← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 84

Sashe 64

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta gama kashe masa jiki da qwayoyin sonta da bai taba tsammanin akwai kalarsu a duniyarmu ba,banda time to time yana ganinta da yana tsammanin tuni ya dade da zaucewa,yana tare da ragowar matansa amma ita yake gani,zaici abinci amma sai ua bude hotonta cikin wayarsaa fakaice yana kalla ko da su salima na gun sanna zai samu ya iya ci A yau dai yaci alwashin ba zaya qyaleta ba sai yaji ta bakinta,bazai barta ba sai anyita ta qare,ya jawo daya kujerar ya zauna a gabanta gwiwarsa na manne da tata,yayi mata kane kane ya hanata ta ko motsa duk lokacin da tayi yunquri sai ya maidata ya zaunar,idanunsa sun kada jajur "I promised ko da yau zamu kwana anan indai bakice komai ba na shiryawa hakan,ni ko ke babu inda wani zaya motsa,u stole my happiness any moment in my life am feeling am lonely,ina jin na rasa komai na rayuwata,why me yasa ba zaki yafemin ba?" "Na sani I let you down,I made you frown,na sani I dont deserve forgiveness,but I want you to see the depth in my apology just listen to mu heart,it has been torn apart broken,but it still beats for you,ina sonki fadeelah ina sonki!!!..... "Baka sona! stop saying it aliyyu,already ka riga ka gayamin *baka sona baza ka soni ba ko anan gaba kada nayi tsammanin zaka soni*,ka manta aliyu?..ka manta?,duk wanda yace baya sonka da safe ya dawo da yamma yace yana sonka he does not mean what he said,yana nufin wani abu ne na daban ba son ka ba Sak yayi yana kallonta,bai taba tsammanin tana da baki har haka ba,but....at least yaji dadi...yaji dadi da yau ta bakinta ya gaya masa wani abu da ta qunshe cikin zuciyarta game da shi,don haka yana ganin dama ce ta samu gareshi,hannayenta ya kamo tana qoqarin zamewa,hakan bai dameshi ba ya riqe hannayen qam qam, "duk abinda kike tuhumata da shi na amince na aikata din,annabimmu ya umarcemu muyi soyayya saisa saisa don zata iya juyewa qiyayya,hakanan ya umarcemu da kada mu zafafa qiyayya don wata rana zata iya zama soyayya,na mance da hakan,na tozarta kyautar da iyayena suka min shi yasa yanzu Allah ke mani hukunci,na manta da cewa *babu wanda yasan gobe sai Allah*,but now fadeelah I identified my mistake,I made so many mistaken,sai dai ki zama mai afuwa yafiya rangwami da sassauci" ta sake zame hannayen nata da sauri ya kama su "I love you.....I love you" "nooooo!" Ta fadi hawaye na zirya a kumatunta, "baka sona aliyyu....bani kake so ba jikina kake soo.....don me yasa da can baka kusance ni ba sai da nayi amfani da wani abun?,don me yasa baka soni ba sai da ka kusanceni?,ina buqatar amsoshin wadan nan tambayoyin aliyu!"ta qarasa fada a dan tsawace wadda kanta bata san ta iya ta ba balle aliyyu da ya zuba mata ido hadi da sakin hannayen ta ba tare da ya sani ba Kafin yace komai akayi knocking qofar ana fadin "yau kuma me muka samu a office din namu anty fadila ta rufe mana qofa?"cewar fauziyya da yarinyarta dake tayata knocking qofar,kasa motsi fadilan tayi koda na yunqurin goge hawayen ta ne,cikin rashin kuzari ya isa ga qofar ya bude,fauziyya ta kalli fadila da aliyyun tana son tuna inda tasan fuskar,sai ta saki murmushi tana komawa baya "oh...sorry na katse ku ko?,ku gafarceni"ta juya zata wuce tana murmushi"anty fadeelah iman tace a rage kukan