← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 84

Sashe 18

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da damuwoyi masu yawa tun yanzun......ya danja fasali sanna ya miqa hannunsa ga wayarta dake gefanta abinka da giant tuni hannun yakai ba tare da ya hau gadon ba ya lallatsa sannan ya ajjiye mata yace"ga abinci nan da magunguna ki sha,then ga number ta if there is any problem contact me"daga haka ya juya ya fita ba tare da Saura ron komai ba Sai abun ya zamewa fadila wani iri ta jima akwancen kafin ta samu damar miqewa zuciyarta na qarfafa mata gwiwa ta tashi ta taimaki kan nata kamar yadda aliyu ya shawarceta,tq shiga toilet tayi fitsari sannan ta daura alwala wai ko zata ji sauqin zugin dq zuciyarta ke mata,ta dawo bakin gadon ta bude ledojin daya magunguna ne a ciki daya kuma gasashshiya,ta dinga zare tsokar tana ci zuciyar ta dauke da addu'o'in samun sauqin daga quncin zuciya(inda Allah ya taimaki fadila kenan bata mantawa da add'a duk irin situation din da take ciki,muyi koyi da ita yan uwa domin hatta qaddara babu abinda yake tareta sai add'u'a,mu dinga tuna Allah a yayin da muke cikin jin dadi da walwala sai Allah ya tuna da mu lokacin da mu kuma muke cikin qunci da neman taimakonsa wannan fadar annabi ce s.a.w,kai ta addu'a da sannu Allah zai isar maka,take note pls!)jin naman take kamar magani mai daci haka taci gabada dannashi har tqji kamar zata yi amai,ta balli.maganin adadin yadda aka rubuta tasha sanna ta dan zauna na mintina don abincin ya fada mata sanna ta ja pillow ta kwanta,cikin ikon Allah ta dinga jin sassuci a zuciyarta,ta jawo wayarta sai taji tana qamshin aliyu ta soma duba contact dinta taga number din da yace yasa mata ai kuwa a rukunin A taci karo da sunansa full name dinsa ya saka mata ta bude numbers din tana qare musu kallo suma special ne don cikin taqaitattun daqiqu zaka iya haddacesu,(mrs muhammad nace ko na sato muku numbers din A.s maitama ne cikin wayar fadilan?to gasu 0803344....... to naqi don naga wata har tana saurin kwafa ba ruwana ku da fadila )ta zuba musu ido kamar tana son ganin fuskar mamallakin numbobin da ta gaji da kanta ta rufe wayar ta maida ta qarqashin filon ta lumshe idonta tana maida numfashi cikin zuciyarta ta soma tilawar suratu yusuf tana yi tana bin labarin annabi yusuf din da Allah s.w.a ke bayarwa cikin surar,zuciyarta ta mata sanyi damuwarta ta ragu sosai lallai Allah yayi gaskiya da yace(ala bi zikrillahi tadma'innal qulub/ku saurara da ambaton Allah ne kadai zukata ke samun nutsuwa) To fa makaranta na labari yanzu muka soma shigarsa kuci gaba da jumurin bina insha Allah zamu cimma gaci Dumbin godiyata a gareku Mrs muhammad ce ........ [10/16, 12:35 PM] Salma Wa yasan gobe? Written by safiyya Abdullahi musa huguma Washegari misalin sha biyu na rana tana kitchen tana tafasa ruwan lipton so take ta dan sha ko zai warware mata ciki don tun tashinta yau ba abinda ta iya ci,muryar farida taji tana qwali mata kira da gudu ta fito suka rungume juna suna dariyar farincikin ganin juna ,farida ta dan janye fadila daga jikinta tana cewa sister yi a hankali kada ki mana asarar baby,fadila ta ballamata harara tace"wai ke wa ya baki wannan labarin qanzon