Sashe 38
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*written by masoyiyar buk din wayasan gone..* *Part 2* 1 Fadila tacigaba da sake2 azuciyarta bata ankaraba taji ana bude get tana dago kaitaga harsun iso gida ashe,parking space ya nufa ya kashe motar,fadila dakekokarin bude motar setaji ya kulle motan ta waiwayo tadubesa suka hada ido tayi saurin dauke kanta zuwa gefe,shiko gogon sebinta ya ke da kallo can yace wai meye kiketa wani bata rai tamasa banza yacigaba damagana ,inatambayarki,kaikidanayine nayi lefi koso kike danabarki kikwana? nan ma shiru yaharzuka cikin tsawa yace wai badakenake maganaba salan wulakanci, Se asannan fadila tadago kai da fuska cike da hawaye tace wulakanci? wulakanci yawuce wulakantani dakakeyi Wanda haka har matanka suka sami damar gorantamun,Aliyu nayi nadamar aurenka auren bakinciki Inatabbatarma dabadan mahaifinaba dana dade dabarin gidan nan,cikin kuka takemaganar yayin da Aliyun yatsinci kansa da tausayinta Yakuma kasa cewa kome illa binta da kallo. Fadila tacigaba kodan matanka da ni ba irin su naso nayi kishi dasuba,naso ahadani da wayanda suka San mesukeyi bawadannan da kake kallo amataba nibanga mata anan ba kuma duk ajin naka akan salima da samera yakare ragowar wasu,cikin bacin rai yadakamata tsawa,itako ta dannan motar tabude tafita da gudu tanufi sa shinta,tana shiga tafada kujera setaji ya akayi tayi wadannan magana,setaji kamar bats kyautaba cankuma wani bangaren zuciyarta tacemata garadakika masa haka yasan fa kinsan mekikeyi kuma yasan badan shikike gidanba Dan biyayyar iyayankine,tamike tashiga toilet tayi alwala ta fito ta tada sallar isha dabata samu tayiba. Can Aliyu kuma kasa futa yayi daga motar jikinsa duk yamutu zuciyarsa ta cunkushe abinda yafi damunsa shine kalmanta datayi kansu samira da salima domin yakaratunawa da yanda yasamu samira adarensu nafarko,sannan Salima bayan rabuwarsu itama ba agida tayi rayuwaba,yadafe kansa karo na farko da naga A S metama na kwalla daya nazurarowa daya bayadaya yace inna lillahi wa inna ilaihirraji un.tabbas jidakai bekama ceniba domin ina tare da wadanda basu cancanci suzama iyayan yayanaba,gashi inakallo se haihuwa ake Wanda akai bikinmu tare duk sun haihu,su naji kowacce tace batashiryaba itakuma wanan yarinyar banashiga harkanta,gashi du k ta gane kome,Aliyu yacigaba da hawaye yana maibakkincikin abubuwa kala kala yadaure ya fita daga mortar jiki akasalance yanufi bangaransa yanashiga ya kulle kofar yabar makullin ajiki sabida bayasan ganin kowa domin koda sunzo sunyi amfani da makullinsu bazebuduba.yashige bedroom yafada gado yacigaba da tunani aranar dai Aliyu beruntsaba Dan maganganun fadila kemasa yawo akwalkwaluwarsa, Itako fadila cikin nishadi tayi barci domin tafidda wani tabo da kedamun zuciyarta. *amun afuwa Mrs Muhammad nayi muki shishshigi amma haka mukeson buk yadawo munakara mikamiki godiya dayabawa Allah yakara basira kidora saga inda natsaya domin zansamu goyon bays amma kitambayi friends sunyarda kidora *bye nabarki Lfy Wanda sukaji haushi suyafemin kar azagen nima wlh soyayyar buk din yasa nayi Ba Mrs Muhammad bace [10/16, 1:46 PM] Salma *WA YASAN GOBE?..* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *part 2* Qarfe tara fadila tayi wa iftihal wanka itama ta shirya cikin riga da skert na atamfa a cikin qana nun kayanta ta cirowa iftihal wasu riga da skert dama sun mata kadan jajayene in and top ta raba mata gashinta gida biyu ta tufke mata da ribbon sosai iftihal tayi kyau suka yi break sannan ta soma gyara part dinta kafin ta isa ga na aliyyu don duty dinta ne duk inda ta shiga yarinyar na biye da ita ita ala dole sai ta taya ta aiki sai da fadila ta bata mopping din kayan kallo sanna ta rabu da ita Fadila ta fito tana goge hannunta da duster bayan ta gama aikin ta iftihal dake ta fama da chocolate tace "anty ina daddy na?"murmushi fadila tayi ta kama kumatunta tace"kwantar da hankalinki 'yar daddy yanzu zaki ga daddy shiga daki bakin gado ki dauko min hijabina"da gudu kuwa ta shiga sai gata da shi a hannu ruwan madara ne iya qugu wanda ya shiga da atamfar jikinta sosai,ta kama hannun ift ihal din bayan sun rufe qofan Tana sa kai falon taji hayaniyar sama sama muryar salima ke a sama,tana tsaye hannayenta harde saman qirji kan aliyyu shi kuma na zaune kan kujera yana sanye da kayan bacci na maza ruwan madara shima hannun nasa harde a qirjinsa ,shigowar su yasa salima yin dif daga maganar da take yi din gami da sakin fuskarta daga tsukewar da tayi tana dan binsu da kallo(salima akwai duniyanci)sam bata lura da iftihal ba da suka shigo tare sai da yarinyar ta zame hannunta daga na fadila wadda ta shige kitchen ta ruga a guje tayi gun daddynta tana cewa"daddyyyy daddyyyy...."kamar yadda ta saba ta durqusa a agabansa kafin ta haye cinyarsa tana cewa"morning daddy sabahul khair",murmushi ne sosai dauke a fuskarsa wanda bai bayyanar da haqora yasa hannu ya dagota yana kallonta yace"sabahun nurrrr my lovely khadija"tayi tsalle ta dane cinyarsa abinta tana wasa da maballan gaban rigar baccinsa tana cewa"daddy tunnjiya nazo da daddare kaqi zuwa na ganka" "wonderful,anan kika kwana ke da wa?""ni da anty fadila tare ma yanzu muka taho"ya daga kansa yana nemanta da idanunsa sai dai tuni ta jima a kitchen bata a gun sai salima dake tsaye ta zubawa 'yar tata ido Kallonta take tana jin wani alfahari na shigarta tana godewa Allah da bai bata damar rasata ba,wani dadi ne ke cikata ganin gudan jininta ita da halitta mafi soyuwa a gareta wato Aliyyu salim Abdallah maitama,tabbas iftihal abar alfaharinta ce yarinyar bata debo kammaninta ba ko kusa babu wani abu nata data dauko illa farar fata wadda aliyun ma na da ita,kowa ya ganta ya san jinin su ce family din alhaji salim Abdallah maitama ce jininsu ce Ta dawo daga duniyar tunaninta hadi da miqawa iftihal din hannu alamar ta taho sanda suka hada ido fuskar salima dauke da murmushi,da taga kamar yarinyar bata fahimta ba sai tace"come on baby na come on my dear " yarinyar ta noqe kafada tayi luf jikin mahaifinta kamar mai tsoron ta babu sabo ko kusa tsakaninsu,wani kishi ya kama salima don taga yadda suka shigo da fadila yarinyar a sake take kana ganinsu kasan akwai sabo mai yawa tsakaninsu Ta sake gwada sa'arta ta miqa mata hannunkaro na biyu tana sake cewa"come on mana mai dear kin manta mominki ne iftihal? Me yasa baki zo guna kin kwana ba ina da chocolate da biscuit da yawa da zan baki"ta sake noqe kafada tace "um um nafison na kwana gun anty fadila she's nice like daddy"sai salima ta maida hannunta ta rungume cikin jin haushi Aliyyu na ankare amma yayi kamar baiga abinda ke faruwa ba,sai da yaji tana jan qwafa sannan ya tanka mata"duk uwar da bata yi showing mercy akan yaronta ba tayi abandoning duk