nan,duk da ta sani na soyayya ne"aliyu baisan sanda yace "baiwar Allah....don Allah sai ya zama laifi don mutum na tsananin aon matarsa?,don kawai......... Zumbur tayi tace"ni din ma bance laifi bane"fadilan ta katse shi da sauri,dariya fauziyya ta sake yi ta gyada kai bayan ta gama qare musu kallo"wow,salonsoyayyarku abun sha'awa ne,ya burgeni hakan,well.....koma dai mene ne naga zallar son junanku cikin qwayar idanunku,Allah ya bar soyayya"tayi gaba ta kama hannun iman da tuni tayi gabanta tana ta tsalle tsallenta,ta nufi ofishin da zata kai aikin da taje yi A sanyaye ya koma gabanta ya tsaya ya zubawa qasan office din ido wanda ke shimfide da terrazzo,a hankali ya saki hannayen nasa,ya tsugunna a gabanta tamkar mai kama ruwa ta yadda zai iya gano fuskarta sosai don kuwa kanta na duqe tana sharar qwalla,"fadeelah" shiru tayi ya sake cewa "fadeelah kin daina sona?" Nan ma shiru "fadeelah kin daina qaunata ko?!" Ya fada cikin dan fusata,a zafafe itama ta mayar masa "amsa kake so kaji?"daga girarsa yayi idanunsa na kanta"yes!" "Na daina sonka bana sonka,kai ada din ma ba sonka nake ba,ban fahimta bane sai yanzu!" Ta fada kanta tsaye ba tare da kawaici ba,lumshe idanunsa yayi yana jin radadin saukar kalaman cikin kunnuwansa kamar ana soka masa mashi,kusan wannan itace kalma mafi muni da yaji wadda ya jima baiji irinta ba,mace ta farko da zuciyarsa ta soma so don radin kanta ta kuma yi mata wani irin kyakkyawar masauki can cikinta tunda Allah ya ginata,irin masaukim da bai taba budewa wata mace koda bakin qofarsa...yau ita ke furata bata sonsa,kalmar da tunda yaje babu wata 'ya mace da ta taba furta masa ita sai ita din,wani daci na kalmar qiyayya da aka gaya masa ke ratsa zuciyarsa Sai yaga bashi da wani mataki da zai dauka saboda haka itama ta dandani makamancin wannan dacin koma wanda ya fishi,saidai yana son tabbatatwa da kansa da gaskene bata sonsa?,ya bude idanunsa ya zubesu fes a kanta har yanzu kanta na qasa tana share qwalla,"fadeelah!" Ya kirata cikin wata iriyar murya,bata amsa ba hakanan bata kalleshi ba,ta sani babu abunda bai so irin shirun nata "fadeeelahhhh!"ya fada cikim qaraji,bata sanda ta dago kai suka hada ido ba,da sauri tayk qoqarin maida kan nata amma sai ya fita hanzari,da sauri ya riqe habarta ya dago kan nata........ *note*:don Allah masu caccanza numbers na novel dina na roqeku ku daina ,sai nayi typing sai acanza tsarin number a dinga rikitarmin da makaranta na to gaskiya bana so,idan kuma aka ci gaba to ba shakka zanyi Allah ya isa,sannan na samu wata kuma tana samin number din wayarta cikin typing dina,to itama na roqeta ta bari,idan bata ji ba zan kai qararta gurin Allah,don kuwa yana gaggawar amsa addu'ar wanda aka zalunta,ku barmin novel dina yadda na tsara,kuma kuyi naku ba wanda ya hanaku,Allah yasa mu dace *Mrs muhammad ce* [10/16, 2:13 PM] Salma *WA YASAN GOBE?....* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 3* Da sauri ya riqe habarta ya dago kanta,"ki kalli qwayar idona ki gaya min baki sona,I promised zan bace daga rayuwarki kamar yadda kikamin alqawari kema!" Ta sani qwarai aliyyun kaifi daya ne,yana aikata duk abinda ya furta komai tsananinsa,tashin hankali da tsantsar rigima da take hangowa yanzun a qwayar idanun aliyyun ba kadan bane,ko bama haka din ba tana jin ko kanta za'a sanya gabas a dora mata wuqa ba zata iya kallon qwayar idanunsa tace bata sonshi ba,ita kanta ma tasan ta yima kanta qarya koda ta fadi hakan,wannan ma wasa ne Ko motsi kasawa tayi don tasan abinda yake buqata din ba qaramin girma ke da shi ba a gunta, "uhummm.....am waiting,tell me fadeelah.....tell me baki sona kamar yadda kika fada dazun"shirun dai ta kuma yi din bata da abun cewa,yasa yatsunsa ya sake dago fuskarta ta sosai still dai taqi yarda su hada idanun"fadeelah ni na sani kina sona,kina qaunata,amma me yasa ba zaki yafe min ba?me yasa ba zaki manta komai ba?,if u are nt willing to forgive someone,then you don't truly love them,fadeelah silence the mind and hear the heart,ina sonki fadeelah ina sonki har bansan adadi ba"cikin murya dake nuna alamun karaya ta dago kan nata ba tare da ta dubeshi ba ta dawo da tambayarta ta dazu "na gaya ma baka sona aliyu jikina kake so!" Cikin rudu ya sake kamo hannayen nata da ta sabule ya riqe gam "wa ya gaya miki hakane fadeelah?,who told you?" "Ni na gani da idona,baka soni ba aliyyu sai da kwanta da ni?" Bai son wanna kalmar da taje furtawa bai san sanda ya zauna dirshan ba qasan office din,"wallahi Allah fadeelah idan ba tare muka fara son juja ba to da kadan kika rigani,wani kurman so nake miki fadeelah ki yarda da ni ba tare da ni kaina na sani ba,zuciyata na sonki ba tare da nasan hakan ba,na sani......kuma na zaci haka dama zaki zaci cewa jikinki nake so,saboda ban tashi sanar dake ina sonki ba sai a wannan gabar,bani da kalmar da zan kare kaina da ita,amm abu daya ne zai tabbatar miki da gaskiya ta,abun kuwa shine....ki amince ki dawo gidana fadeelah wannan shi zaisa ki tantance wanne irin so nake miki,zaki gane za kuma ki fahimci ba wani abu daya nake kwadayi tare da ke ba....a'a....kedin gaba dayanki nake qauna nake so fadeelah,na miki alqawarin baza sake taba koda yatsanki ba har sai kin nutsu kin amince da soyayyar da nake miki "Fadeelah na sani ni da bakina nace miki bana sonki amma wallahi Allah shine shaida ba haqiqanin abinda ke zuciyata ba kenan,ban taba jin qinki a zuciyata ba dai dai da qwayar zarra,wallahi fadeelah da bana sonki bazan aurenki har na iya zama da ke ba,bana iya zama da abunda zuciyata ke qinsa,mata nawa ke sona?mata nawa aka kawo min a take na qisu?,amma fadeelah na amince na aureki na zauna qarqashin inuwa guda dake.....nake ci daga abincin da hannayenki suka sarrafa shi....nake buri da muradin sha daga abunda hannunki ya hada,nake kuma kwanciya bigire daya dake qarqashin rufin kwanon daki guda" "Fadeelah.....kalli qwayar idanuna na tabbata sun isa amsa a gareki,ban iya qarya ba fadeelah,amma karo na farko da na fara yinta a rayuwata,na bugi qirji nace bana sonki bayan nasan ba haka bane,nace bazan soki ba koda wata rana ne bayan *bansan gobe ba,ba wanda yasan gobe sai Allah*,gashi yau wata ranar tazo ta riskeni ta qaryatani......kuma nima na qaryata kaina da kaina"yayi shiru idanunsa na kanta yana maida numfashi Gaba daya ya gama da ita,ya lalata mata dukkanin tunaninta,ya tarwatsa duk wani mummunan tunani zato da tsammani da a da take da shi a kansa,maimakon haka ma sai wata sabuwar qauna da soyayya tasa dake ratsata har jinin jikinta,ahankali take fasa qashi tana malala har zuwa bargonta,jinta take kamar ba'a duniyarmu take ba,abinda ta jima ta
Chapter 64 · 0% Book details