kuregen?farida tace bayan mun gama waya jiya da ke da daddare rabi'ah ta kira ni take gayan again,fadila na qoqarin komawa kitchen din tace uhm sai ki zauna ai kiyi ta jiran cikin,farida tayi dariya ta bita,maimakon daba lipton sai ruwan zafin ya koma na girki,suna yi suna casar hira,suka kammala suka zuzzzuba su a warmers suka wanke kwanukan hadi da gyara kitchen din Wash! Inji farida bayan ta zauna fadila ta kalleta tace kin canza sister fa sosai kinga qibar da kika fara yi?farida tayi murmushi tace ke dai bari ya fadila ina tsammanin ciki ne fa?,fuskarta cike da fara'a tace ke dan Allah,tace wlh da jibi ko gobe mubarak ya matsa sai naje an min test wai kada na jawo masa asara cikin rashin sani ni sai naga kamar ba shi ba,kasala kawai fa nake da yawan bacci,fadila tace,a'ah nima fa ina bayan mubarak sister kije a dubakin meye amfanin zaman haka,kina likita ai kinfi kowa sanin alfanun abin,tace insha Allahu gobe zamu je Farida ta janyo jakarta ta bude ta miqawa fadila takardunta,cikin zumudi ta buda tana duba result din ba abinda bakinta ke fada sai alhamdulillah,domin kuwa yayi kyau fiye da yadda ta tsammata cikin farinciki tace da farida"burina na gaba farida inga na soma aikin media shine burina tun ina qarama"murmushi ta sakar mata tace"kwantar da hankalinki ya ahmad yana can yana miki wannan aikin don kuwa freedom da express tuni sun karbi takardunki jira yake kawai yaji daga garesu,wani farincikin da qaunar yan uwanta ya sake kamata Tana toilet tana wanka ta bar farida a afalo tana kallin arewa 24 suna haska maimaicin shirin boyle bitmesin wato kyautata rayuwa da yake jiya tace tayi missing bacci ya dauketa bata kalla ba,ta jiyo hayaniya sama sama ta tsinci dai muryar anty hauwa din haka a gurguje ta gama tana fitowa ta shirya kanta cikin shigar doguwar rigace ta shadda wadda aka mata paint work mai tasadar orange ce akayi mata kwalliyar light blue,body spary kawai ta fesa ta daura dankwalinta ta debo magungunanta wadanda zata sha da rana ta fito falon,rabi'ah ce da sumayya da anty hauwa,cikin fara'a suka gaisa suka mata sannu da jiki"tace ai na samu sauqi ina momy da iftihal mutuniyata,anty hauwa tace suna gida gurin momyn nace ne ba da wanda zanzo duk har su kausar suna gunta muhammad ma tunda ba nono yake sha ba acan na barshi don suna zamu wuce dqga nan wata maqwafciyata ce ta haihu to kuma da yake haihuwar ta danzo da matsala a gidan su take acqn za suyi taron,tace eh Allah ya qara mata lpy,amin inji anty hauwa Nan suka shiga hira abinsu minti talatin suka miqe suna shirin tafiya fadila dake ta qoqarin zuba musu abincin tace anty ga abinci don Allah ku tsaya kuci,anty hauwa tace bayan lemo da cake da kika cika mana ciki da shi alhamdulillah wlh,rabi'ah tace nikam anti fa na fasa rakiyar nan gidan sunan kuce da maman hidaya ina mata barka na taho anjima farida ta saukeni a hanya,sumayya tace"dama na sani anti ba rakaki zata yi ba ina ji tana cewa yau ana rana da yawa nasan dama daga nan gidan ba inda zata dara"aishikenan muje mu gaisa da samirah sai.mu wuce,inji anty hauwa,sumayya ta coge sannan tace a'ah anty nikam zan jiraki cikin mota ki shiga ki fito tayi saurin yin gaba damma kafa antin ta tsayar da ita,fadila tace "baki kyauta ba sumayya idan kika wuce baki gaidata ba"rabi'ah dake zaune tace wlh anty ko nice ba zan je ba,farida dake ta faman cin abincinta abunta tace qyalesu sister mai daki shi yawan inda yake masa yoyo ,ai kuwa dai sister farida sai.kaje kayi ta bugu taqi budewa gashi fa kana kallo ta tana kalloka qiri qiri,bayan kuma ta bude sai tayi.bake bake a bakin qofa ta tsare ka da ido tana wani ce maka meye?kamar wanda kazo maula gurinta,duk suka kwashe da diyar yadda rabi'ah ta gwada yadda samiran keyi banda fadila da ta dan murmusa gami da girgiza kai tana mamakin halayya irinta samirah Biyar da rabi farida ta dauki rabi'ah suka tafi suma sashen sai ya dawo sai ita kadai ta so ta yiwa farida zancan dawowar maman iftihal sai kuma taga mai hakan zai dadeta da shi iyaka ta taya ta jimami sai shawara wadda a yanzu ita ma bawa kanta da kanta take,tunanim data fara yin zurfi a ciki ne yasa barin kanta ya soma ciwo bata yada hakan yayi zurfi ba ta tashi ta jona home theatre dinta ta saka cd plate na karatu ya karade falon Takwas da mu mintina na dare nasiru ya turo hancin motar ogan nasa cikin gidan,ya samu parking space ya daidaita tsayuwar motar sanna ya kasheta,a hanzarce ya fito ya budewa aliyu shima ya fito sannan ya miqa masa keys din motar yana fadin gashi sir ya amsa yana cewa debo min files din nan na sit din gaba,ya debosu ya bashi sukayi sallama aliyu ya sallameshi,hankalinsa gaba daya ya yi gaba burinsa kawai ya isa sashen nasa ya watsa ruwa a jikinsa ya samu ya kwanta ya huta,ya soma tafiya idanunsa suka kai kan sashen nata babu wadatar haske kamar bangaren samira dake tarwai da haske harda qarar abin kida ya dauke kai ya shige Yana fitowa daga toil et ya zabi doguwar riga jallabiya fara sol.mai yankakken hannu ya saka ya feshe jikinsa da turarukan baccinsa masu sassanyan qamshi kan sofa ya fada ya miqe qafafunsa sannan ya hardesu ya kansa na kallon sama yasa daya hannun nasa ya shafi cikin sa,yunwa yakeji amma ya rasa inda za shi ya samu abincin da zai gamsar da shi,mutum ne shi.mai tsan tsami ba ko ina yake iya saki jiki ya ci abinscinsu ba sai ya yarda da ingancin tsaftarka hakan ne yasa ya tsani masu aiki hakan yasa tun yana gida ya yi ruwa yayi tsaki ya hana mominsa daukar masu aiki yace meye amfani su sumayya duk da suma bai yarda ko kadan yaci girkinsu sai na mominsa Ya tashi ya qarasa fridge ya bude ya dauko yoghurt na l&z ya hado da fura ya samu cup ya dama ya sha ,ya sake tashi ya maida cup din kitchen sannan ya qarasa window dinsa yana bude glass din don ya bawa iska daman shigowa duk da iskar a.c da ta mamaye dakin kasancewar mutum ne shi maison natural air,idonsa ya sake fadawa kan bangaren nata duk da yaune ya shigo bashi da niyyar ganin kowa bacci yakeso ya samu isashshe don haka har wayoyinshi ya kashe su gaba daya Ya saki labulen yana ajiyar zuciya saboda tunawa da yayi haqqine a kansa ya kula da lafiyarta don rabonsa da ita tun jiya da ya batta da magungunan da ya siyo mata ,ya zari keys dinsa ya zura slippers dinsa ya fice Tana kwance a miqe sambal bisa kujera three sitter don tunda tayi sallar isha'i bata tashi ba agun falon tsit yake ba komai sai sanyin na'urar sanyaya
Chapter 18 · 0% Book details