← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 84

Sashe 81

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Wannan ce rana ta qarshe Kuma company na qarshe da aliyyun zai qarasa bude wa ,dukkanin yaran nata uku sanye suke cikin sutura iri daya sai dai su maxan na maza ne Islam Kuma na mata ne haka aliyyu ke sawa ana musu,tuni Muslim da aslam suka saje cikin fararen fata su da abbunsu,Fadila kuwa shigar babarbariyar usuli tayi (kanuri)cikin lafiyayyar laffaya maroon tayi mata kyau matuqa,sosai ta burge mutanen sin har wata Daga cikinsu mr.shengping ta Kasa shiru har sai da ta yaba family din na su
Ahankali bai sake yiwa kanta ba sai da aliyyu ya anshi microphone
"A kyau ina farinciki gabatar muku da mata ta,farincikin rayuwata,zuciya ta jinin jini na,Fadeelah aliyyu Salim"
Tafi suka sa kowa so yake yaga fadilar nan da wancan karon ta ruda Mr aliyyu,dai dai da dai dai take ba wa Matan hannu suna musabaha maza Kuma su na gaisawa ne kawai ta wuce,kallonta aliyyu yake kawai ganin yadda take sarrafa harshenta tamkar haifaffiyar qasashen turawa,bata fiya yiwa yaranta magana da harshen nasara ba don suna yi a maka ranta,tafi yi musu larabci ko barbanci,shi Kuma ya musu fulatanci don su tashi da ainihin yaransu na uwa da uba
An tashi taro lafiya baya ga kyaututtuka da suka samu masu tarin yawa Daga abokan kasuwancin aliyyu,direct gidan mukhtar (abokinsa)suka wuce,a can suka ci gaboncin dare,Fadila na tare da matarsa Aisha suna hirarsu abinsu,Islam tayi bacci ita da Muslim,aslam Kuma na gun abbansa a parlour su na lissafe lissafe kan company din Fadila da irin ribar da aka samu
riba ce mai tarin yawa,da Kansas mukhtar ya shiga ya kirasu fadilan,sun soma mata baya nin irin ribar da aka samu,Tun tana dauka har kanta ya gaza dauka,sai ta sai kuka irin kudaden da dake ambato mata sunfi qarfin kanta,ace kamarta ba 'yar wani ba ta mallaki irin wadannan kudaden a matsayin riba.......
*Mrs Muhammad ce
[1/29, 9:56 AM] My Mom:
*WA YASAN GOBE?.......*
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*part 3*
4
Ya duba littattafansu na makaranta dayake wuni lkc shike dubawar,ya taimaka musu sukayi assignment, da suka bude na Arabic don son ya tsokaneta sai yace"kai kai 'yan uku wannan yafi qarfina,wannan ai sai balarabiyar mamarku,Ku kai mata maza"
Suka kwashi littattafan sai aslam ya noqe jikin abba nasa don tsoron zuwan yake ji,
Ta kalle su ta dan zare musu idanu
"Yalla Ku tafi gun abbu ya qarasa muku,Nima ban iya ba"suka juya gunsa din kuwa,yadda ta musun sai ya sosa ransa,sai da suka gama ya musu brush ya suya musu kayan bacci ya raka aslam gun samira sannan ya dawo
Tsaye yayi a kanta hannayensa harde saman qirjinsa"me kike nufi da abinda kika yiwa yaran nan?"
Ta dubeshi,sai ta Dakota da shan fruit salad dinta
"Me kuwa nayi musu?"
Sai yaga ta ma raina masa wayo,cikin hasala Zuciya ta tunzura shi yace
"Kinga malama,idan Kema baki sonsu ki fito ki gaya min,ina da inda zan kaisu dama ni na saba ganin hakan,ba kanki farau ba"
Za can ya qona mata rai,cikin gatse tace"shikenan,ka kaisun inda kake so din"taci gaba da shan fruit salad dinta
To Ashe bata sani ba ta tada masa tsohon miki,don haka ransa ya dugunzuma,ya ranqwafo wait in fuskarta"oho......alright, to wa ya sani ma ko ke kika hana kanji sake dauka ciki tsowon wadannan shekarun don wadannan ma baki sonsu ko?"
