Sashe 41
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta qarasa ficewa fit daga ransa,bata da wani abu a yanzu da zata burgeshi da shi Ganin momi ta soma tsanantawa a al'amarin sai ya soma shirin komawa indiyarshi ba tare da sanin kowa ba bai so ba ba kuma a son ranshi ba don baiso yayi nisa da yarinyarshi sai da ya kammala ne suka sani,momin taso ta hana abba yayi mata magana aka ta tsagaita hakanan da Maganar dole sai salima ta dawo idan da rabo zaman bai qare ba zata dawo ne,aliyyu mai tsananin biyayya ne bashi da tarin kunne akan duk wani umarni da iyaensa suka bashi,yana dai da zurfin ciki ne da nauyin baki,tun yana yaro idan suk ce yayi abu ya kafe baiyi ba to yanada dalilinsa ne mai qwari wanda sai daga qarshe idan suka bincika sai suga lallai yana da gaskiya Momi ta gamsu da bayanin abban ta kuma yiwa aliyyun fatan alkhairi da samun dacewa,aliyyu ya bar nijeria cike da kewa da qaunar 'yar diyar tashi tsoka daya a miya khadijatul iftihal,ya tanadar mata duk wani abu da zata buqata daki guda ya ware mata yajibge mata komai hatta da ruwa da zata sha ya tanadar mata bai bari ya dorawa kowa wahalarta ba harda kayan banza ma da wofi wanda bata buqatarsa,hakanan ya bude mata account duk wata yana saka kudi a ciki yace da momin aje a cira ayi mata abinda tale da buqata,to kawai take cewa kamar yadda uncle abba ya umarceta don shi tuni ya karbe ragamar komai din kudin da aliyyun keta aikin turowa uncle abba yace abarshi cikin account din ta amfanesu idan ta mallaki hankalin kanta Wata shida kacal salima taji ajikinta qaunar aliyyu da yarinyarta tamkar zata zautata cikin begensu take kwana take tashi,yayin d iftihal ke cikin walwala da samun gamsashshiyar kulawa gata da soyayya ta qannen uba kakanni na gun uba da kuma dangainsa,tayi bulbul abinta madarar dai ita taci gaba da karba don itama taqi nonon kowa zakaran da Allah ya nufa da cara sai gashi cuta mai taba yaro bata taba samun yarinyar ba don ko haqori tashi sukayi suka ganta da shi ya soma fitowa,ga wayo a gunta gane mutane da kaifin basira Shekara daya da rabi salima ta kasa daurewa,ido ta rufe ta soma neman aliyyun,saidai ya riga ya toshe duk wata kafa da zata sada shi da ita,sai daga baya ta samu labarin ya koma india,ba bata lokaci tayi visa ta bishi don zamanta da aliyyu ta samu dukiya sosai kasancewarsa mai sakin hannu shi yasa hatta zaman gidansu take jin bai mata ba Acan din ma bata sameshi da wuri ba don ya canza gari ma gaba daya sun zauna a mumbai ne shi kuma ya koma new Delhi taci wuya ka su hadun saidai haduwar tasun mabata haifar mata da d'a mai ido ba,kaca kaca yayi mat irin wanda bata tsammani ba ya kuma jamata kunne da idan har ta sake suka kuma hada hanya sai ya wulaqantata,ta samshi qwarai idan ya fusata baida dadi iya kuma qurewa ta sani ta qureshin don haka bashiri ta tattara ta dawo nijeria ba tare da ta cimma nasara ba Aliyyu bai waiwayi nijeria ba sai bayn shekaru uku cike da nasarori da budi masu tarin yawa wadanda bai taba tsammatar samunsu ba,company nasa ya bude babba acan hadi da qulla harkokin kasuwanci kala daban daban da wasu manyan kamfanonin,yazoya taras salima naci gaba da bibiyar rayuwarsu shida yarsa taqi aure sam duk wadata tsaya da shi sai taga ba namiji bane ganinsa take kamar mace yar uwarta taqi sauraron kowa da komai,itace kira saqonni na email sms duk wata kafa da ta samu ya rabu da duk wasu layukansa saboda ita amma ya rasa yadda take samun sababbi,sunzo don a basu iftihal yafi sau hamsin tun yana india suke da muradin haka ya gaya masu su da iftihal saidai su ganota daga nesa don bata buqatarsu *samira* Shekarunsa hudu da dawowa ya hadu da samira gun bikin abokin kasuwancinsa,tunda ta qyalla ido a kansa ta qwallafa ranta,ta rasa ta inda zata samu shiga domin kuwa baida walwala ko sakin fuska shi yasa take fargabar tunkararsa,da yake tare yake ta hidimar bikin abokin nasa da iftihal dinsata lura da yadda yake ta nan nan da yarinyar ta samu kuma information kanncewa 'yarsa ve da yake tsananin qauna sai itama ta jata ajiki sosai tattali take nuna mata kamar babu gobe,shikam mai son wanda ke son iftihal dinsa ne don haka ya sakar ma samira duk da ya ja jikinsa sosai da fari saboda yakan tuna yadda ta kasance masa a baya tsakaninsa da salima Itama tazo akan gaba don lokacinne tsananin ya sake aure ya masa yawa a gida ahi kuma a zahitin gaskiya a wannan lokacin bai da time na duba mace,ganin ya samu maison iftihal dinsa yasa ya amince daga qarahe ne ma momi ke masa albishir din itafa ba zata bashi iftihal ba donnta riga tazo kenan,ba yadda ya iya duk da son da yake wa yarinyar tasa Sai da salima ta gasu sosai fiye da tsammaninta wanda tadinga jelen kamun qafa da momi da abban da a baya ta watsawa qasa