← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 84

Sashe 39

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

garin karkatawa ya wuce taga silmiyowar wani abu daga aljihun trouser dinsa ma baya amma bata zaci wani abu mai muhimmanci bane sai da ta sake matsowa ta sa idonta sosai sannan taga ashe wata 'yar kyakkyawar wallet ce ,da sauri tasa hannunta ta bude ciki,rupees(kudin india) ne masu yawa aciki a miqe,sai dan qaramin hotonsa wato passport,sai kuma wasu kati guda uku biyu na wasu shaguna dayan an rubuta *adishwar garment* shagon na cikin *janta cloth market hawkers plaza*ta maida shi ta duba dayan shi kuma na shagon *ajmeri fashion* shagon shi kuma na *hazarat abbas road Samuel street*,duk cikinsu babu shagon da ta taba zuwa tunaninta na kan yadda Atayi masa da wallet da kuma yadda zata sake samun damar hanawa da shi,tana duba kati na uku uku na dauke da sunan hotel din da ya sauka haka jikinta ya bata tunda su muta nene da komai ka siya ko kayi mu'amalar ciniki da shi sai sun baka rasit ko card nasu,tasan hotel din tunda takan ziyarci cikinsa lokaci bayan lokaci nan kusa da makarantarsu yake Ta maida duka kayan ciki tana sauke ajiyar zuciya,bayan sun kammala siyayyar suka koma cikin makaranta,da daddare ta canza shiga irin tamu ta hausawa atamfa ce saidai dinkin riga da skert ne tayi kwalliya sosai a fuskarta,ba wata tafiya ce mai nisa sosai ba tsakaninsu don haka irin keken nan nasu ta hau ya qarasa da ita,bata sha wahalar samunsa ba saidai da yake hotel ne na manyan mutane akwai tsaro sosai da kuma tsari duk magiyarta basu yarda sun bata number din room din ba sai da sika kirashi suka sanar masa,duk da yayi mamakin mai neman nasa kuma sunce mace yace a bata number din baisan me ya kawota ba ko da taimakon da zai iya bata Ku biyo Mrs muhammad [10/16, 1:47 PM] Salma *WA YASAN GOBE?...* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *part 2* Sai da tayi knocking sama da sau biyar sannan aka bude mata,fuskarta ta wadatu da murmushi yayin da tasa take a tsuke kamar hadari,"sannu ko?"tace da shi cikin fara'a"yauwa sannu" ya fadi adan dake yayi bake bake abakin qofar babu wata hanya bare ta sa ran shiga ciki don ko kalan labulen bakin qofan ba zata tantancewa ba,cikin qosawa ya gyara tsaiwarsa ganin tayi shiru yace "I hope lafiya dai ko?"ta sake yin murmushi a karo na biyu ya zaro wallet din daga cikin yar purse dinta dake damqe a tafin hannunta sannan ta dubeshi tace"wannan ka yar dazun a mall din paras mahal collection"ta miqa masa tana dan murmushi,ya sa hannu ya amsa yana cewa"thank you verry much"ya juya yana qoqarin mai da qofarsa ya rufe Da sauri ta dakatar da shi ta hanyar cewa"haaabaaa haabaa malam babu ko goron tsintuwa? " a qagauce ya dakata ya juyo yana cewa"nawa kike buqata?"t saki wani mayaudarin murmushi"ba kudi nake so ka bani ba,kawai passport nake so na cikin wallet naka sai kuma phone number dinka shikenan abunda nake buqata Girgiza kai yayi hadi"it can't ki zabi wani abun dai daban banda wadannan"ta kanne ido daya tace"ni su din dai nake so"kafewa yayi kai da fata bazai bata ba"i told you ba zaki samu ba"itama kafewa tayi akan shi take so indai alherin da tayi masa yake son rama mata,daya lura tana da yawan