← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 84

Sashe 2

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zafi ba"sai kuma ta juya ta koma gunsu sumayya tana bata lbr,ummi ta kalli momy tace"wai iftihal din Aliyu ce wannan?"momi dake tsiyayawa ummi lemo a cup tace"itace mana kinga yadda ta girma ko?"ummi ta jinjina kai tace"ba shakka gata nan kuwa masha Allah,ina zaton ai ba zata wuce shekara bakwai ba ko?"momi tace "idan watan nan ya mutu sabon wata ya kama yakai ashirin zata cika shida",sai bayan sunyi magariba suka fito,tuni iftihal ta maqale wa fadila domin cikin qanqanin lokaci suka saba,don fadila ba daga baya ba gun son yara,bare iftihal yarinya ce kyakkyawa ga wayon tsiya,har bakin mota suka rakosu sumayya na yaba kyawun motocin nasu,fadila tace idan kina so ki amsa mana,sumayya ta kama baki tace rufamin asiri kada kisa yaya aliyu ya babbalani kina ganin abba zai sai mana ma ya hana wai har yanzu bamu da hankali sai randa muka qara nutsuwa?fadila tayi dariya tace "sai kace yau aka haifeku""kema dai kya fada sister cewar rabi'ah,dai dai nan ummi da momi suka qaraso momi ta miqawa fadila baqar leda tace"to ga kayan kwalliyarnan aje ayi tayi ana samo mana sueukai"a kunyace ta amsa tana mata Godiya,momin tace to sai wata shekarar kenan,fadila ta sadda kai qasa tace"a'ah momi insha Allahu zaku dinga ganina"Allah yasa inji momi,ummi tace"wai ni kuwa ina Aliyu ne,na kwana biyu rabon da na ganshi fa"fuskar momi ta canza zuwa yanayin damuwa tace"hmmmm,mtsw,ke dai bari kawai haj kwanan nan zaki jiyomu da shi,Aliyyu fir ya guji aure yaqi fidda mace yayi aure,yafi ganewa kasuwancinsa kawai nayi har na gaji hakanan abbansa kullum zancen kenan amma yaron nan sam yaqi mai dakansa"ummi tace"addu'a kawai zaku ci gaba da yi masa Allah ya kawo ta gari kada a kuma komawa 'yar gidan jiya a bata goma daya bata gyaru ba"momi ta gyada kai tace hakane,Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi"tace amin Daqyar iftihal ta rabu da fadila harsai da ta laluba cikin motarta ta samo mata chaculet sannan ta yarda ta barsu suka tafi,basu tsaya ako ina ba sai a shop rite dake ado bayero mall,ta nufi parking space ta gyara tsayuwar motarta sannan ta kashe,ummi ta zaro kudi cikin jakarta ta miqa mata,tace maza kiyi da jiki ki fito"tasa hannu biyu ta amshi kudin tana qoqarin maida murdin motar ta rufe ne ummi tace"saura ki kwaso kayan zaqi da sanyi ki koma gida ki guji maqiyin naki abinci"tayi murmushi kawai tace baza'a siyo ba ummi ta rufe motar ta shige,cikin nutsuwa take daukar musu abinda tasan suna da buqatarsa ita da farida har ta kammala,har zata nufi kanta ta tuna bata dauki turarenta ba blue lady,cikin sauri ta koma,hankalinta yatafi ga turarurrukan tamkar ance ta kalli gefanta,tsaye yake shima yana zaban nasa kalan,yana sanye cikin shadda dinkin tazarce blue Black ce ta haska farar fatarsa matuqa,ta gefan tana iya hango qaya taccen sajensa dake kwance luf bisa tsararriyar fuskarsa,ga tsinin hancinsa nan yayi das qasan farin qal din glass dake bisa fuskarsa,kyakkyawan idonsa wanda gashin idon suka yiwa rumfa suna juyawa cikin farin glass din nasa yan karanta rubutun dake jikin kwalin turaren,kansa ba hula sai sumarsa dake kwance an dan saisayeta,ya zari turaren kwali uku cikin sassarfa ya juya yabar gun,samun kanta tayi da bin bayansa zuwa inda