Sashe 26
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fadila da ke tsaye sai yanzu ta motsa ta saki ajiyar zuciya gami da fadin Allah ya kyauta ya iya mana abinda ba zamu iya da shi ba,ta isa inda suka baje kolin abincinsu suka ci suka tashi bar kwanukan ta tattare su ta gyara gun kamar ba'a yi hada hadar abinci ba agun Ta isa kitchen ta zubasu cikin sink ta kunna gas ta hada ruwan bununsa wanda ya wadatu da citta kanunfari da lemon grace ta saka lipton daya sannan ta rufe tukunyar,ta koma ta saki fanfo ta wanke duka kwanukan ta adanasu sannan ta juye mishi tea din cikin wani dan qaramin flask mai kyau ta dauki cups guda biyu na tangaran ta dora a saman plate ta hada masa da spoon,ta rufe qofan kitchen din ta doshi bedroom din nasa Ta tura qofar tana dar dar don tana tsoron kada ya maimaita mat abinda ya mata dazun,ya canza kwanciyar tasa zuwa barin hannun damansa yayin da ya juyawa qofar shigowa baya,qafarshi da yake dan kadawa kadan kadan shi yasa ta fahimci idanunsa biyu a hankali ta ajjiye tire din a asaman bedside sannan ta koma saman kujerar madubi ta zauna tana fuskantar bayan nasa,dakin ya yi tsit kamar ba wata halitta a dakin sai qarar agogon bango dake maqale a abangom dakin yana ta aikinsa,ita batace komai ba bareshi da tasan dama ba maganar zaiyi ba Zuwan can ta dan ja numfashi sannan ta tattaro dukka dauriyar da ta rage mata bayan ta gama wassafa da tsara maganar da zata fito a bakinsa,tayi yar gajeriyar gyaran murya a dan tsorace sanann tace" nazo ne baka haquri game da bata maka rai da mukayi dukkaninmu mu ukun,zan ari bakin yan uwana na ci musu albasa ince kayi haquri da mu baki daya,idan ban manta ba haka Abba ya gaya maka a ranar da mukaje masa _lamarin mata sai da haquri da kuma jajircewa halitta ce maau wuyar sha'ani amma idan kasa Allah a gaba sai komai ya zo maka da sauqi_"kayi haquri da mu Allah kuma ya huci zuciyarka ,ga black tea nan ko kana da buqata sai da safe Ta miqe tana barin dakin ya dan waiwayo yana dan kallon ta har ta fice,yana cike ne da mamakinta dama tana da saurin sauka a fishi ne?,at least ya samu relief ainun daga damuwarsa,hakan ne ya bashi dama har ya jawo flask din ya murda murfinsa ya bude qamshinsa ya taso ya mamaye hancinsa ya dan lumshe idonsa take kwadayin tea din ya kama shi,yasa kofi ya tsiyaya ya sanya zumarshi ya kurba qamshin cittan da kanunfarin da lemin grace suka hadu a abakinsa suka masa dadi Tana idar da sallar asuba bayan kammala al'adarta ta kullum wato azkar na sabahi wal masa wanda annabi ya koyar ta koma ta jingina da gefan gadonta idanunta a lumshe ta soma tilawa kamar yadda ta saba cikin sassanyar muryarta,sai da tai izifi biyar sannan tayi addua ta shafa,ta linke sallayarta sannan ta soma gayara bangaran nata duk da ba datti ko kadan sai 'yar qura da ba'a rasa ba wadda hadarin da ake tayi kwana biyu idan ya hado sai kuma ya zama iska mai sanyi wadda ke tashi hade da yar qura,tana kammalawa tayi wanka sannan ta shirya cikin doguwar rigar yan kanti mai roba roba red ce ta sauko mata har qasa ,daga gaban rigar wajen qirji an kamata an mata tattara yayin da ta bude sosai daga qasan aka jera wasu irin dutsuna manya guda uku masu garai garai da qyalli hannun vest ne da ita saboda haka ta sanya long sleeve shirt fara ,tayi rolling da farin mayafi wanda acucin da tayi da gashinta ta mai doughnut ya taimaka wajan qarawa rolling din nata kyau iya kafadunta mayafin ya tsaya,qananun fashion na barima farare ta saka sannan ta jawo takalminta slippers na fata shima fari ne,wayarta ta dauka ta kulle bangaran nata Yauma da keys dinta tayi amfani ta bude gurin,shiru yake ba motsin komai hakan yasa tayi tsammanin bacci yake,hakanne kuwa ta gani sanda ta leqa bedroom din nasa cikin sanda,yana kwance tsakiyar gadon duqunqune cikin farin lallausan bargo ,gefansa daga qasa dardumarsa ce qur'ani da kuma carbi akai,yayi mata kyau sosai aliyyi gwanin kyau kome yakeyi kyansa fita yake,baccinsa yake verry calmness fuskarsa tayi fresh,sai ta lumshe ido tana tuna da yadda daren jiya tayi nata baccin cike da kewa da azaba,amma shi yanzu gashi yana nasa hankalinsa a kwance har da qarin wani na bayan sallar asuba kenan,ta dauko wayarta ta kashe plasher dinta tayi snapshot din fuskarsa,ai kuwa ta fito shar zara zaran gashin idanunsa sun kwanta luf,tayi kissing din hoton sannan ta juya ta yi kitchen *mrs muhammad ce* *wa yasan gobe?