Sashe 16
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bulbule jiki da shi tana taunar chewing gum qas qas qas, tana wani ya tsina fuska tace sweet yace ki fito zamu siyayya,fadila tace waye sweet kuma?,ta wani juya ido tace my aly, Tabe baki fadila tayi tave kice bani buqatar komai,bata jira cewarta ba taja qofarta ta rufe,wani kishi ne ya motsa mata ita kanta tasan tana da tsananin kishin aliyunta amma ya ta iya?,ta jiyo muryar samirah na masifa"aikin banza wa ma ya damu da ke ?kada Allah ubangiji yasa ki je din dama sho ya takura ayi kiranki waishi mai adalci toga abinda ya jawo mana nan wulaqanci agun wadda bata isa ba"fadila dai murmuahin uaqe tayi wanda akace yafi kuka ciwo,ta dauki plate dinta taci gaba da cin fruit din ta ba tare da tana jin dadinsu ba kamar da Knocking ta sake ji ana mata ta maida plate din kitchen sannan tazo ta bude yana tsaye a bakin qofar hannayensa zube cikin aljihun jeans dinsa fuskarnan kamar hadarin dake shirin zub da ruwa ba tare da ya dubeta ba ya kalli agogon hannunsa kana yace"nan da minti biyar ki sameni a mota,abindabya fada kenan ya juya yayi tafiyarsa,cikin qanqanin lokacin kuwa ta shirya kasancewar ita dama koda yaushe bata taba yarda ta zauna babu wanke bare uwa uba qamshi da yariga ya kama jikinta kida muwa bata sanya turare ba,shigar doguwar riga abaya tayi baqa wuluk mai sheqi saqar qasar dubai an mata ado da dutsuna masu kalan sararin samaniya(sky blue)rigar tayi bala'in amsarta musamman da tayi rollinga da wani dankwali madaidaici shima sky blue ta nannde gashinta tayi acuci da shi,ta saka zobe qwaya biyu a yatsunta na tsakiyar hannu plate din takalmi ta saka baqine mai light blue din igiyoyi,ba wani make up tayi ba hodace kawai da weet lips amma kada kaso kaga kyawun da tayi kamar wata baqar balarabiya kasancewarta mai zagayayyar fuska da cikakken gshin gira ga yalwar sumar kai wadda ta bayyana har a gaban goshinta Suna zaune shi da aamirah cikin motar tana ta faman mitan dole wai sai da gadilan za'a tafi ne ya daga mata hannu fuska ba walwala kamar kullum yace"ya isa fa mitarki tayi yawa,for god sake,zaki taimakeni ranar da na tashi barin jiki na ashanye?,anje da ita kamar yadda kaje da ke ruwanta ne ta siyi abinda take ruwanta ne ta barshi fine an fita haqqinta,cikin salon jan hankalinsa tace da tuni ni kadaice taka sweet,an tashi an.manna maka wannan baqar yarinyar,wani kallo ya sakar mata wanda ya tilasta mata tsuke bakinta don kuskuren da taso tafkawa,baya ga haka ma aliyu shi tun usulinsa bai iya yi da mutum ba gaskiya daya ce zai fade ta ne agaban mutumin koda zai mutu ko zai kasheshi Sukayi tsai suna sauraron isowarta aliyu nebya faa hangota ya glass din gefansa,sai ya samu kansa da qarewa shigarta kallo tabbas tana da kyau babban abun ma iya dressing na nutsuwa bana hauka ba fuskarta babu tarin kwalliya irinta ta samira hakanan babu qamshin turare har sai da ta ahigo motar gidan baya ta zauna sannan yaji nata qamshin,shigar tadauki hankalin samirah tamkar ta fito itama ta canza irinta haka ta ji tunda ita fara ce ai zata fi karbarta haka ta gani,amma a fili sai ta wani tsaki,aliyu ya tashi motar ya yi ribas ya nufi get tun kafin yayi