Sashe 34
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mutunta mutum Hira suke gaman da zamantakewar aure irin hirarmi dai mata da aka sani wadda matuqar mayan aure suka wuce biyu aka hadu sai an yita,hira ce ta qaruwa ba banzar hira ba wadda bata kamata ba,duk da haka fadila na gefe don bata da abun fadan saidai jifa jifa takan ce wani abu Hira tayi nisa fa'iza ke basu labarin wata maqociyar yayarta 'yaf nijar dake saida magungunan mata masu kyau na gargajiya wadanda basu cutarwa,dukkansu suka ce ayi kiran matar suna so fadila kawai ta rage,fa'iza ta kalleta"ke ba ki siya fadila wlh maau kyau ne"murmushi tayi tana neman qaryar da zata gilla musu,don ko ta siya me zata yi da su,ta kalli fa'iza "to a hado da ni ga nawa kudin"ta nude zif din jakarta ta fito da kudin,fa'izan ta kuma cewa idan ma bakiso akwai wani hadin tutare mai tada sha'awar mai gida sai a kawo miki shi"cikin basarwa fadila tace"a hadomin duka kawai"(kaji fa mai karatu kamar gasken tana da buqatarsun Take fa'iza ta kirata ta sanar mata,ta kaahe wayar tana dubansu tace kun taki sa'a don gata nan ma anan kusa don tana ja'en,cikin minti talatin sai gata kowacce ta karbi nata ta sanya ajaka Qarfe biyar ta soma hada kayayyakinta tana sallama da su zata wuce gida don ta kammala aikinta ,wayarta dake aljihun bayan jakarta ta dauki qara alamun ana nemanta *sister ta* ta gani bisa screen din hakan na nufin farida ke kiranta,da sauri ta daga hadi da yin sallama,"sister ki taho kiga baby girl mai kama da ke kamar copy naki akayi na haihu yanzu haka ina gida"wani tsalle fadila tayi hadi da qaramin ihun farinciki sam ta mance a office take ba a gida ba sai da taga su fauziyya sun taso suna tambayarta mai ya faru sannan ta tuna ta maida wayar tana dariya cikin doki tace junior sister na ce ta haihu wlh"suka mata barka hade da dariya suna cewa saura ke kenan,murmushi kawai ta musu ta saba jakarta tana cewa"Allah ya bamu alkhairi"ta kama kumatun yarinyar fauziyya tana mata wasa har ta fice yarinyar nata kuwa bangala mata dariya don fadila akwai son yara yarinyar ta soma sabo da ita yauma sa'a akaci bata sa kuka ba da zata tafin Da dokinta ta shiga motarta da niyyar wucewa gidan farida kai tsaye,har ta kunna motar ta tuna cewa sai fa ta sanar da aliyyu,take murnarta ta ragu tamkar an zare mata laka ta kashe motar,ta jawo hand bag dinya dake kusa da ita ta ciro wayarta ta bude sannan soma searching number'n sa cikin contact dinta wadda yayi mata serving da kansa ranar da bata da lafiya,tayi attempting din kiransa yafi sau goma ta kasa,sai ta fara dialing sai ta katse da kanta,bata san answer da kuma result da zata samu ba Daga qarshe taga hakan bazaiyi mata amfani ba sai kawai tayi shahada ta kira din,yadda wayar ke qara yin din din haka zuciyarta ke bugu,idanunta a rufe gam tana jiran wayar.... Mrs muhammad dinku ce *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *PART 2* "Assalamu alaikum" dakakkiyar muryarsa ta doki dodon kunnen fadila,numfashinta ya dan dakata na wucin gadi,komai da ya danganci aliyyi jinsa yake har cikin jininta da bargo komai qanqantarsa kuwa,"hello waye ne?" Ya sake maimaitawa, "idan mai kira baida abun fada zanyi rejecting I