Sashe 8
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ya faru haka?"fadika ta sake fashewa da kuka tana cewa"na shiga uku anty,innalillah,anty zuciyata bata yimin adalci ba ta jefana cikin mawuyacin hali,anty ki taimakamin,me yasa zuciyata ta yimin hka anty?why?why?, Anty hafiza ta dafa kanta tana shafawa tana cewa"calm down ki nutsu ki gayamin meke faruwa?" Tasa bayan hannunta tana share hawayen dake kwararo mata sannan ta saki ajiyar zuciya tace"anty tun kafin na San shi waye zuciyata ta dade da kamuwa da matsananciyar soyayyarsa ,tun daga lkcn na rasa sukuni a zuciyata kwata kwata,kullum kwanan duniya qaunarsa na qara ninkuwa ne a zuciyata kamar jaraba abun,ina cikin wannan haline muka fara face to face da shi saidai abu na farko da ya fara shiga tsakaninmu fada ne,hakan ya zamana har zuwa lkcn da mahaifin Aliyu salim maitama ya nema masa arena gun abbammu ba tare da nasan shine ba,na shiga matsananciyar damuwa a lokacin da ta bayyana an bada arena ga wani,sai dai sanda nayi tozali da aliyu a matsayin wanda aka bawa ni sai farinciki ya mamaye damuwata Sai dai kuma me?anty ga tarin mamaki na sai kalaman qiyayya suka zamo kalaman farko da na fara samu daga masoyina,kalaman da suka kusa tarwatsa zuciyata ,qarara aliyu ya nunamin bai qaunata ba nice choice dinsa ba samirah ce muradinsa,meye aibuna naty?wane naqasu nake da ahi wanda ya janyo aliyu ya tsaneni?ban can can ci so bane daga gurinsa bane anty? Aliyu yana sonki zai kuma soki fafila"ta fada tana girgiza kafadarta,kukanta ya tsaya cak sai hawaye dake shatata ta ski baki tana kallon anty hafizan da itama ido ta zuba ma ta tashiga girgiza kai tana cewa"bazai soni ba naty baya kuma sona din ya fada anty da bakinsa fa yace"kada nasan ran wata ran zai soni"anty hafiza tayi saurin tarar numfashinta tace" ke da'alla can rabu da shi shike da kansa?WA YASAN GOBE?ai sai allah"ta karyar da kai cike da neman agaji da mafita "amma anty haka zamu rayu da shi?rayuwar aurece naty wadda ba yau ko gobe za'a yita a watse ba" anty hafiza tayi murmushi tace" ki kwantar da hankalinki,abu na farko da nake so gareki shine ki miqawa allah lamuranki babu abinda ya gagari allah,abu na biyu ki zamo mai juriya haquri gami da kawaici ki zamo mai controlling din anger dinki ,ni kuma insha 'allah nayi alqawatin doraki akan step na gaba,nayi alqawarin baki shawarwari na gari harsai inda burinki ya gama cika Cikin hikima da dabara ta zauna tana bude mata babi babi na hikima da dabarun zaman tare gamida kwantar mata da hankali har fadila ta ji nutsuwa ta shigeta tace ni anty abinda ke dada tayr min da hankalin ganin yadda nake jin zallar soyayyarsa a zuciyata to shi haka yake jin zallar qiyayyata"tave cool down sister na gaya miki kada ki damu irin wananna ita take fa juyewa wata rana ta zama zazzafar soyayya ke dai ki dinga yiwa soyayyar tasa linzami kada ki bari ya fuskanci akwaita a ranki don kada ya samu jin dadi da sakewa na wulaqantaki harsai lokacin bayyanatan ya yi Daf da sallar magariba yaya ahmad ya dawo bayan sun gaisa yake zolayarta"lpy kuwa amarya n ga tana ta qarewa haka?"tayi murmushin yaqe tace lpy lau yaya"anty hafi a tayi saurin tare tambayar ta hanyar cewa"abban twince a kasan fama haka na faruwa ga mutum idan aurensa yazo"ya girgiza kai xikin gamsuwa da bayaninta yace"hakane aure yaqin mata,Allah yasa ayi a sa'a"anty hafiza ta masa amin Bayan isha'i tayi haramar tafiya bayan anty hafiza ta tsareta dole ta sata cin abinci ,antyn ta rakota bakin mota tana sake kwantar mata da hankali fadilan ta dubeta tace"anty unason don Allah ya zama sirei wannan zancan""haba f fila kada ki damu dake da aysha daya nake daukarku(qanwarta ce aysha)fadila tace anty na gode Tana driving tunani ne fal cikin ranta duk da tana jin ta samu relief sosai cikin ranta,ita kanta mamakin kanta takeyi tasha jin yadda mata 'yan uwanta ke yaba kyau da ajinta bare maza wadanda ita kanta batasan adadin masoyanta na dili da na b ue ba wadanda ke jatumtar sanar da ita da wadanda take musu kwarjini suke batin abuna zuciyarsu,wadanda ke kuka akanta bazata.iya tuna yawansu ba don ita dama Allah bai dora mata kule kulen samari ba amma yau kamar almara sai gata a wata wawakekiyar qofar jarrabawa,ta saki ajiyar zuciya sanda ta iso bakin get din gidan malam sani ya budw mata qofa ta shige ta tsaida motarta bayan ta daidait parking,a gefabta taga motar farida hakan yasa ta gane sun dawo,ta saki doguwar ajiyar zuciya tafito daga motar ta kulle ta tunkari falon nasu MRS MUHAMMAD BELLO 07066139278 [10/16, 2:39 PM] +234 706 914 1005 : 8:39 pm Wa yasan gobe? Written by safiyya Abdullahi musa huguma