Sashe 35
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bawa faridan,nan da nan ta tabo mata miki basu gama sallama ba ta kashe wayar don bata son taji kukan da ya qwace mata,kamar kuwa hadin baki yan uwa ke kiranta suna cewa ita zasu yiwa barka itace uwar 'ya,hakan ya raunana zuciyarta sosai tasha kuka,sister faridanta guda amma wai a hanata ganin 'yarsu? Har magariba jikinta amace yake,sai sannan ta tuna bata kira umminta ta mata barka ba,jin muryar ummin bayan ta daga sai ya karyar mata da zuciya kuka ta saki,a tsorace ummin tace "meye haka lafiyarki kuwa?"cikin kukan tace "ummi ya hanani zuwa ya hana ni inje inga baby ummi"ummin ta saki ajiyar zuciya sannan ta ja tsaki"wlh harkin tayarmin da hankali na zaci wani abune ya faru ko ya sameki?" Ta sake marairaicewa cikin muryar kuka tace "ummi wani abune mana sister farida fa ummi" "to sai me idan baki je din ba?,idan kinje ma me zakiyi mata iyakaci kije kuyi ta surutu,tunda Allah yasa an sauka lpy bashi kenan ba abunda dama ake buqata kenan"ta sake sakin kuka tace "ummi ki masa magana don Allah idan ba haka ba baza ni ba"kama haba ummin tayi kamar fadilan na gabanta tace" lallai bansan haryau quruciya na damunki ba fadila,to ba da ni ba wannan shiriritar,bana som sakarci ki maida hankalinki fadila kada na soma jin wani abu kuna jina ko?" A sanyaye ta gyada kai ta sani ummin bazata so ace bata je ba amma bazata taba bata goyon baya ba,halin ummimsu ne a gidan aure maca ce mai tsananin biyayya ga abbansu ko layi uaja yace kada ta tsallake to insha Allahu ba zata tsallake din ba hakanan kaf yaran babu wanda zata bari ya tsallaka hakan ne yasa har yau har gobe har ma jibi inji shi abban nasu yake alfahari da kuma ji da ita Ta saki ajiyar zuciya bayan ta kashe wayar tana jan majina hadi da son maida kukan ta,alwala ta daura tayi sallar magariba ta zauna kan sallayar tana jiran a kira isha,hakanan fadila take tana da kwadayin wannan garabasa da ake samu ga duk wanda ya idar da salla bai kuma tashi daga gurin ba,jira ne baifi na awa daya da rabi ba aka tada isha'i ta gabatar da ita duka harda shafa'i da wutiri sanann ta sake zama ta karanta subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil azim,don kanta ta gaji da zaman ta ninke abun sallar ta maida shi muhallinsa ta baro dakin sa hijabinta a jiki don dumin cikin hijabin ya mata dadi Cartoon ta maida tana kallo kan tashar m.b.c 3,lokaci lokaci tana sakin ajiyar zuciya saboda kukan da tayi,sannu a ahankali ta soma jiyo qamshinsa ,ta daga fararen idanunta ta maida su bakin qofar shigowa falon,cikin nutsuwa da sallama ya shigo yana sanye da jacket black blue sun haska farar fatarsa,sunyi amsarsa matuqa da gaske adorable structure dinsa ta fito sosai,sassanyan kyawunsa din nan ya bayyana cikin kamilalliyar tafiyarsa ya qaraso falon hannayensa sarqe a qirjinsa,can qasan maqoshinta ta amsa sallamar carelessness ya samu hannun daya daga cikin kujerun ya zauna ba tare da ya dubeta ba With bounded face yace"ki fito na miqaki kiga baby"tamkar tayi banza da shi ko tace ta fasa sai taga idan ma tayi hakan ai kanta ta yimawa ba wani ba don shi kam bashi da asara,ta miqe kamar marar laka ta shige bedroom dinta tana