fargabar ya za'a yi ta iya cin abinci yanzu?,ita hasalima tun abin nan da ya mata dazu taji cikinta ya cike amma taga ma shi ko ajikinsa tamkar bashi yayi ba,tamkar ba aliyyun nan ba kamar kullum canza shi akeyi Da qyar tayi spoon biyar ta fara yunqurin amai "stop don't vomit,go" hakan dama takeson ji saboda haka da sauri ta kwashe kayan ta maida su,sai ta kasa zama afalon