taurin kai sai ya bude wallet din ya zaro rupee dubu daya kwatan kwacin kudin nijeria a yanzu naira dubu hamsin ya ajjiye mata saman qafarta ya juya karo na biyu yana shirin sake rufe qofarsa Ta tabbatar idan ya subuce mata a yanzu mawuya cine ta sake samun dama kwatan kwacin wannan don haka cikin zadin nama ta tattara kalmomin"idan kamin haka baka min adalci ba zaka kashe min gwiwa ne na aikata aikin alkhairi,ni bana buqatar kudinka Da haka ta kashe masa gwiwa don bazaiso ta zama mara kirki ba ta sanadinsa ya sani idan har hakan ta faru yana da tagomashi a agun Allah,dole ba dan yaso ba ya bude wallet din ya bata passport din hadi da karanto mata numbobinsa ta kwafe tsaf bisa wayarta tayi serving,tun daga lokacin hotonsa shi ya zama abokinta da zarar ta kadaice shi take sawa a gaba tayi ta kallo,kyan Aliyyu na qayatar da salima ya tafi da imaninta 100% Takan bata lokaci tana gurin kiransa amma ba zai daga ba,ta jure hakan ba tayi zuciya ba tana ci gana da kiransa,yau da gobe tafi qarfin wasa har takai da idan ta kirashi sau goma zaoyi qoqari ya daga mata ko sau daya ne shima daga gaisuwa bai bari a wuce haka,an halicci zuciya abisa son mai kyautata mata to hakan yake don kuwa kulawa sosai salima ke nunawa aliyyun mutum ne dama da bai taba budurwa ba samun hakan yasa ta shiga cusa masa ra'a yinta sannu a hankali har ya minta da ita ya bada amannar zata zama abokiyar rayuwarsa Asalin salima 'yan katsina ne mahaifanta,yan boko ne na bugawa a jarida irin mutanen nan ne da ake cewa"yan boko aqida"wato ga karatun bokon ga kuma bin duk wasu aqidu nasu, bokon suke da gaske babu sirkin addini ko kada cikin mu'amalar rayuwarsu ta yau da gobe bokon kawai akasa agaba shine madubi,hakan yasa tun a nijeria salima ke alalace don babu kwaba balle hantara da zarar kin kai shekaru goma sha takwas a gidansu to kina da yancin yin komai da kika ga dama,iyayenta na da arziqi daidai gwargwado don su suka dau nauyin karatunta ta fita indian Mutum daya ne salima ta yarda da shi ta sallama masa jikinta a nijeria suke harkarsu duk da tana bawa wanda taga dama kanta yayi tabe tabensa don a cewarta ita babbar harka take,sai kuma zuwanta india ne wani abokin karatunta rahul,shima din tunda ta hadu da aliyyu tayi mishi fata fata sukayi handing over don kuwa tunda ta ga aliyyun tayi amanna ta samu kalar namijin da take so ya zama miji a gareta ya hada komai hundred percent Cikin lokaci qanqani salima ta dage a tada maganar aure don kuwa tsoron take kada ta rasa aliyyun saboda tana ganin yadda mata jinsin qabilu kala kala dake indian mazauna can yan asalin indian da kuma baqin haure ke kara kaina akansa abunda ya sauqaqa abun ma babu fara'a ma bisa fuskarsa ko yaushe tana daure ne tamau balle kice zaki kawo masa wargi Bai damu ba suka koma gida nijeria aka gama komai sannn ya dauko ta suka dawo indian saboda business dinsa ita kuma ta samu ta kammala karatunta,dole salima ta yakice duk wani abokin shashancinta saboda matsananciyar qauna da take ma aliyyun Ba qaramin tashin hankali aliyun ya shiga ba yadda ya sameta ba budurwa ba duk da bai san ya budurwar take ba hakanan tasha stitches duk don ta matse,yafi aqalla sama da wata abun ma dukansa amma kasancewar sa mutum mai tsananin