qunquni qasa qasa"sai an ma gama qonawa mutum rai sannan za'a wani tasa shi a gaba akaishi kamar wani dan qanqanin yaro" "idan baki zuwa ba saiki zauna ba ke ya shafa"ya fada a tsawace,baki ta rufe da sauri ta qarasa shigewa bedroom din don batayi tsammanin ya ji ba,lallai shi kuwa wane irin kaifin ji gareshi take mamaki cikin zuciyarta *NOTE*: assalamu alaikum masoya littafina saqonninku nata isheni da maganganunku game da littafina,duk da cewa na sani nayi muku bayani tun a farko na yadda rubutun zaici gaba da kasancewa sakamakon shirin fitar da shi kasuwa,na dauka tuni mun wuce gun saboda banyi zaton zanci gaba da baku shi littafin ta watsapp bama amma yanayin yadda kuke nuna qauna gameda da shi din yasa naci gaba da rubuta mukun duk da na rage yawansa kamar yadda na fada, To amma naga rashin fahimta na son shiga ciki,na farko har ga Allah yadda wasunku ke min bana jin dadi yana bata zuciyata,saboda bani da wani uziri da zai taso min a matsayina na yar adam a gunsu abunda kullum suke buqata shine nayi musu kawai typing na turo musu,sannan wasu babu yabawa saidai qorafi da zarar sun gama karanta wanda na samu na turo,hakan da suke yana kashemin gwiwa ne,maimakon suyi abinda zai qarfafa min gwiwa ko saboda gaba kada ku manta hannu ne keyi ba fada muke wayar na rubuta mana,kuma yau da gobe ai sai Allah,ni 'yar adam ce gsky da bana son abinda zai dameni ko ya samun damuwa a zuciyata nakan haqura da abubuwa da dama matuqar zasu jawomin damuwa,don Allah ina roqonki ku tsaya kuyi duba na fahimta game da ni,ni ba budurwa bace matar aure ce ku duba kuga yanayin hidimomin gida na kullum dake kan matar aure baya ga wadanda ka iya taso mata wadanda bata tsara da su ba a rana,ku dinga adalci kuna hukunci na gaskiya,mu fahimci juna don Allah wannan shi zaisa ni daku muci gaba da jin dadin alaqar dake tsakaninmu,wlh akwai abubuwa masu yawa da muhimmanci a rayuwata da nake yi kulluma da kafin fara muku rubutu amma a yanzu sun gagareni yi saboda rubutunku,na sani harka ta mutane sai kayi haquri tunda yadda muka banbanta a halitta haka Allah s.w.a ya ban banta mu a halaye da dabi'u,na gode Allah yasa mu dace Na biyu kuma masu ganin abunda aliyyu yake yayi yawa kada kusa gaggawa a lamarinku kuma kada ku manta shi haquri shine jagoran kafatanin lamuran mu na duniya bare haquri ga 'ya mace kuma acikin gidan aurenta hanyar shiga aljannarta riba ce ba kadan ba,ina so ne yan uwana mata muyi koyi da halinta koda cewa ba irin auren ta kikayi ba amma nasan baza'a rasa matsala daya ko biyu da kike iya fuskanta ba daga mai gida wadda shigen halin da aliyyu ya taba nunawa fadila ne to ga yadda ta shanyeta ga kuma ribar da ta samu,na godewa masoyana gana daya ,Allah yayi mana sakamako agidan aljanna ya hadamu dukkanmu a cikinta in kuma ci gaba da zama marubuciyarku ta gidan aljanna Mrs muhammad din[truncated by WhatsApp] 4:50 pm 23/8/2016 *WA YASAN GOBE?..* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *part 2* 1 Powder kawai ta shafa a fuskarta ta shafawa kyawawan labbanta lip glosses,atamfa ta zaro cikin kayan nata dinkin doguwar riga ne mai umbrella ta bude sosai an mata dogon hannu simple style ne,ta ware dan madaidaicin mayafinta ta yafa shi har saman kanta kamar yadda ta saba yafenta sannan ta fesa turare ta fito Yana tsaye a wajen motar yana amsar calling yayin da salima ke tsaye kusa da shi hannunta harde a qirjinta tayi kicin kicin da fusaka,sallama fadila tayi mata sai taga ta dauke kai don haka sai ta ja tunga itama tayi banza da ita,ya gama amsar kiran ya kashe wayar hannunsa na kan mabudin motar salima ta kalleshi tace"please dear"kai ya gyada yana cewa"dont mind" ya bude gidan gaba kusa da kujerar mai tuqi ya zauna ta bude baya itama ta shige,nasiru ya gaida ta cikin girmamawa a mutunce ta amsa sannan ya tada motar suka fice Tafiya ce kamar ta kurame sai ka rantse bata cikin motar sai shi da nasirunne ke hira jefi jefi galibi ma bai wuce zancan kasuwa,idanunta na kan titi yayin da zuciyarta ta lula duniyar tunani A bakin get suka dakata bayan mai gadin ya dage masu get aliyyu yasa nasiru yayi masa magana ya rufe ba shigowa za suyi ba,fadila ta tabe baki cikin ranta tana gulmar aliyyun,nasiru ya gyara parking din sannan ya fice daga cikin motar,fadila ta sa hannunta a kan mabudi zata fice "twenty minutes"haka ya fada cikin carelessness,ba abunda tace da shi tayi ficewarta "ko baka gaya min ba ai na sani uban masu tsari da qa'ida na duniya "tayi zancan cikin zuciyarta Da yake takwas na dare ma ta dan gota gidan ya samu sararawa daga cincirundon 'yan barka mutum hudu ta tarar Amina da mariya qannan mubarak ne sai maqociyarta guda daya sai kuma wata dattijuwa inna jummai wadda mahaifiyar mubarak ta kawo mata ita saboda kula da mai jegon da kuma jaririyar,alokacin da ta shiga ma tana kitchen tana kwashe tuwon da ta yiwa faridan,fadila nata qyalqyala dariya ganin inna jummai nata loda tuwon a flask tana ce mata"inna zanso naga dambarwar ku kam da farida don ba abincin da taqi jini irin tuwo,dama dai ni kika baiwa"innan da yake macace mai kirki da saurin sabo da jama'a tace"ai duk qinta kuwa da tuwo yanzu ya zama abokinta dole ta cishi tunda jego ya zo" Tayi sallama ta shiga falon faridan dukkaninsu suka amsa mata cikin fara'a suna dariyar hirar fadilan da inna jummai,farida kam ture kayan jarirai dake gefanta take tana cewa sister taho nan daya hannun nata kuma cup ne cike da tea tana sha sai hada gumi take inna kuma taqi ma a kunna fanka bare a.c saboda wai jego faridan zatayi irin na da,fadilan ta qaraso tana cewa " sister farida mai tsokana da yawon gidan qawaye yau gata dq baby" dariya ta basu dukkaninsu harda faridan,idanu fadila ta baza tana neman baby tace nifa baku nazo gani ba wlh ina 'yata ku bani ita naji duminta"yarinyar na hannun maqociyar ta ta nannade cikin farin shawul mai taushi ta miqe tana miqawa fadila ita hadi da yi misu sallama ta ajjiyewa faridan 1000 kudin barka ta mata godiya ita kuma ta fice Ta kammala shanye tea din tas ta dire cup din tana kallon fadila tace "sister da fa har nayi fushi kece ta farko da kika fara sanin haihuwarnan baya ga abbanta amma sai yanzu zaki zo mana tun dazu baby ke son ganin mummynta bata zoba sai da aka rigata gane mata ita" "hmmm lallai yarinyarnan kukan dadi fa kike da yaya yanzun ma ya barni tare ma fa muke"cikin zolaya wadda attitude din farida ne tun usulinta tace "wow