zai biya kudinsa ,kusan tare suka biya sai dai sam shi bai lura da ita ba ya juya ya fita ta sake bin bayansa,tafiyansa ma abar kallo ce tamkar wani saraki haka yake takawa,daga nesa tadan tsaya a harabar adana motocin don batason ya ganta,cikin aljihunsa yasa hannu ya zaro key ya bude wata baqa sidiq din mota qirar range rover ya shiga yayi mata key ya jata da gudu ya bar gun,jan ajiyar zuciya tayi gamida lumshe idonta hadi da dafe goshinta da tafin hannunta"inna lillahi wa inna ilaihir raji'un allahumma ajirni fi musi bati wa akhlifni khairan minha"abunda take ta nanatawa kenan,wannan wace iriyar musibace zuciyarta ke son jefata ba gaira ba dalili?,ta bude idonta ahankali jikinta ba laka ta soma lalubar inda tayi parking Cikin motar tayi dif zugi da radadi take ji,ba abunda zuciyarta keyi sai zillo cike da dimbin qaunarsa,shi wa?,ita kanta bata sanshi ba,ummi nata mata hira tana cijewa tana amsa mata har suka isa gida,farida na falo ta baje kolin takardu da alama assignment takeyi,batason ta dameta da hira don haka tadan daure fuska,itama faridan data fuskanci hakan bata ce mata komai ba illa sannu da zuwa ya kuka barosu?,ta amsa mata ta haura sama inda dakinsu ita da farida yake,ta watsa siyayyar tasu kan gado zuciyarta cunkushe ta cire kayan jikinta ta fada toilet da niyyar sakarwa kanta ruwa ko zataji sanyin zuciyarta Muje zuwa S.A.M huguma [10/16, 12:19 PM] Salma WA YASAN GOBE? SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Lotion kawai ta shafa bayan ta fito ta feshe jikinta da body spray ta lalubi rigar bacci doguwa har qaurinta ta zura don bacci take da muradin yi, ta daura zani a sama ta sanya hijabin sallarta ta gabatar da sallar isha'i, ta dora da shafa'i da wutiri, bayan ta shafa addu'o'inta tabi lafiyar gado, a maimakon bacci yazo mata sai tunani ya mamaye gurbinsa, ba zato ta tsinci kanta da zubarwa kanta da kanta hawaye na tsananin tausayin kanta, a cikin jikinta da zuciyarta take jin ta shiga halin tsaka mai wuya, zuciyarta na bulayi da lalube cikin duhun son wanda bai ma san tana yi ba, farida ta shigo dakin hade da sallama hakan ya sanyata saka hannu tana goge hawayen cikin dabara don bata son faridan ta gani, faridan tadan kalleta jikinta yaso ya bata tamkar yar uwarta na cikin damuwa, don haka jikinta sai ya danyi sanyi ta shigo ne da niyyar tsokana don flask guda ummi ta ciko da abinci tace kada ta sauko da shi sai ta cinye Farida ta ajjiye flask din a gefan gadon ta janyo dressing chair ta zauna tana fuskantar fadilan tace"sister lafiya naga kamar fuskarki ta nuna kamar kina cikin damuwa? ,ta qaqalo murmushi sannan tace"ba abunda ke damuna just na gajine fitar nan da nayi"farida ta girgiza kai ba don ta yarda ba tace"ok,to ga abincin ki nan ,ummi tace " kada ki sauko mata da shi sai kin cinye tana daga kwancen ta zubawa flask din ido tace"har gabana ya fadi wlh, ina zan kai wannan abincin? ,farida ta qyalqyale da dariya tace"ni dai yar aikece kuma na isar da saqo,qafafunta tayi saman tiles din daya mamaye da qaton dakin nata Ta daura zani a sama ta sanya hijabin sallarta ta zari flask din, farida ta kalleta tace " a'ah ina zuwa? "Ba tare data kalleta ba ta juya tana shirin fita sannan tace"jirani ina zuwa"farida ta bita da kallo tana dariya ciki ciki ,ta qofar baya fadila ta fita ta bulla bakin get din gidan,kai tsaye ta