← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 84

Sashe 71

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

curry kawai yake zubawa,kana Kallon abincin kai kasan ba Salima ce tayishi ba don ba zata iya din ba Amma maimakon ya burge ta sai ma tashin Zuciya da haifar mata,don ita yanzu a duniya babu abinda yake burgeta take biya ci irin ayaba ,komai dadi ko haduwar abinci,saidai ko lemon zobo,koda ta kwata cin ma amai ne ke biyo baka Ta rufe da sauri tana mata godiya,maimakon taga salimar ta tafi sai taga tana gyara zama harda qoqarin zuba mata "Gara kici tun da duminsa,nasan h lin masu ciki yanzu yana kaiwa anjima zai iya fita daga ranki",da sauri fadilan ta dakatar da ita"kada ki zubamin yanzu don banajin yunwa" Sororo saliman tayi cikin rashin jin dadi har hakan ya bayyana akan fuskarta,tilas ta haqura ta rufe ba don ta so hakan ba,saidai don bata so ta fiya matsantawa har fadilan ta dago wani abu, Haka ta fice tana jaddadawa mata taci fa,sanda wai sai tana ci tana qoshi,hakanan fadila taji ko bayarwa bata so tayi,saboda haka ta samu baqar leda ta kwafe a ciki ta cilla cikin dustbin kwana daya biyu salima taji shiru,ba qaramin tashi hankalinta yayi ba,Duk wani shishshigewa da kulawa tayi wa Fadila shi,duk cikin qoqarinta na ganin ta samu yarda gurinta,babu abinda bata dafa ba na kwadayi ta kai mata ba,sai dai kash....abinda bata sani ba babu abinda cikin fadilan ya sani banda ayaba Dukkansu sun shirya don zuwa gida Momi karbar lefen sumayya da rabi'ah Wanda za'a kawo ranar,mai gidan ne da kanshi zaya kaisu cikin motarshi sabuwa dal da duka dauka shekaran jiya ta iso,yayi haka ne a fakaice don fadila wadda ke sanye cikin doguwar riga ta atamfa exclusive mai adon orange da army green, Duk da turtsetsen cikinta hakan bai hanata yin adonta ba,Kuma tayi kyau abinta,ta fita daban a cikinsu tamkar zahra cikin taurari,hakan ne ya sanya aliyyu ya kasa yiwa idonsa shamaki daga kanta,Duk inda ta motsa idanunsa na biye da ita Baisan me yake s urin daya fushi ba,kwanakin gaba daya a fusace take,Abu dan qanqani sai ta hau masifa ko tasa kuka,har doctor ya tambaya tace masa kada ya Samu wa su mata idan su na da ciki hakan na faruwa da su,musamman idan yaw soma tsufa suka fara gajiya da shi,to ko a yanzu ma ya lura kamar 'yan rigim r na kusa,don ko su Samira da bata kulawa a irin wannan mood din tana jin dai dai take da duk wadda ta tabata a cikinsu Ya sake kallonta,tayi lullubi har saman kanta da farin mayafi da ya dace da atamfarta,ba kamar lullubin 'yan uwanta ba ita kafada,sai ta sake masa kwarjini,cikin ya mata kyau duk da dan uban girmansa Wanda ke sake sashi jin tausayinta tare da sake mata addu'ar sauka lfy hannunta harde saman cikinta,tayi kicin kicin da fuska,hada ido sukayi ,ta same qwayar idonta ta wani dauke kanta tamkar bata ganshi ba,dan qaramin murmushin nan nasa ya saki,wani lk n salon shan qamshinta da miskilancin nan nata na burgeshi,ta iya shariya da dake kai da gangan Ya dubi salima wadda ita ke d girki,ba yadda ya iya a zahiri zaifi son ace Fadilar ce kuwa da shi,ya danna madanni ya bude gidan gaban da a dazu yake a rufe yace da Saliman"shigo nan" sai ta tsinci kanta da ji wani bacin rai,suka Kuma hada ido,batasan sanda ta danna masa harara ba gami d Jan dan qaramin tsaki a ciki,ta shige sit din can baya na qarshe tana kumburi *Mr s Muhammad ce* [12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed *WA YASAN GOBE?..........* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 3* 2 Jinta take kamar ta fashe,ita kanta tana mamakin yadda yake saurin fusata a yanzu,Duk da ta sani akwai tsananin kishin aliyyu dake dawainiya da ita,tabbas ba kuwa ce maca ce ce zata San Wayne ainihin aliyyun ba ta kada kishinsa,musamman ma ita da kunsan tafi kuwa saninsa zahiri da badininsa Salima nata rawar kai ta shige gaban,Aliyyu ya tada Motar yana qoqarin gyara madubin motar ta yadda zai samu sukunin gano fuskarta sai dai sam taqi yarda da hakan don tuni ta kautar da fuskarta,dole ya haqura ya soma tuqin hankalinda na rabe gida biyu Duk yadda salima yaso ta janye hankalinsa suyi hira mai tsawo