wasu duty nata akansa no need to deceive her self akan shi zai iya jin qanta ya kuma ji tausayinta"idanunta sun kada sunyi ja kadan take jira ta fara malalar da hawaye tace"aliyyu abinda ya wuce ya riga ya wuce please"ta juya cikin zafin nama ta bar part din nasa kamar zata rushe da kuka *TUNA BAYA* Aliyyu da salima sunyi aure ne irin auren da zaka iya kiransa na soyayya,karatu shi ya fara fitar da aliyyu india cikin garin mumbai dake qasar india,ya karanci fannin kasuwanci da masana'antu ne tun usulinsa,kusan binda ma ya zaunar da shi kenan a qasar bayan kammala karatunsa kafin daga bisani ya soma kai kawo tsakanin nijeria da indian Tun kafin aliyyu ya kammala degree dinsa na farko yake siyan kaya yana turawa uncle Abba yace a siyar masa tun uncle abban na dariya yana dauka wasa ne abun nasa yakance"alii rigima idan banda abinsa mai ya nema ya rasa da zai takurawa kansa sai ya fara kasuwanci tun kafin ya kammala karatunsa?"shi kama aliyyu ya dage aiko kaya yake tun daga lokacin da uncle abba ya fuskanci son kasuwancin a jininsa yake sai ya qyaleshi ,sai gashi tun kan ya kai ga kammala degree dinsa na biyu ya mallaki kudade masu tarin yawa na qashin kansa tsantsar guminsa,sam yaqi amsar tallafin sisin kwabo dag dukiyar da Allah ya horewa mahaifinsa,kwata kwata aliyyu ba cima zaune bane akwai zuciyar neman na kai tun yana qaraminsa,bai damu da arziqin da mahaifinsa ke da shi ba Wadannan kudade yaci gaba da juyawa har kawo yanzu matsayin da yake kai na mamallakin companies da share shares a gida nijeria da wadansu maqwaftan qasashen,aliyu ya zamo daya daga cikin matasa masu tarin dukiya mutumne shi da Allah bai bashi dagawar son a san wayeshi ba,yasha gayawa abban nasa tun kafin zuwan wannan lokacin shi yafison yasan ya san zafin neman na kai,sai gashi burinsa ya cika don ya tara dukiyar da shi kansa bai sa ran samun kamarta ba,darajar addu'ar mahaifa riqon gaskiya da amana tausayi da taimakon na qasa su suka kaishi ga wannan matsayin da yake kai Haduwar su da salima ta kasance ne sanadiyyar hutun qarshen zangon karatu da daliban instute din pashwar suka samu ciki harda,wadanda ba 'yan qasar ba kuma suke da sha'awar zuwa qasashensu hutu nata shirye shiryen zuwa gidan ciki kuwa harda saliman,wasunsu na ahiga kasuwannin dake cikin mumbai don yiwa yan uwa tsaraba Cikinsu harda salima su hudu ne ita sai wata qawarta 'yar nijeria sa'adiyya abikan karatunta biyu 'yan qasar data nemi rakiyarsu don qasarsu ce sun fita sanin kan farashin kayayyakin shruti da arohi,sun ahiga shagon a sanda aliyyu ke ciki yana zaune kan daya daga cikin kujerun dake ajjiye a shagon suna lissafi ne shi da mai mai shagon kan wasu kaya da aliyyun ya sara a gunsu alokacin tun kafin ya bude kamfaninsa Abu na farko da ya fara kama jan hankalinta game da aliyyun shine baiwar tsantsar kyau da Allah ya bashi da daddadan sauti ,abu na biyu ya bata mamaki jin yadda yake hira tar tar da indiyanci tamkar haifaffen can,tunda suka shigo shagon daga kallon farko na amsa sallama bai sake duban sashin da suke ba ya mai da kai yaci gaba da abinda ya kawoshi shagon Ita din ma azahiri idan ka kalleta sai kayi tsammanin hankalinta bai kansa saidai duk siyayyar da take yi kusan qani abun ma bata san me zatayi da shi ba data dauke shi don hankalinta na kan alin Tuni ya kammala abinda yake yayi sallama da raja ya wuce,sanda yake fita ashagon