horn salisu mai gadin ya dage grmet din gidan nasiru da suke zaune tare da slisun ya taso ya iso saitin da aliyu yake ya fan ranqwafa yace yallabai kai kadai yau zaka fita,ya girgiza kai ina tare da matan gidan ne,nasirun ya dan sake ranqwafawa yace barkanku da dare hajiya an quni lpy,fadila ce kawai ta amsa samirah kam dauke kai tayi kamar batasan yana yi ba takaici ke cin ranta da dab banzan kishi sai tayi banza da shi Aliyu ya qare maganar da suke yi da shi da"sai na dawo kaima zaka iya wucewa gida sai gobe insha Allah"nasiru ya dan ja baya yana cewa to yallabai a dawo lpy Allah ya tsare,har ya saoma jan motar ya tsaya ya dannawa nasiru horn ya dawo da sauri yace masa"nasiru kayi qoqarifa gobe ka fita da wuri ka fara zuwa gunsu haruna ka b tabbata a gobe an gama sa kayan duka cikin store qarfe sha biyu zan qaraso insha Allah ,yace to da yarda Allah goben za'a kammala,aliyu yace sai ka wuce gida ka kwanta da wuri don ka samu tashi da wuri Allah ya bamu alkhairi,ya ja motar suka fice Yanayin tuqinsa salon da fadila bataso ne sau tari sukanyi fada da frida akan haka wato gudun tsiya ne da su,ya iya gudu da keta motoci,motar ta dauki shiru sai sanyin raba dake ratsa kowanansu kowa kuma da abinda zuciyarsa ke saqa masa,a sace fadila ke kallon aliyu ta mirror,fuskar nan ahade tan shaqar qamshin turarensa na chastity sai ta kasa dauke idonta a kansa sonsa na mamayarta,ji take tamkar ta kamoshi ta rungumeshi a qirjinta ko zaiji yadda zuciyarta ke bugawa saboda shi ya tausaya mata,a yanzu ba abinda tane buqata illa soyayyarsa,tana ji ne kamar ta furta masa abinda ke danqare a a zuciyarta ,don kanta ta dauke idonta tana sauke boyayyar ajiyar zuciya Tafiyar mintina qalilan suka isa katafaren kantinnan na shoprite,ya dauki wayarsa iPhone 6 yayi yan danne danne sannan yayi kira da bai wuce na second goma ba ya maida wayar gefensa ya kashe motar minti ashirin na bayar kada kuma a wuce haka,samirah tace cikin murmushi"ok sweet"ya maida mata da cewa"ok dear"wani dadi ya rufe samiran kamar ta taka rawa domin ta dade bata samu hakam daga gareshi ba duk da tsan ba laifinsa bane ita ta barar da damarta,ta kama hannunsa ta masa kiss sannan ta fice,abinda bata sani ba tuni fadilan ma ta rigata ficewa Ta kwashi kusan minti goma bata dauki komai ba tana zaune duniyar tunani sai da taga giftawar samiran a inda take sannan ta ankara ta miqe,wani abu ya darsu a zuciyarta,nana da nan ta soma zabar vest ta maza cotton fala qal mai kyau da taushi ta dauki gajerun wanduna dozen sai hand kerchief dozen agoguna na kamfanin gucci uku azurfa biyu takalma hudu budaddu biyu rufaffu biyu sai turarurruka na kamfanin rasasi sai rezar aski ta maza tare da shaving cream na nair,ta daukarwa kanta turaren blue lady sai relaxer,sannan ta amshi mutuminta wato ice cream manya robobi guda hudu,leda biyu aka mata kayan sai tata ledar ta tashi shafal babu wani abun kirki da ta dauka,kayan basu da wani nauyi don haka da kanta ta dauka ta fito,tana kusantar motar gabantana dada faduwa bata ga alamun samira ta dawo ba don haka ta iso motar ta sanya hannu ta bude gidan baya ta zuba ledojin hannunta sam sai ta kasa zama cikin mitar kasancewar