nufi gun idi mai gadinsu, mutuminta ne dama da hangota kuwa ya miqe yana cewa " uwar dakina"miqa masa flask din tayi tace"yi sauri ka juye idi"cikin qanqanin lokaci kuwa ya juye abincin ya bata flask din yana zuba godiya Ta tarar da fadila na waya da alama da saurayinta take, ta koma gefan gadon ta zauna tana kallon faridan har ta kammala tsaki fadilan tayi, farida tayi murmushi tana kallon flask din da fadila ta dawo dashi don tasan kwanan zancan, bata son idan zatayi waya tayi mata a dakinta,fadila ta harareta tace"bana gaya miki ki daina shigomin daki idan zaki shirmen wayarki ba? ,tace tana gyara kwanciyarta akan sofa qwaya daya dake dakin " sorry anty na"tana dan murmushi tace kiyi haquri Tun bakwai na safe take a kitchen dama haka al'adarta take, idan bata da lecture to Itace mai shirya musu breakfast haka da rana ko da daddare,girki yana daya daga cikin hobby dinta hakan ya sanya ta zama gwana ta fannin abubuwan ci da na sha, Awa daya da rabi ta kammala komai ta koma dakinta tayi wanka ta shirya kasancewar tara da rabi tana da lacture,dakin ummi ta shiga bata nan sai muhammad ta tarar yana kan gadonta yana bacci,dala masa duka tayi tace"tashi malalacin banza eight thirty amma kana bacci ina school din?"cikin magagin bacci yake murza ido yace"wlh nayi wanka bacci ne ya daukeni"tace"oya tashi ka shirya idan zan wuce na sauke ka na baka eight minute"da sauri kuwa ya duro daga kan gadon ya shige toilet Bangaren abbansu ta wuce tare da diba masa breakfast dinsa ta tafi masa da shi,yana zaune kan kafet din falon hannunsa dauke da jaridar daily trust,haka yake a al'adarsa bayan ya dawo a masallaci yakan yi azkar da tilawar qur'ani idan gari ya dan sha kuma sai ya karanta jarida kafin ya fita aiki,fadila ta shigo da sallama, ya masa yana dubanta fuskarsa dauke da murmushi,ta dire kayan abincin ta rusuna tana gaidashi ya amsa yana fadada fara'ar shi yace"sannu fadila da qoqari hala yauma anada da lacture din safen"kanta a sunkuye tana qoqarin hada masa kunun shinkafa da yasha madara tace"eh Abba",ummi ce ta fito daga bedroom din Abban hannunta dauke da doster da alama goge goge ta gama,fadila ta gaidata tana qoqarin tashi tace"abba zan tafi"ya dubeta sannan yace"ai banga kin ci komai ba haka zaki tafi?""abba zan karya a capteria idan na.......... Ummi tayi saurin katse ta da cewa"yi mana shiru wlh abbansu idan taje ma bacin take ba farida ai ta gaya min wai ba zata iya cin abinci a waje ba,wannan yarinya na rasa meke damunki anya lafiyarki qalau kuwa?",abban yayi murmushi yana dakatar da ita"dakata umminsu,fadila lafiyar ta qalau,kin manta yawon asibitin da muka dinga yi da ita tun tana qarama?,haka dai halittarta take"ya juya ga fadila yana tura mata cup din da ta hada masa kunun yace"maza zauna kici wani abu kada ki qara bata ran umminki kinji ko?"tamkar zata sa kuka ta zauna tana cewa"to abba"yaci gaba da cewa"gashinan fadila tafiki abin arziqi shi yasa ta rainaki tana ganin kanku daya,ummin tace sai rawar kai da gwanintar yin girkin amma saidai wasu su ci mata,abban yayi murmushi yana kallon yadda take tura abincin kamar magani Kafin ta kammala muhammad ya shigo don haka abban ya sallamesu suka fita tare,suna mota muhammad ya dameta da surutu,ta daga masa hannu hadi da cewa kaga malam bafa aku na dauko ba idan kuma kai aku ne
Chapter 2 · 0% Book details