have a lot to do"dadi muryar tasa ke mata har can qasan zuciyarta,zata so ta dawwama tana sauraren muryar idan da halin hakan,din din din da taji sau uku shi ya tabbatar mata ya katse wayar kamar yadda ya fada tun farko,ta saki wani dan murmushi da ya tsaya a kuncinta tana kallon fuskar wayar tata,tazarar minti biyar ta bayar sannan ta redial din number tasa Tana daf da tsinkewa ya daga wannan karon ita ta fara yin sallamar ,yayi dan dum sannan ya masa a daqile sanan ya dora da "who's on d line?"cikin in ina ta soma magana don gaba daya dakiyarsa ta rudata "nice" "kewa"ya maida mata da tambaya,"fad...fadila"ya sake shiru na yan sakanni har tana tsammanin ko baya kan layi ta duba wayar sai ta ga yana nan "What's going on?"ya sake tambaya,wani abu ya dan taba ranta da gaske bai ganeta ba har sai da yayi analysing a qwaqwalwarsa,"sister farida ce ta haihu" "uhm labari kike ban kenan?"ya fadi cikin watsar da muhimmancin batun a gunta,tambayar ta quleta hakan yasa tayi shiru,"me kike buqata ne ina fa da aikin yi"ta daure tace "baby nake son inje na gani" "ban amince ba"ya fadi kansa tsaye,din din ya katse wayar,wani hawayen takaici ne ya sulmiyo mata,tayi wurgi da wayar kujerar gefenta,cikin takaici ta figi motar sai gida Danja na tsaida su tana ganin wani wani saurayi dake gefan tata motar yadda ya zuba mata ido da alama yana mamakin me ya sanyata kuka ne,ta kawar da kanta gefe cikin zuciyarta tana ayyana in banda babu kyau fita babu izini tabbas da sai tayi wucewarta gidan farida saidai aliyyu yayi tsirenta,ta share hawayen sanda danja ta sake su ta sake figar motar,tana kallon yadda saurayin ke sa mata signa yana son tsaidata tayi banza da shi ta qarawa motarta speed,ita kanta bata san tayi gudu haka ba sai da ta iso gida agogon wayarta ya harba taga yan taqitattun mintocin da suka kawo ta gida,tana qoqarin shiga gidanne bayan mai jire bakin qaton get din gidan ya dage mata qofa ta soma shiga taji wani horn din,ta glass ta hangota motar samira ce wadda take cin ubanta da hawa ta tabbatar da motar mutum ce da tuni ta dade da guduwa,ba samiran ba hatta qawayenta sai suzo su ari motar su wuni sur suna cin ubanta ko a daddoke mata ita su kuma dawo su yasar mata ita ce mai kudin banza ta gyaro ta zuba musu mai gobe su dawo su sake ara ita kuma ba lissafi ta basu saboda tsabar neman suna irin na samira,shi uasa tayi nacin aliyyu ya canza mata mota qememe yayi buris da ita don yana sane da abinda takewa tatan Mrs muhammad ce 12:36 pm 22/8/2016 *WA YASAN GOBE?..* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *PART 2* 9 Ta ajjiye motar a parking space ta kashe ta tana mai dauke idanunta daga kansu samira zuciyarta na tur da irin halayen mutanen da samiran ke mu'amala da su,hakanan ko yaushe zaka gansu cikin shiga ta banza da rashin da'a,yanzun ma qawayenta ne su uki ta dauko cikin motar kowacce kuma cikin shigar tasu dai ta dabi'ar da suka dorama kansu ,tana jin shewarsu sanda take rufe motarta kasancewar suna bayanta ne tsaye jikin motar samiran su basu shige ba hakanan basu komacikin cikin motar ba,sun saba yi mata haka tun ba yau ba kula su ne sam bata taba yi ba don bata kallonsu ma a matsayin cikakkun masu