← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 84

Sashe 27

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ado da kwalliya zata yi wankanta tayi kwalliyarta hakanan zata qoqarta ta dafa masa koda jallop ce albarkacin masifar son sa da take duk da bata taba girki a gidansu ,amma samira kuwa babu daya qanwar biyu daga ciki Cikin harshensa da zuciyarsa yana jin dadin girkinta sosai dandanon da bai taba jinsa ba gun kowa ba baya ga mominsa,miskilanci irin nasa yasa ko a fuska bata taba ganin alamun haka ba,takan tattare masa socks singlet handkerchief three quarters da duk inner wears dinsa harda jallabiyoyinsa da yake sawa ta wanke su tas ta goge su sannan ta feshe su ta turare ta jera masa su to ammafa insha Allahu bayan kwana hudu ta karbi girki zata zo ta tarar da su kamar kamar ba su ba komai an hargitsa shi sai ta soma fuskantar wani abu akwai gayya a ciki ta kuma san bazai wuce su salima ba don adawarsu gane da aikin nata a fili yake qara ra wani lokacin takan jiyosu suna yan qana nan maganganu takan sharesu taqi tankawa don basu tari gabanta sun gaya mata ba bare ta kula da shashancinsu Abu daya ke qona mata rai aishi aliyyun na gani suke batawar shin bazai tsawatar musu ba idan su basu da tunani? Ga misali a farkon fara aikin nata kafin su soma adawarsu takan tsince kayan aliyyu ne kawai a dakin a watse takan gyara ba tare da ta damu ba tunda tasan aikin ta ne dama,da tafiya ta soma nisa sai suka dinga barin brassiere panties sleeping dress underwear musamman salima wadda kullum sai ta tsince nata tunda samira ke fara girki sai ita wanda a qa'ida fadila ce ya kamata ta zamo mai girki a farko amma suka maida ita ta qarshe ta qyalesu duka ta zuba musu ido ,tasan da gayya take zub da kayan,zuciyar fadil na matuqar baci da hakan,a duk lokacin da ta tsinci kayan takan bata lokaci mai yawa tana qissima dalilin barin kayan daga jikin mai su wanda hakan ke qara ta'azzara kishinta ga aliyyu Wani sabon rainin hankalin kuma sai ta fuskanci ya shigo ta soma gyaran sai ta shigo tace" sorry fa don Allah,jiya na mance kayana akan gado wallahi dear ne ya rudani daren jiya shi yasa da safe na manta da su ban dauka ba,kinsan shi akawai nacin abun,sai dai fa ba sauqi shima fa gwani ne "wannan ya bata ranta fiye da abinda tayi mata,har ta soma hasashem anya basu da masaniyar babu abinda ya taba gilmawa tsakaninsu? Akwai lokacin da ta zube har da magungunan mata maau dauke da hotunan banza,wannan fadila maganinta tayi ta dauko mata wasu wanda wata maqociyarsu a acan gida ta bata ita basonsu take bame ma zatayi da su tunda ta bata ta jawo locker ta watsasu sai yau ta tuna da su ta qara mata tace ga wasu sai ki qara naga naki basu kai wadanan tsada ba ni kinsan bana amfani da su halitta ta bata buqatarsu komai nawa yaji ba sai da kwaskwarima ba"jiki a salube ta karba duk da bata nuna mata hakan ba,ai kuwa da ta karanta kwalin sai taga tabbas sun fi nata kyau to tun daga ranar bata sake bari ba samira nata rashin mutuncin yafi ysakanin falo da kitchen parlour zuwa kitchen,zata dauko plates ne kofuna ne da su spoon tayi ta batawa wani abun plate din ma leda ce ta chewing gum ko biscuit zata dora akai kuma ta barshi a nan tunda ta sani cewa babu mai aikin gyara gun sai fadilan,duk da wannan neman masifa da suke ba wadda ta isheta kallo a cikinsu Su kansun so suke ta kulasun amma ta qi basu wannan dama Mrs muhammad 01:18 pm 05/11/1437 *wa yasan gobe?* Lahadi daya daga cikin ranakun qarshen mako ne wanda yake zama ranar hutu ga ma'aikata to haka ne ya zama ga fadila hutun ya zame mata double babu zuwa office kuma bata da girki,la'asar sakaliya ta ranar ta shirya tsaf cikin doguwar riga shigar da tafi so kenan ta material ce ruwan qwaiduwar qwai dinkin rigar ya bude sosai dga qasa an mata dogon hannu tayi rolling dinta kamar yadda ta saba da jan mayafi,takddunta ta diba na aikin office da takeson dubawa zata yi wani aiki a kansu ta dauki yar madaidaiciyar dadduma da daya daga cikin matashin kujerarta ta zira takalminta ta firo harabar gidan,sai ta tarar da saluma da samira zaune kowacce a harabar sashenta bisa farar kujera plastic,novel a hannun salima samira kuma na riqe da wayarta tana tana ta faman danne danne,tun kafin fadila ta kai ga zama ta fuskanci zaman nasu ba na Allah da annabi bane don kuwa taba fitowa ta fara cin karo da baqaqen maganganun da auke jifan juna da shi a fakaice ba tare da kowa ya kalli dan uwansa ba kamar ta koma ciki sai kuma ta duba agogon wayarta taga biyar harda rabi da minti uku bata da wani lokaci na duba takadddun idan ba yanzu ba cikin gidan kuma zafi yayi yawa sanadiyyar hadarin da keta hadowa ana yin yayyafi dan kadan wanda ke qara tada zafin garin,ga injinsu yayi tsiya yaqi tashi tun wajen uku bakaniken ke kansa yana fama da shi kasancewar ba dan qarami bane yana daukar dukka freezers dinsu heater a.c da sauransu sun riga sun saba da wuta ko yaushe 24 hours,sai kuma ta ahimfida dardumarta cikin ranta tana fadin _ina ruwan biri da gada?