Sashe 21
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sanya kukanta katsewa ta tashi kamar mai sanda ta isa window dinta da yake cikin balcony dinta ta yaye labulen ta riqeshi a hannunta,daga nan tana iya hango dukkq sararin gidan samira ce ke wannan hayaniyar cikin hargowa da babat tanajanyo akwatina irin wanda nasiru ya kawo.mata dazu daga part dinta daya bayan daya tana cillarwa anan tsakiyar filin gidan ko nauyinsu bata ji ,aliyyu na tsaye hannayensa harde a qirji ya zuba mata ido bai ko motsa ba Sai da ta gama lodesu sanna tayi cikin gidan nata a fusace sai gata da gallon da ashana ta daga tana qoqarin bulbula musu fetur din da yake ciki sai a lokacin aliyyu yasa hannu ya fincikota baya a fusace ya nunata da dan yatsa yana cewa kul kada ki soma,ta dubeshi duk da ta tsorata da yanayinsa amma sai ta dake cikin bala'i take cewa" sai na qona aliyu sai na qona wallahi kayan fadar kishiyan wata tsiya ce,sai dai idan na qona idan ka so nima ka qona ni" ta sake zabura tayi kan kayan da nufin idar da niyyarta cikin qaraji da tsawa ya ambaci sunanta wadda sai da hantar cikinta ta kada amma sai ta waiwayo tace"ko kasheni zakayi ba zan fasa ba" tadai sake nufar kayan cikin azama a karo na uku,cikin fusata yasa hannu ya janyota baya harsai da ta zube warwas a gun tamkar ya bita ya tattaka haka yake ji,don da namiji ne ya masa haka to yanajin ba shakka sai ya nuna masa qwarin qwanjinsa Ta sani cewa idan taci gaba da abunda take hukuncin da zai yanke mata ba mai sauqi bane hakan yasa tana daga zaunan ta hau borin kunya cikin surutai da maganganu marasa kan gado daga baya ma da taga ya qi kulata sai ta fashe da kuka Ko kallo bata isheshi ba ya dinga siban akwatunan bibbiyu bibbiyu ya shigewa da au bangarensa yana gamawa ya rufe qofarsa ya barta a nan,data waiga ta waiga taga ba kowa ba wanda ya gansu sai ta goge idonta ta miqe tana kade zaninta tana wa allah godiya da ba wanda yaga abinda ya faru tana yi tana tsinewa hannatu qanwarta gashinan ta jawo mata asarar akwatinan ma dungurun gum dan ita ta bata shawarar tayi haka A falon sa ya zube ya dafe kansa hannu bibbiyu yana tsananin jimanta al'amarin to haka mata suke ne basu da hangen nesa ya jima a haka sannan ya tuno bai ma shiga bangaren dayar ba kamar yadda yake ce mata a ransa"itama idan ka shiga wataqila haukan da zata yi maka kenan"wata zuciyar ke gaya masa,ba yadda ka iya tunda itama aqarqashinka take kuma ka shigarwa 'yar uwarta indai adalcin kake son yin Da sallama ya shiga ta amsa a sanyaye tana zaune ne kan kujera hijabin da tasa ta budewa masu shigo da kaya har yanzu shine a jikinta saidai sabanin da yanzu akwatinan a rufe suke,a fakaice yake dan nazarin falon komai tsaf yake cike da tsafta da qamshi hakanan komai a killace yake a muhallinsa da kyawunsa kamar yau aka jerashi sabanin falon samira da komai ya fita hayyacinsa saboda rashin kulawa duk da dama tsadar kayan ma ba daya bane don iyayenta basu da qarfin iyayen fadilan,kanta na qasa ta dam zamo daga kan kujerar tace ina wuni? Duk da bata sa ran masawarsa ba don bai taba amsa gaisuwarta ba ga mamakinta wannan karon sai taji yace "lpy ga kaya nan abinda babu ko baiyi ba sai ki yi maga ko ki rubuta ta girgiza kai tana cewa komai yayi mun gode Allah ya qara arziqi" ya lumshe idanunsa don har zuciyarsa ya ji dadin addu'ar "madalla" yace ya zaro bandir na dubu dubu guda uku ya dora saman akwatinan ya juya ya fice sai yaji wani sauqi na radadin da zuciyarsa ke masa addu'ar ta faranta ransa don tunda yake bai taba samun kwatan kwacin wannan ba daga bakin wani abu wai iyali ba Muje zuwa yanzu aka soma Mrs muhammad 12:45 pm 03/11/1437 WA YASAN GOBE? Written by safiyya Abdullahi musa huguma Ana ya gobe daurin aure su anty hafiza anty hauwa farida sumayya rabi'ah har da rahama suka zo wa fadila,farida ta zube dinkunan da fadila ta bayar aka mata sunyi matuqar kyau da gaske duk da tana da sababbin din kunan ma da bata taba sa su ba,kala ashirin farida ta zabar mata aka dinko su lace biyar atamfa biyar shadda biyar material ma biyar ne,anty hafiza ce ta taho mata da mai gyaran jiki gashi da lalle takanas sai hade haden magunguna namu irin na mata imgantattun na 'ya'yan itace,anty hauwa sai dariya take tana cewa o'o'o fadila 'yar gata to ai ko kece amaryar sai haka,sai dai tayi dariya ta sunkuyar da kanta qasa cike da kunyarnan ta ta,anty hauwa ta zuge jakarta ya fito da littattafai tace ga saqon momi nan,hannu biyu tasa ta amsa tana godiya litttafai ne kusan goma na addu'o'ine da kuma gyara zamantakewar aure, Zuwansun ya sake debe mata kewa taji dadi nan suka fara tsara yadda za su gudanar da yinin su na gobe wanda ko wacce mace da za'a