Sashe 25
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da hanata tafiya tana gaya mata saurin fushi ba nata bane yanzu da sauran lokaci dai,kujerar da ta tashi a kai can ta koma ta zauna tana qoqarin maida kukanta ta canza tasha zuwa mbc boollywood ta tarar suna film din kuch kuch hotahie tsohon film ne amma bata gajiya da kallonsa Ta kasa hankalinta kusan gida uku kason farko na kan aliyyu ne da taga ya ci gaba da danne dannensa a computer ya shanya abincin,na biyu na kan matan gidan da ta ga har yanzu ba wadda ta leqo da niyyar yi masa barka da dawowa ashe haka suke masa har ita din?,na uku kuma ta dorashi kacokam ne bisa t.v dake gabanta sai ka rantse da Allah ta bata hankalinta ne gaba daya Ta gefan ido taci gaba da satar kallo da nazarinsa sanda taga ya rufe computer din ya sauko qasa mamakinta zaman da taga yayi zamane irin wanda annabi yake yayin cin abincinsa mamakinta ya sake qaruwa ne sanda taga yayi bismillah ya sa hannunsa ba tare da ya nemi cokali ba A hankali taci gaba da bi biyarsa da idanunta,yanayin yadda yake cin abincin a nutse yq burgeta tana ankare da shi har sanda ya cinye ta biyu ya soma cin ta uku,ranta yayi mata dadi ganin yadda yake cin abincin bisa dukkan alamu yayi masa dadi Hankalinsu dukkansu ya kai bakin qofar jina naturo ta,saluma ce ta shigo da yalwar fara'a a fuskata amma sai taja tayi turus ganin fadila a falon,cikin iya tsabar duniyanci da iya waskewa ta gayyato fara'a fuskarta ta dubi sashen aliyyu tace" a'ah dear inacan ina zullumin yau ka jima baka dawo gida ba"ya miqamata hannu sanda ya sa lomar tuwo a abakinsa yana mata nuni alamar ta taho ,ta taho din kuwa ta zauna kusa da shi sai da ya hadiye sannan yace almost one hour da wani abun da dawowata na gajine shi yasa ba wanda na nema"da ido ta nuna masa fadila tana masa nuni da ita ya akai tasan da dawowarsa har ta rigata zuwa?,dauke kai yayi kamar bai fuskanci abinda take nufi ba don ba'a haka shi da shi,itama tasan hali don haka ta bar maganar Murya a anarke tace dear dama zancan ankon lubabatu ne qawata da nayi maka,kudin nakeso na karba don banason in zama a qarshe saboda baka fiya samun mai kyau ba"ya gyada mata kai yana ci gaba da cin abincinsa,ta tsare shi da ido ganin baice komai ba bayan gyada kan sai tace sake cewa naji kayi shiru baka"ya dago cikin qosawa yace ba munyi maganar ba tuntuni ba kuma ana amsa miki kuma yanzu baki ga abinci nake ci ba" tace cikin son wayancewa ok takai dubanta ga abincin gaban nasa sannan tace" dear yaushe ka fara cin tuwo?"kai tsaye yace "yau"cikin mamaki ta maimaita yau" ya gyada kai yace "yes"sai kuma tace ammafa nima abincin ya burgeni bari muga"ta tsoma hannu a plate din nasa,aliyu ya tsaida cin abincin ya bata fuska ya dago yana dubanta "repeatedly am telling you duk sanda kika soma cin abinci ba tare da kinyi bismillah ba kina cine tare da shaidan ko?" Ta dan dafe kai tace oh sorry na manta bismillah amma fa abincin nan dear yayi sosai a wane restaurant ka siyo" na gida ne ya bata amsa ya dan dubi sashen fadila wadda idan ka kalleta a zahiri zakayi tsammanin kallin film dinta takeyi haiqan sai dai duk tana jinsu tayi kunnan uwar shegu da su,salima ta fuskanci abinda yake nufi don haka ta tsuke bakinta tana da na sanin yabawar da tayi wa abincin din bata yi tsammanin fadilan ce tayi ba Salima na ta zubawa aliyyu surutu jefi jefi yakan tanka mata har suka kusan tashi da abincin gaba daya har farfesun kifin,suka gama aliyyu ya koma kan computer dinsa ya ci gaba da lissafe lissafensa na kayyayakin dake cikin store da wadanda za'a zuba sababbi da kuma wadanda ya saba rabawa yan kasuwan Har kusan tara na dare salima na zaune taqi tafiya,cikin haka saiga samira itama ta shigo yanayin samira ne yasa sauran kadan farida ta tuntsure da dariya duk da quncin da zuciyarta ke ciki,nikam safiyya kasa daurewa nayi sai da na dara har sai da maman walid ta rufemin baki don kada su ganni Zanin shadda ne a jikinta rigar atamfa dankwalin material,har abada ba zaka ga kwalliyar samirah cikin gidanta ba idan har kana son ganin kece ado tofa saidai idan fita zatayi cikin qawaye takan ce kada a raina min wayo ina gidan nera dole na dinga keta shiga da kowacce mace zata kiyayi kanta tasan tana tare da matar Aliyyu salim maitama(kunji wata toshewar basira fa) 03:15 pm WA YASAN GOBE? Salam! Samirah tace cikin daga murya tana tafiya tana wani budewa babu wanda ta kalla direct ta wuce gun maigidan hannunta dauke da zungureriyar farar takarda,ya dan bar abinda yake kana ya dubeta yana masawa,ta qaraso inda yake ta zauna hannun damansa yayin da salima ke hannun hagunsa takardar ta miqa masa ya amsa kafin ya duba yace" kada ki sake min irin wannan sallamar da kikamun