_,tayi bismillah ta zauna ta soma aikinta,ashe duk suna ankare da ita,minti goma bai cika ba da zaman nata samira ta soma receiving call "shegiya kina duniya?......heeeee wlh gamu a cikinsa muna gogawa.......hahahahahaha aike kinsan fa hali tun ba yau ba"ta danyi shiru sanna ta sake kecewa da dariya kamar wani gardi tace"a haba haba ke sai kace ba nice samira ba?.....k kinsan saidai a gaji aqyale mana,kowacce qaramar shegiya sai ta kama gabanta da qafafunta ,salima ta bude shafin gaba na littafin dake hannunta tamkar da gsken karatun take tace"qaramin dan iska ma yaci uwatar ai yasan kansa,samira ta sake kecewa da dariya "wlh har mai share share da goge goge ita wannan ai ba wahala zata bani ba.....yo hannatu yar anacen ma ba komai bace a guna wallahi duk hasashen da take na ita wata ce a gunsa Sarai fadila ta san da ita take amma sai taga ba mutuncinta bane tsayawa tana cece kuce da wadda batasan ciwo mutunci da kuma darajar kanta ba ,kan ta qare wannan tunani sai ji tayi tas! Da sauri ta dago idanunta don ganewa kanta wanda ka zubawa wannan lafiyayyen marin,aikin salima ne tana tsaye a gaban samiran bayan ta kwasheta da marin tana huci,tuni samira ta katse wayar hannunta na kan kumatunta ta miqe tsaye salima ta dora mata da bayani shiru shirun da kike ganin ina miki ba fa tsoronki nake ba ki bar ganin kina min kina samun nasara wallahi kin kaini bango nifa ba sa'ar yinki bace don uwarki"tasa yatsanta tan nuna qirjinta tana cewa"ni kika mara?" an marekin kadan ma kika gani wata rana zaki ga abinda yafi marin ma,kina tsammaninke ka aice tantiriyar karuwa ko? nima karuwace nayi nayi kuma yaqon duniya fiye da naki ke da kika local ma mamaki da tsoro suka kama fadiladama har akwai abun tutiya gun mace don tayi yawon karuwanci?wannan wane irin zama nine da Allah ya kwom da har karuwanci ya zama abun ado?ita takaici ma sai ya sata ta maida kanta kanrubuce rubucenta taqi kola kowaccensu tana jinsu cacar baki mai zafi ta barke tsakaninsu tamkar zasu cinye junansu Duf taji gun yayi shiru kamar an sanya musu kwado a baki ,ta dago da hazari don ganin mai ya sanya su yin shirun ba tare da kowa ya raba su ba?,aliyyu ne ashe ya ahigo kuma baau ankara da shigowar tasa ba sai da ssuka soma daga hannu da niyyar kaiwa juna duka ,kowaccensu tayi sak saluma ce ta fara cewa wallahi tallahi ban kulata ba itace ta fara takalatakuma ka tambayi fadila"jin sun sanyo sunanta cikin sha'aninsu ya sanyata azamar taahi ta soma linke sallayarta,daidai lokacin da ya kai dubansa gun da fadilan take da salimar ke nuna masa,ga mamakinsa tana gama ninke sallayar a nutse ta duqa ta mwaahe takardunta ta juya ta shige sashen nata ba tare da ta kalli ko da daya daga cikinsu ba cikinsu ba sai aliyyu ya bita da.kallo karon farko wani abu daga garet ya fara burgeshi nutsuwarta ,sai da ta shige ta kulle qofarta sannan ya dawo da idonsa kansu tuni samira har ta gudu ta rufe itama qocarta cike da fargaba da tsoron fushin Aliyyu a akanta don ta tabbatar In dai ya bincika ya tarar bata da gaskiya to la shakka fa kashinta ya bushe,ta ruwan sanyi yake ma hukuncin da zaka raina kank babu duka ba z gi b baqar magana,ya juyo ya dubi saluma da jikinta ke rawa sai kawai shima ya gewayeta ya shige nasa part din Kwana uku tsakaniya kamaqarshen wata ne,kamar yadda ya zama al'adar gidan fita aiy yya a i in lokacin don sabunta abu uwan buqata na amfanin yau da kullum Yaune za auyi fitar farko tun bayan dawowar salima gidan gidan Fadila ta shiryq cikin shigarta ta bare bari tana nannade cikin lafayarta ,ta kammal komai ta kira umminta don su gaisa,hira suke sosai ta ji o tashin horn ta tabbatar aliyyu ne don bai son jira kuma baya jira saboda haka shima bai bari a jirashi tayi saurin maqale wayar a kafada tan ci gaba da hirarta da ummin tasa daya hannunta dauki jakarta ta sa m y ta kulle sashin,ta qarasa jikin motar tana sallama da ummin ta ciro wayar daga kafadarta tana kashewa sai ga salima da samira tamakar an jehosu kowacce na qoqarin bude gidan gana ta shige don badon fadila tayi azamar matsawa ba da daita zasu yi awon gaba,ta rufe bakinta da tafin hannunta dariya na shirin subuce mata ,cikin zuciyarta tana cewa sunan wani film *qauyawa* Allah kayi mana magani wannan ai kishin jahiliyya ne Ku biyo *mrs muhammad* [10/16, 12:41 PM] Salma *wa yasan gobe?* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* Allah ya sawwaqe tace,ta bude gidan baya ta shiga tana kallon drama,aliyu ne ya juyo don ganin meke
Chapter 27 · 0% Book details