a ido kullum tana cikin gidantana magiya sannan ta samu dawowa gidanta,gidan da ta tarar ya kubce mata har wasu biyun sun samu mazauni cikinsa,ya ta iya da ranta son da take masa yasa bata ji wani abu ba tayi zamanta duk da a baya tana daga cikin matan dake iqirarin basu ba kishiya don ba zasu iya zama tare da ita ba *_dawowa labari_* Washegari tun qarfe tara fadila ke shirin fita suna,tayi wanka ta shirya tsaf cikin shadda dinkin doguwar riga ne yasha aiki daga sama har qasa butter colour ta debi wadanda zata sauya a can kala biyu ne da tayi musu anko ita da faridan zasu sa tare ta shirya iftihal cikin itama doguwar rigar yan kanti wadda ajiya ta bada aka siyo mata hade take da takalminta da ribbons dinta red ce in and top ta tsaya mata iya qauri takalmin boot ne na yara fari qal tayi ma gashin yarinyar ado da fararen ribbon tayi kayu matuqa kasancewar yarinuar mai yalwar gashi mai tsawo da santsi Hat ta tada motarta iftihal ta hango abban nata ta balle murfin motar ta fice aguje,bayan ta duqa ta gaidashi ya dauketa yana wulla ta a sama shiko nauyi bata yi masa"cewar fadila cikin ranta tana satar kallonsu,tana ganin iftihal na nuno mishi ita,ya juyo ya kalleta suka hada ido tayi maza ta sunkui da kai don kada qwayar idanunsu ta hadu ya saka mata dafin da ya saba jefa maya cikin zuciyarta na qarin qaunarsa,"verry neat ya fada sannan ya dauke kai"iftihal ta leqa fuskarsa "daddy munyi kyau kuwa"yayi kissing kumatunta yace kinyi kyau sosai my dear"tadan bata fuska tace "anty na fa?"yayi yar qaramar murmushi yace "both of you""thank you daddy"ya sauketa bayan ya sake kissing dinta tana daga masa hannu ta zura aguje ta dawo cikin motar tana dariya Mrs muhammad ce [10/16, 1:50 PM] Salma *WA YASAN GOBE?..* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *part 2* Fadila tayi murmushi sannan ta tada mota iftihal tace "anty Abba yace munyi kyau wai na zama 'yar gatan anty ni 'yar gatanki ce wai anty?"ta shafa kanta da daya hannun nata tana murmushi tace"iftihal ke 'yar gata na ce mana" Minti arba'in suka qarasa gidan da yake safiya ce babu yawaitar mutane sai 'yan uwa na jiki sosai,su hajja gana(kakarsu ta gun uba) umma a'i anty hafiza rumaisa da sauran 'yan uwa na nesa da na kusa,Fadila ta fada jikin hajja gana tana cewa bari na more cinyar 'yar tsohuwa" hajja gana ta sa dariya da yake sunfi shiri da Fadila fiye da farida"more abinki kafin kema Allah ya kawo miki masu more taki"murmushi fadilan tayi sannan suka soma gaisawa da yan uwan hajjar na tambayarta mai gidan tace lpy lau yana ma gaisheki Kafin azahar gidan ya tumbatsa da jama'a,ko ta ina,bayan azahar kuma da kadan sai ga family din aliyyu momi ce kawai banda ita,cikin bedroom din farida sukayi zamansu anata karbar baqi Rabi'ah ta kalli fadila lokacin da take canza kaya su anty hauwa na sallah tace "ni dai anty idan kuka tafi chinan nan qana nan kaya kawai nike son tsarabata"fadila ta dago ta dubeta bayan ta gama zuge zif din rigarta tace"wace china kuma rabi'ah"dariya rabi'an tayi"kai anty ko baki son asan zaki ne?"cikin rashin fahimta take dubanta tana qoqarin daura dankwalinta"wai wa yace miki zani china rabi'ah?"ta sake qyalqyalewa da dariya tace"tun last week fa yaya aliyyu ya gaya ma momi an gama ginin sabon company dinsa da zai bude zai wuce china cikin satin nan ke da shi,shekaran jiya kuma sai ga shi ma da visa dinku a hannu ta fito jibi zaku tashi da daddare amma anty kice baki sani ba? A badini zancen yayi matuqar kidima fadila ya daketa sosai amma sai ta dake don kada ta bada satar amsa ta qago murmushin yaqe"kinsan halin yayanku akwai lafiyar miskilanci dazun dai yake cemin idan na dawo zai min wani albishir to ina tsammanin shine"sumayya da a lokacin ta sallame sallarta tace "har Allah Allah nake na idar kinga haukan da salima ta dinga yi wai da ita za'a tafi?"su sumayya suka kwashe da dariya rabi'ah tace"qara fa ta kawo gun momi sai gata tayi tsuru tsuru da ya aliyyu yake fadin babu abinda suka iya ba inda zai je da su su zamar masa nauyi"sumayya ta dora "qarshe ma momi da yake zayyano mata matsalarsu kunya ce ta isheta ta bar falon ba shiri tace suje gida su shirya kansu mu dai bamusan ya aka qare ba bata sake tada zancen ba ma"anty hauwa tace"ku kuma gaku sarakan gulma ba,kwaci qaniyarku da ya kamaku kuna labe ai" Duka wunin ranar bunda ke cin zuciyar fadila kenan zancan tafiyar yayi masifar daga mata hankali,sai ta rasa nutsuwarta gaba daya,lokaci lokaci qwalla kan taru a idonta ta faki idon mutane ta matse ta,gaba daya sai kuzarinta ya ragu,Allah Allah take su kebe da farida,bata tsammani alkhairi aliyyu ke nufi da tafiyarsa da ita,nufinsa ma fa kenan gaba daya tabar aikinta da take masifar so ta kuma fara jin dadinsa yake kuma debe