kishi da baijin zai iya auren mace ya saketa wani ya aureta yasa ya qyaleta,bugu da qari tsantsar qauna da take masa tamkar ta fidda ranta ta bashi,yayi imanin idan ya rabu da ita mawuyaci ne taci gaba da rayuwa parfectly Cikakkiyar kulawa aliyyu ya dinga samu sosai daga farkon aurensu duk da ya fuskanci qalubale da dama na wasu ayyuka na cikin gida wanda ya zama dole kowacce *cikakkiyar mace* ta iya su,kama da girki zuwa tsaftace gida amma sai yayi haquri da hakan yake koya mata wasu abubuwan da niyyar idan sundawo gida nijeria zai turata makarantar koyon irin wadannan abubuwan Abu na farko da ya fara kawo babbar baraka a zamantakewarsu wanda shi ya zama sila kuma sanadiyyar barkewar alaqar dake tsakaninsu shine,wata uku da yin aurensu ta soma rashin lpy,tuni suka yiwa mumbai general hospital tsinke sabodancita take sosai ,ba bata lokaci likita ya fara aikinsa cikin dan taqaitaccen lokaci sakamako ya bayyana sun samu qaruwa Allah ya albarkaceta da samun juna biyu Ba qaramin tashi hankali da razana aliyyu ya tsinkaya ba kan fuskar salima shi da ya tsammaci ganin farinciki,tun acikin asibitin take kuka wi wi har suka iso gida,duk da ya kawo abubuwa da dama cikin ranta game da kukan da take sai dai ya hani zuciyarsa da yanke hukunci bisa zato da zargi,don ya tabbatar ya matsa mata da tambayar mekw faruwa? Bata yi qasa agwiwa ba kuwa budar bakinta tashin farko ta ce masa"gaskiya darling ban shirya haihuwa ba yanzu babu abinda ke cikinta banda wahala da tsofar da mutum,just shekarata ma nawa da zan fara shiga rayuwar raino da wahalar 'ya'ya?,am just 25 fa"ta qaraahe maganar idanunta na malalo da hawaye Da fari ua dauka rashin fahimta ne saboda boko da ya dabai baye rayuwarsu don haka sai ta ma bashi dariya ya murmusa idanunsa akanta yace"that's my salima,wannan tunanin naki fake ne it's not real,haihuwa ai ni'imace daga Allah wanda kudi ko mulki ko wata isa basu isa su baka ita ba,tsufa kuma ai lokacine,idan yazo babu abinda ke tareshi,bama haka ba idan kika ga haihuwa tasa mace tsufa ya danganta ko daga gareta ne rashin gyara ko kuma daga yanayin kulawar da take samu daga mijinta,ke kam baki da wannan matsalar ko daya,come on baby dont bother your self kinji,I promise I wil be with you cikin ko wanne irin yanayi" Wannan duk baiwa salima ba tun aliyyu na rarrashinta har ya gaji ya sanya mata idanu,daga qarahe ma ganin ya zuba mata idanu sai tayi tsammanin ko ya haqura ne gaba daya?,sai kuwa ta fito masa da aniyarta na son zub da cikin wai ko don ta samu taci gaba da yin karatunta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa tunda tana final year dinta watanni kadan suka rage mata zata fuskanci exams A ranar taga bacin ran aliyyu irin wanda bata taba ganin irinsa ba,yayi mata kaca kaca ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba ya mata jan kunne mai zafi akan kada ma ta yarda koda mistake wani abu ya samu cikinsa bazai lamunta ba bare kuma intentionally,ta tsorata ainun amma duk da haka ta kafe ta turje akan bata ga abunda zai sata zam da cikin ba tunda bata so ai ba'a dole shi kuma yace zai mata dolen kuma zata gani,kamar ta haqura amma zugar qawaye na sake tunzurata,cikin rikici ta dinga rainon cikin ji
Chapter 39 · 0% Book details