yanzu don ba sallama bace take note,ok?"ta gyada kai tana buntsuro baki,ya bude takardar yana dubawa,ya qare dubawar sannan ya dago kai yana kallon fuskar samiran idanunsa da alamun neman qarin bayani,ta dan yatsine fuska sannan tace"eh abu uwan amfani ne da suka qare nake da buqatarsu" ya dan gayara zamansa ya jingina da makarin kujerar ya sanya idanunsa sosai cikin nata,sai ta kasa kallonsa ta dan soma rikicewa tana son janye idonta ta kasa tasan shi tamkar maye yake wajen naqaltar mutum tasan yanzun nan ba qaramin aikinsa bane ya harbo jirginta,da zarar aliyyu yayi ma irin wannan kallon yake gamawa da kai,sai da yayi shiru na muntina sannan yace"ina zaton yau ko sati biyu ba'ayi ba na karbi list na dukkan abunda baku da shi na kawo.....ya akqi naki ya riga na kowa qarewa bayan ko sati biyun ma ba'a cika ba?" Ganin tayi shiru ta kasa bashi amsa yasa ya maida kallinsa ga salima wadda tayi kasaqe tana sauraronsu zuciyarya cike da farinciki tana mai addu'ar Allah yasa a ci mata mutunci"nawa ne kudin naki ankon"tawani yi fari da ido sannan tace atamfa dubu arba'in ne lace dubu sittin aai gudun mawar da zan bata dubu dari"(kunji tsabar rashin hankali irin na wasu matan mutumin da duk qarshen wata yake fita da su suyi siyayyarsu idan akwai abinda sai anshiga kasuwa ake samu zai sa su su rubuta ya bayar a akawo musu haka nan kayan abinci da na ciye ciye zaisa a sabunta miki koda basu qare ba kuwa ruwanki ne kisan yadda zakiyi da su shi dai duk qarshen wata zai miki haka,hakanan zai kawo kudi masu kauri ya baki bayan wanda kullum zai baki koda ba ranar girkinki bace )baiji komai ba kasancewarsa mai hannun kyauta ne koda ba ga iyalinsa ba,amma ya lura barnar ta soma yawa don haka ya sake waiwayawa ga samira yace"uhm....am waiting for d answer Ta yatsina fuska tace" kasan ni maca ce mai jama'a 'yar dangi kuma duka dangina anan garin suke ba baquwar haure ka auro ba wannan ya shiga ne wannan ya fita"salima tasan da ita take kasancewar iyayenta da danginta ba a garin suke ba a hannun qanwar mamanta take anan kanon amma ba yan garin bane,cikin hasala tace "da uban wa kike?"kamar dama jira samiran kuwa take tace da ubanki nake ,kinji na kasa da ke ne bare ki dauka banza kawai mtswee!"ai kuwa salima tayo kukan kura tayi kan samira da niyyar shaqota dama da qullin samiran a ranta Wata gigitacciyar tsawa ali ya daka musu wadda hatta fadila dake gefe sai da ta miqe tsaye saboda razana bare su salima da suka koma sukayi zamqn dirshan ba tare da sun shirya ba,ran 'yan maza ya baci fa zuciyarsa ta tabu take idanunsa suka kada Cikin tsananin bacin rai ya kallesu "wadanne irin mahaukata ne da baku da burin da ya wuce kuyi kokawa?"salima da ta shaqa da yawa ta nuna kanta tana cewa aliyyu nice mahaukaciya?" Ya dora da cewa "kun wuce hakanne?ba i sauraresu ba ya murza yatsunsa suka ce das das das ya nuna su sannan yace dis is d last worning kunyi na farko kuma kunyi na qarshe dambe a agabana..... bazan dauka ba don ni ba shasha sha bane" salima da idonta ya ciko da qwalla tace"amma fa kana gani fa tana shigowa ta hau habaici daga qarshe ta hau zagina.....samirah ta tari numfashinta da cewa"tambaya kimayi na baki amsa daidai da tambayarki" shut up!" Ya sake dakawa samira tsawa ya nuna mata qofa sannan yace da ita get out of my room,jiki a salube ta juya zata fita ya ce hey ta juyo ya nuna mata paper dinta take your rubbish neman tashin hankalinki ya siya miki ya bita da "stupid" wani takaici ya sake turnuqeta ai kuwa buguzum buguzum ta qarashe ficewa Ya dawo da idonsa kan salima yace"ni bani da kunne sanda tayi zagin ba zaki bari kiga hukuncin da zan dauka ba sai ke sarkin iya hukunci?,sai kuma alokacin ta soma shagwabe masa da sunan bashi haquri ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu" dont disturb me please leave me alone"ta san bacin ran aliyu bashi da dadi do haka ta ja qafafunta ta fice cikin takaicin asarar da sira ta jawo mata na kudaden da take son karba a gunsa,yaja tsaki mai qarfi cikin ransa yace"silly girl" ya juya a hanzarce ya shige bedroom dinsa Ransa ya baci sosai mutum ne da baison hayaniya yanzu haka qirjinsa zafi yake haka yake ko hira yayi mai tsaqo yanzu kansa zai fara ciwo shi yasa ko musu bai iya ba,ba ruwanshi da shiga wata harqalla ko abokai bai fiya tarawa ba baifi ka qirge abokansa ba da hannu,to da shi da fadilan bansan wanda yafi wani ba Mrs muhammad dinku ce [10/16, 12:39 PM] Salma *wa yasan gobe?* Writting by safiyya Abdullahi musa huguma Kai tsaye bedroom dinsa ya nufa ya canza kayansa zuwa na barci farare ne sol masu taushi mutum ne shi ma'abocin son fararen kayan amfani ya fada bisa gadon yayi rigingine qafafunsa na qasan gadon ranshi a cunkushe yake