* Chips ta soya hade da wainar qwai sannan ta dama masa kunun gyada da ya sha madara yayi fari qal sai zuba qamashi yake,sannan ta bare indomie ta yi masa awarar indomie,nan fa qamshin abincin ya karade gaba daya falon har cikin gidan to wani ma yayi rawa bare dan makadi,fadila gwanar girki ce mayyar kitchen ce tun tana gida ma,tana saitin window inda kan famfo yake tana wanke kayan da ta bata ta ke jiyo motsi kadan kadan,windon na cikin lambun bangarenshi da ke bayan part din kowa,tana daga kai ta hangoshi qarfe yake dagawa ya hada gumi sosai,armless riga ce a jikinsa da shortnekeer damtsensa cike da qwanji a murde,ya ajjiye qarfen ya dau dan farin towel dake gefansa yana sharce gumin kana ya dauki bottle na ruwa ya daddaka ya rufe ya koma kan keken training kuma Ta saki murmushi ta kada kai,da azama ta hada komai ta koma bedroom ta gyara masa ta wanke toilet ta hada masa ruwan wanka,ta budade ko ina da qamshin nan nata sannan ta dawo parlour ta zare rolling din kanta ta fara gyare falon shima ,yana daga can yake jiyo qamshi kala kala na shiga hancinsa da fari qamshin girki ya fara jiyowa ya bude dogon hancinsa yana shaqar sa saboda ya masa dadi daga bisanai kuma ya jiyo wani qamshin qamshin da ya kwana jiya yana sheqa,ya sauka daga kan keken shima ya dauki wayarsa da towel dinsa ya bude qofar bayan ya shigo ta cikin kitchen wanda yasa sauran kadan suyi karo,ta ja baya da sauri tana gaidashi kanta na duqe a qasa kamar kullum bai amsa mata ba dama ta zaci hakan ya dai daga mata hannu ya wuce A bandaki ya tarar da ruwan wankan nasa,ya dan yi dam domin bai saba ganin hakan ba a tarihin rayuwar aurensa ba ganin tunanin zai bata masa lokaci yasa kai tsaye ya shige cikin ruwan yana sheqar qamshin da yake Cikim suit ya fito baqaqe masu sheqi sunyi masifar fito da ainihin kyawunsa,takalmi ne half cover dan hasken marun kamar yadda tie dinsa yake marun da jakarsa a hannu fuskarsa saye da fari qal din medicated glass dinsa wanda bai hanawa mutum ganin kyakkyawan qwayar idanunsa,sumarsa a kwance luf baqa sidik sai sheqi take ita ba mai yawa ba kuma ba a aske ba qamshin nan nasa na musamman ke fita a jikinsa,ya dan zauna a hannun kujera yana qarasa taje sumarsa da brush dake hannunsa Afuwa afuwa Nayi rubutu mai yawa zan turo muku na ajjiye wayar ina dan wani uziri kafin na dawo ya goge,chargy kuma ya riga yayi halinsa,kuyi haquri da wannan ku bini bashi da yardar Allah Na gode Mrs muhammad ce [10/16, 12:40 PM] Salma *wa yasan gobe?.....* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* Ganin wannan dama ya sanya fadila tayi saurin sauko da kayan breakfast din gabansa duk da cike take da fargabar kada ya gwasaleta,tayi saurin hada masa tea ta daidaita masa zafinsa ta ajjiye masa sannan ta sa masa wainar qwai da farfesun kayan ciki ,taji dadi da baice komai ba ya sauko ya karya,bayan ya kammala ya dauki jakar laptop dinsa ya ciro yan dubu dubu guda uku ya ajjiye mata kamar yadda yake ajjiye wa sauran matan ranar nasu girkin duk da kuwa babu abinda zasu siya komai diba za suyi yana ajjiye,ya yi gaba ta biyoshi a abaya gabanta na dukan uku uku bangaren samira ta ga ya shiga don haka ta ja tunga ta tsaya baifi mintina biyar ba ya fito ya shiga gun salima mintina takwas sai gasu sun fito yana gaba tana biye da shi ganin fadila na tsaye da alamum jiran fitowarsa take sai yanayin fuskarta ya sauya take ta juya ta koma ciki Har sai da ya shiga mota ya zauna sannan tace a dawo lafiya tayi saurin juyawa ba tare da ta jira cewarsa ba don tasan bazai ce din ba ma idan ma ua fadan to ba mai dadi zata ji ba,tana hango salima da ta yaye labulen falonta tana kallonsu don haka sai fadila ta qorqiro murmushi ta dora bisa fuskarta Ta rasa hali irin na salimar mutum ce mai tsananin qyashi da hassada ga azabar sa 'ido komai idanunta na kai kamar wadda aka bata aikin yin hakan ita dai samira barta da kishi masifa da tsokalar rigima kuma kana tabata za kuyi uwar watsi agun shikenan duk da haka kishin salima har yafi na samira ita kawai tanada duniyanci da yasa take iya boyeshi ba kamar samira da ba ruwanta ko a gaban uwar waye ayita ta watse ba munafunta Haka fadila taci gaba da tsara rayuwarta duk ranar da take da girki zata shiga bangaren ta gyara ko ina da ina,tana kuwa fama da aikin domin tsakanin samira ko salima babu mai iya yin cangal kowacce haka take fita daga girkin ta tabar sashen a ahautsine Tsakaninta da aliyyu sai girki ta shirya masa daddadan abinci ta zuba masa ya ci idan ya kammala ta kwashe ta wanke kana ta ja qafarta ta bar sashen sai kuma washegari idan ta shigo hada masa breakfast,da zarar kuwa kwanakinta ya qare bata bi ta kan kowa da zarar ta taso a aiki ta shiga sashenta ta qulle qofa tofa sai washegari zata sake fitowa Wai inji hausawa sunce jiki da jini kuma mutum da zuciya cikin lokacin sai sai qyamar girkin su samira ya fara kama aliyyun ransa ya soma sosuwa da ganin sam gyara bai damesu ba,har gwara ma.salima tunda at least akwaita da son