qarawa abokiyar zama ke gudanarwa,wuni akai ana qalqale mata jiki yayin da su rabi'ah sumayya da rahama suka zage wajen qal canzawa gidan fasali,sune canza labulaye canza carfet goge goge da ahare share duk da komai na fadila tsaf yake sai abinda ba'a rasa ba,cikin qanqanin lokaci kuwa gidan nata ya canza kamar ba shi ba,hatta qamshinsa sai da aka canza kalarsa ya zama na musamman abinka da diyar bare bari Rahama ke tambayar fadila samirah fa?fadila tace wlh tun safe dai naji tashin motarta amma ban sani ba ko qunshin itama ta tafi "Allah ya kyauta inji anty hauwa ,bayan isha'i komai ya kammala anty hauwa tace zasu wuce sai gobe kuma idan Allah ya kaimu anty hafiza da yake kwana za suyi ita da farida tace"dama kwanciyar ku muka yi maman kausar wlh ,a'ah hafiza na bar yara su daya a gida daga su sai Abbansu wunin yau fa duka?"anty hafiza tace to don Allah ga laila(mai qunshin da ta dauko)ku sauke min ita a dorayi Suna kan gado duk su ukun sunyi shirin yin bacci hafiza ta zubawa ido dake qoqarin shafa addu'a tace wai yau wa kuka barwa mijin ne?samira fa bata dawo gidannan ba haka kuke masa?"cikikin son rufe sirrinta da son gyara rayuwar aurenta ba tare da taimakon kowa ba tace "girkin samira ne anty bana son neman rigima da tashin hankali me zani in masa tunda ba girkina bane?salin inje mu raba dai abun fada?"daga haka suka qyale zancan Washegarin aka zo akawa salima jeranta da yake aikin maza ne nan da nan yayi sauri amma akwai wasu daga cikin yan uwanta mata da suka zo da su,girkinsu su fadila sukayi sosai suka zuzzuba a manyan warmers suka aikawa yan uwan salima da wani wasu kuma suka barshi nan cikin kitchen dinta saboda mutane yan uwa da maqota da keta zuwa Allah ya sanya alkhairi har a lokacin sashin samira na kuelle ne alamar bata dawo ba kenan hakan yasa kowa ya shigo gun fadila yake yowa idan suka tambayeta samira sai tace ta tafi gidan qunshi Ba qaramin kyau fadila ta zuba ba tamakar ita ce amaryar daga wayewar garin zuwa yanzu ta sanya kaya kusan kala takwas kenan har harabar gidan jama'ace don babu laifi yan taru duk da ba wanda suka gayyata Qarfe sha daya da rabi na rana aka daura auren Aliyyu salim maitama da salima tukur Abubakar,kasancewar gidansu salima na na unguwar dake daura da g.r.a ne yasa yanuwan fadila na jiki da suka halacci daurin auren suka dinga zuwa ana gaisawa suna tafiya ciki kuwa harda abbanta da muhammad da ya ahmad taji dadin zuwan hakan kuma ya faranta mata ranta don tun da aka daura aurenta rabonta da taga abban nata kuma shima yaune zuwansa na farko gidan nata,ya mata nasiha sosai da ta qara mata nutsuwa ta kuma sata kuka ta sake tabbatar da cewa ba qaramin zumunci bane tsakanin abban nata da uncle abba mahaifin aliyyu tabbas babu abinda zata wa abban ta aduniyar nan fiye da ta jure zaman aure da aliyyu,anan suka bar mata muhammad zuwa yamma abban zai turo a daukeshi Qarfe sha biyu da rabi ta sake wanka ta sanya wani Swiss lace pink ne mai dan turuwa kadan sai kore aka masa da ratsin silver din zare sai manyan dutsina masu walqiya sarqarta abun hannu da dankunne mayafi da takalmi duk silver ne dinkin riga da skert aka mata skert din eight pieces ya bude daga qasa sosai ,yayi matuqar karbarta ya haska chaculet din fatarta gashinta mai tsawo da santsi da baqi ya sha parking da pink and green din ribbom sai ya kwanta a bayanta sai sheqi yake tayi daurinta das wanda ya ta qasansa gashin nata ya fito,ta dauki turare tana fesawa taji ana kiranta maqotanta sun shigo kuma wasu na nemanta a harabar gidan saurin da take yasa ta manta bata dauki mayafi ba,suka gaisa da baqin tasa aka kawo.musu abinci sannan ta qarasa harabar gidan, nasiru ne da wasu mutane suke neman gun jibge abincin da ake ta shigowa da su,ta nuna musu store dinsu dake harabar gidan ta farko kusa da parking space Tana shirin shigewa ciki motocin suka soma danno kai suna parking daya bayan daya,bata fuskanci su waye a ciki ba sai da suka cika harabar gun dukkaninsu cikin fararen kaya suke,Aliyyu ta hango a tsakiyarsu fuskarsa nata fitar da wani annuri cikin wata rantsatstsaiyar shadda babbar riga da yar ciki sai wando zata iua cewa bata taba ganinsa da irin wanna shigar ba ya qara wani kyau da kwarjini sosai ta shagala da kallonsa har suka hada ido Haushi ne da takaici suka cika shi ganin yadda tayi kwalliya kuma ta fito har kusa da get a haka na tare da tayi lullubi ba,yayi mata kallon nan nasa data tsana wanda ya saba yi mata hakan yasa ta tuna a uadda ta fito fa tayi saurin shigewa cikin jama'a ta bacewa ganinsa Tana zaune cikin baqinta sumayya ta shigo tace anty kije inji yaya sai taji maganar banbarakwai gabanta kuma ya fadi tace yana ina?yana