hankali,tana ganin idan ya kula su ma tamakar ta basu wata martaba da daraja ne,kallon tsiya ma basu isheta ba bare su sa ran wataran zasu samu na arziqi bare fadilan dama miskilar kanta ce sai ka gama cin kashinka a gabanta idan bata ga dama ba quda bazata kore maka ba Kamar ko yaushe yauma har ta bawa banza ajiyarsu tayi gaba abinta maganar da ta jiyo suna fada ita ta sanyata dawowa da baya ta tabbatar ya zama dole yau ta yiwa tufkar hanci bare yadda take cikin takaicin hanata zuwa gidan farida da aliyyu yayi shewa suka yi sanda take yin gaban sannan daya daga cikinsu tace"badi'a (sunan daya daga cikinsu ta kama)saiki dinga fakewa da fita aiki ana yawo a kwararo Da baya ta dawo sannan ta fuskancesu,dubansu tayi daya bayan daya up to down ta saki wata 'yar siririyar dariya tace " ai karuwanci iyawa ne kuma karba karba ce, wata hajar sai ta qaraci zamanta a kasuwa tasha qura tayi futu futu kullum kuma sai an fito da ita an kasa amma sai kiga ko kallonta al'umma basuyi bare su baqaci siya,kinga kenan inda wani yayi rawa aka bashi kudi wani idan yaje yayi dan banzan duka zaici Ta sake watsa musu kallon raini sannan ta dora"ku ba abokan yina bane don ban hada sabga da ku ba wannan.....ta nuna samira da key din mota dake hannunta "itace abokiyar yina,ita din ma zata gaya muku inuwarta bata isheni kallo ba bare zahirinta,but.... well zan baku shawara guda daya hade da gargadi mai kama da jan kunne,shawara ta farko itace ku rufawa kanku asiri ku samu ku raba jikinku a dakin aure kafin a rasa mai kwasar ragowarku...... au am sorry na manta yanzun ma fa hakance ta faru da ku fa shi yasa kuke gararamba da yawon kwadayi da maula agidajen matan wasu And gargadina shine kada wadda ta sake bude rubabban bakinta da niyyar shiga gonata don nikam duk cikinku babu wadda tayi isar da zan shiga gonarta,saboda haka nima akiyaye shiga tawa gonar "ta kama kunnenta daya da hannunta tace"idan kunne yaji......gangar jiki ta tsira"ta saki hannunta ta juya da niyyar shigewa dukkansu sunyi mutuwar tsaye don nasu taba tsammanin ta iya magana haka ba a yadda samira ke basu labarinta,samiran ce tayi yunqurin nuna jarumtarsu tasha gabanta ta kama qugu tana cewa"ke qaramar 'yar iska mu kike nufin zakiyi wa rashin mutumci?" Murmushi fadila tayi tace" a'ah sanin kanki ne fa ni ban iya hayagaga ba ke zaki fara baiwa wanda bai sani ba labari ,to kuwa akan wadancan shashashan bazan fara ba"ta gewayeta tayi wucewarta,tana jiyosu suna ci gaba da kuri da cika baki kala kala akanta har suka wuce sashen samira,cikin ranta take fadi Allah ya bawa daya daga cikinsu sa'a tace zata biyota taga yadda ake rashin albarka Wanka tayi don taji sanyin zuciyarta tuni ta watsar da batun su samira don basu gabanta hasalima bata daukesu wani abu ba don tasan baya ga tsabar jahilci dake damunsu rashin tarbiyya na bibiyar rayuwarsu,tana mamakin tsarin rayiwa irin tasu sam basu damuwa da yanayin da rayuwarsu ke gudana,falo ta dawo ta hada yoghurt mai sanyi da fura ta dama ta koma saman kujera tana diba da cokali a hankali tana sha zuciyarta sam bata gidan,kira ne na anty hafiza ya soma shigowa wayarta tana neman farida ne tayi ta kiran wayarta busy shine ta kira ko suna tare ta