da dadi ko don ta cusa musu haushi abun ya faskara,dole daga qarshe itama ta haqura ta ja bakinta tayi shiru Ko da suka shi go harabar gidan tamkar dama Allah Allah take su iso tuni ta rigasu ficewa tamkar bata jin nauyin jikinta,ya biya da ido don ba haka yaso ba Yaso ne ya datseta a cikin Motar ya mannata da jikinsa ya dan rage mata temper,don a matakin da take ciki tana buq tar wannan,salima dake lure da shi takaici ya cikata,ta sake qullatar Fadila,ta Kuma sake lasar takobin hana abun dake cikinta tayuwa kota halin qaqa Ya dauke idanunsa lokacin da ta bace wa g ninsa,bai bai ta kan yadda suke k llonsa kamar zasu cinyeshi danye ba ya jaw wayarsa dake gefensa ya latsa number din Anty hauwa ya kira,bugu uku ta daga "Hello mummyn kausar,ga ajiyata nan as usual, pls abata kulawa ta musamman Anty na"dariya ta saka "Ho,aliyyyuuuu.......to naji,mene tukuicina?" "IPhone 7 da kike son siya ki bar kudinki ni Zan Waya miki"ta sake dariya"lallai Ashe abun na yine,to ba Matsala,kada ka damu dan qanina" "Thanks Anty",ya fadi yana kashe wayar "Amma fisabilillahi tuni yaushe bace maka ina son iPhone 7 din na ,kowa cikin qawayena ita suke riqewa ammavkaqi siya mini,sai ganshi rana tsaka kace zata siyawa Waya",Kallon da yayi mata ya sanyata yin da in yin furucin,tuni kafin yace wani Abu ta balle murfin Motar ta fice tana qunquni cikin ranta Wanda ta bata isa ta yishi a fili ba,don ba qaramin wuya ta ci ba lokaci da ya amshe mata key din mota da wayarta bakamin ya dawo mat da su Ya maida idonsa kan salima,tayi qoqarin hadiye bacin ranta don son cimma qudirinta kan fadila cikin ruwan sanyi ba tare da an gano komai ba,ta bude motar itama ta fice ranta na mata wata iriyar suya,tanajin zata iya koda kawar da fadilah ne don ta shigar mata hanci da qudundune da yawa,tasa ta rasa fili da gurbin da ada take jin tana da shi a zu Cikin falon ma kowa sannu yake mata,ciki wata bakwai amma sai ka dauka da ka bar gun za'a bika ace ta haihu,haushi,takaici,kishi,qyashi da hassada ta cika zuciyoyinsu,Samira da bata iya shiru ba tace"mu sai a tsine mana albarka ai tunda bamu iya daukan ciki ba"ciki ciki tayi maganar amma wani abun ya dan fito,madina tayi yunqurin magana Momi tayi mata inkiya da tayi shiru kada tabi ta kanta,sama dakinsu sumayya ta haye abinta tayi kwanciyarta Anty hauwa ta cika mata plate da ayaba ta bawa bilkisu ta miqa mata,Momi kuwa tayi ruwa tayi tsaki hawa,hana kuwa hawa,fada ma ta dinga don me yasa b 'a barta ta zauna a gida ba tana fama da kanta haka,batasan ita ta rage lallai sai ta so ba Baccin kuwa take sonyi,don matuqar ba ranar girkinta bace bata ita wani baccin arziqi,ta riga ta saba bacci jikinsa,yana l llabata kamar qwai harda tausa yake Gara mata,baya runtsawa har sai ta rigashi yin baccin Kira ya shi go way rta tana kwance lamp da tsammanin zuwan bacci,ta duba sai taga sunan *darling blood* sunan da ta sama number dinsa kenan,sosai take da muradin jin muryarsa sai dai tana sane tayi banza da wayarta,sau biyu tana rurinta tana katsewa sai a Kira na uku ta sdaga,ta kara a kunnenta ba tare da tace koma ba,ajiyar zu iya ya soma saki wadda ta ratsa Fadila har ta tayar mata da tsigar jiki "Babyyyy..."ya kirata Murya qasa qasa cikin Jan sunan,itama ajiyar zuciyar ta soma saki"I missed you badly"abinda ta iya fadi kenan cikin narkakkiyar murya,ya sani sarai akwai kewarsa dake damunta,kwana hudu ba tare da ju su ba abune ba mai s uqi qwarai da g ske,sai tausayint da sonta ya sake kamashi,iya kawaici tana da shi,gashi nan da kwana biyu zasu wuce umara shi da salima da Samira harda doctor sa'adah wadda ya mata alqawari "I know baby na,saidai hankalina na tashi idan na ganki cikin rashin walwala,please smile my dearest wife,ko da bana kuwa nasan z nji a jikina" Bata San lkcn da murmushin ya subuce mata din ba,musayar kalaman soyayya suka dinga yi masu tsuma zukatan ma'aurata,aliyyu yaqi barinta har sai da yaji shiru alamun baccin ya dauketa *Mrs Muhammad ce [12/16/2016, 10:12 PM] Ameenah Abdulmajeed *WA YASAN GOBE?........* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *part 3*
Chapter 71 · 0% Book details