aliyun na ciki don haka sai ta tsaya jikin motar ta jingina da ita ta harde hannayanata bisa qirjita tana bin harabar gun da kallo gamida qare masa nazari na yadda matasan yan birni maza da mata keta kara kainar shigowa gun da motocinsu Sai fadila ta soma qosawa da tsaiwar gun ganin yadda duk naminin da zai gifta sai ya zuba mata idonsa,taja tsaki tana jin takaicin matsanancin kallo irin na waau mazan,kamar daga sama ta jiyo dakakkiyar muryar Aliyu yana cewa"malama koma.mota ki zauna tun ke bakisan me ya dace ba" a sanyaye ta juya ba tare da ta kalleshi ba ta shige cikin motar zuciyarta na mata quna da jajen yadda aliyu ke mata mu'amala tqmkar wata mara rai kunnuwanta basu taba jiyo mata kyakkyawar kalma daga bakin aliyu ba akanta,zuciyarta ta fara tafasa saidai ta danne bacin ran nata da kiran sunayen Allah,dama ta tsammaci fiye da haka ma daga gurinsa A hankali ta soma jiyo maganganun aliyu dake tsaye jikin mota sai ta tsinci kanta da kasa kunnuwanta cikin qaqanin lokaci ta fuskanci da mace yake hirar,kai tsaye ba zata fassara hirar data soyayya ba amma zaka fuskanci cewa akwai alaqa tsakaninsu ,mai da bayanta kawai tayi ta jingina da makarin kujerar ta lumshe ido tana sauraron bugun da zuciyarta keyi ta dauki tsaqon mintina a haka ba tare da ta tantance halin dabm take ciki ba sai da aka gama zubawa samirah siyayyarta a but qarar rufe buut dinne ya dawo da ita duniyar data Lula Muryar samira ta karade gun cikin tuhumar aliyu da wace yake waya cikin rashin ladabi bai kulata ba sai da ya gama wayarsa tsab yayi sallama dabwadda yake wayar ya kashe bai ko kalleta ba ya bide side dinsa ya shiga itama cikin sauri ta zagayo tana huci ta shiga itama ta bame qofar yana yiwa motar key ta sake jaddada masa tambayarta "na ce ma da wakake waya?"aliyu bai iya qarya ba don haka kansa tsaye ba tare da shayin komai ba yace"da maman iftihal kin gane?"ba samira da tayi tambayar ba hatta fadila da amsar ta daketa,samira ta hadiye abinda ya taso mata don bin qwaqqwafi ta sake jeho masa wata tambayar daidai sanda motar ta saitu akan kwalta"ro mw kake nufi da yin magana da ita gidanka take nufin dawowa koko ya aka soma?""duk yadda ta kama haka za'ayi"ya mayar mata kansa na kallon kwalta,saiga samirah ta dora hannu aka tana shirin zunduma ihu ,da sauri aliyu ya sauka gefan kwalta ya taka birki yace"bari na sauke ki idan kin gama ihun saiki tari mota ki biyo ni tunda lasheki nayi ko kuma satoki nayi"ba tare da ta sauke hannun ba ta hau maganganu bai kulata ba ya figi motar ya koma hanya,fadila kam na baya ji take kamar babu jini a jikinta babu abinfa kunnanata da qwaqwalwarta ke ganewa har suka iso gida ita dai taga ficewar samirah fit kamar walqiya bata ma jira motar ta gaa parking ba don saura kadan ta fadi,ita kam bata da kuzarin yin hakan don haka ta jawo ledar da ta yiwa kanta siyayya tabar wadda ta masa,ta fara tafiya ta jiyo maganar sa abayanta yana tambayar ledar meye ta bari?ta sadda kai qasa cikim sanyin murya tace kayanka ne,ya sake damqe rai yacekayana?na sanar da ke ne ina da buqatarsu?"dum dum taji atsakiyar kanta wadda tamkar an buga mata guduma a tsakiyar kanta taji,batasan sanda ta isa sashenta ba ita dai