Wani wal tayi da idanunta ,batasan lokacin da bowl din fruit salad din ya subuce Daga h
nnunta ba,mai aliyyu ke nufi?,zarginta yake yi ko me?,a guje tayi bedroom dinta saboda wani kuka da ya qwace mata
Yana tsaye a gun ya bita da kallo,jikinsa yayi sanyi,sai yace jin baiyi furucin da ya dace ba,sautin kukanta da ya soma ji sama sama ya sashi zabura ya nufi dakin,saidai kafin ya kai gareta amai yabqwace mata,ta kuwa dinga kwarashi,Duk sai da tayi aaman fruit salad din da taci,gaba daya ya rude fadi yake"am sorry my queen, sannu kinji"shi ya gy
ra gun ya sai Mata ka6an bacci,Duk fusk
rshi ta canza kamar zai sai mata kuka,haka shim a ya gama nasa shirin baccin ya jawota ya manna ta da jikinsa,
Kalaman ban haquri yake ta jeranta mata,sai dai taqi ce wa kanzil,kai Daga qarshe ma sai ya juyata yaga ashe tayi bacci,ya sauke gajiyar Zuciya ya sake rungumeta yana jin rashin kyautawarsa har cikin zuciyarsa
*Mrs Muhammad ce
[1/29, 9:57 AM] My Mom: *WA YASAN GOBE?.....*
*CONTINUATION*4
washe gari asabar ce bai tashi da wuri,hakanan bai fita da wuri sai kusa da wajen azahar,don haka ta lallaba ta gama aikace aikacenta ta fice gun baba talatu wadda ta dawo a Daren jiya,nan suka shiga hirarsu tana bata labarin tafiyar da tayi
Ko da ya farka bai ganta ba yasan tana can,sukuku ya shirya don ya saba ita ke masa komai,wuraren daya ya daga Waya ya kira nasiru yace yaje ya dauko masa su Islam daga gidan momi wadanda da sassafe suka addabeshi sai da aka kaisu,Fadila na jinsu bata ce musu komai ba a lokacin
Hannunta riqe da kwanon zogalen da da baba ta kwadanta tana ci suna hirarsu cikin nishadi har da dariya, ganin shigowarsu kawai tayi suna rigen rigen fada wa cinyarta banda aslam da ya rakabe,batayi tsammanin dawowarsu haka da wurwuri ba,sai yaron ya bata tausayi amma sai ta dauke kai,don kaxa na take ranta ne ba don bata sonshi ba don ta koya masa darasi ne, duka yaran suka gaidata suka Kuma gaida babar kamar yadda ta saba musu Gaisa babba,shima aliyyu suka Gaisa yayi mata sannu da hanya tare da tambayarta mutan garin
Sai ya kalli baban yace"baba Zuwa mukayi ki taya mu roqo,'yarki muka yiwa laifi Kuma taqi yi mana afuwa"
Baban ta kalli Fadila"a'ah,ni kam na San 'yata bata da riqo,ba shakka laifinku mai girma ne,me kuka yiwa diyata?"
Da sauri Fadila ke girma aliyyu inkiya da ido na yayi shiru don Allah amma Sam sai yaqi kulawa
,"baba,aslam ta daka har jikinsa yayi shatin bulala,Kuma suka shige ciki suka barshi a waje,to nayi fada ne har ya wuce kima,na gane kuskure na na bada haquri amma anqi yafe mana,sai ake mana horo da halin ko in kula"
"Ashsha,ashsha,ya akai haka ta farun?"ta maida tambayar ga fadila,cikin raunin muurya tace"baba yanzu ace fisabililahi kamar aslam idan yayi laifi baza'a hukuntashi ba?,yaron nan sau hudu yana fasamin wayoyi,rashin jinsa duka ya zarta na 'yan uwanshi,ga raini,ya raina Muslim,har fa sai yasa hannu ya dakeshi,haka Islam ma bata tsira ba,dan qanqanin Abu zata masa yasa hannu ya maketa bayanshi babu mai dukanshi wai baya son raini"
"Sannan da ance za'a hukuntashi baban ya hana,to don kawai fa rannan na hukuntashi suka dau fushi ya kwashe kayanshi ya maida gun mominsu,qarshe ma harda cemin wai wa ya sani ko......"sai ta kasa qarasawa hawaye ya subuce mata,ai bai san lokacin da ya isa gareta ba,hannayensa ya sanya yana dauke hawayen,sai baba ta yunqura ta miqe ta fice tsakar gida,don ta lura abun nasu salon maganar nan ce da ake cewa *fadan masoya hutu ne ko sunyi zasu dawo su shirya*
Yayi Kane Kane ya hana hawayen zuba"kada ki yimin haka mana Fadeelah ta,na riga na yima ka ina alqawarin fa ba zaki sake zub da hawayenki ba,kinsa alqawari na ya karye?,jiya Kiyi daya kyau kinyi,ina jin zuciyata cikin qunci duk sa'ilin da naga hawaye a fuskarki,pls ki yafe mana,ni da 'ya'yana bamu saba ganinki haka ba kina hukuntamu"
Sai ya juya gun yaran ya kira su da hannu"Ku zo mu bawa mamee haquri"ai kuwa suka yaso da saurinsu duk suka durqushe a gabanta yadda suka ga abbun na su yayi
Muslim yace"pls mamee kiyi haquri kinji mamin mu"
Islam tana riqe da kunnuwanta tace"sorry mamee,pleaseeeee"
Aslam ya taso ya kama qafarta"mamee na na dai na bazan sake ba,kince annabi nabda haquri Kema Kiyi maker pls,I promise bazan qara ba,Duk abinda kika ce nayi zan dinga yi kanji"
Sai suka suka bata tausayi,ta Miqa musu hannayenta suka taso Muslim a hagu aslam a dama Islam ta dane cinya,ta dinga shafa Kansu tana cewa"na yafe muku,Allah yayi muku albarka"
"Ameen maman mu mana sonki"
Ta saki murmushi"Nima ina sonku yarana"
Aliyyu dake kallo su cike da sha'awa ya Matso yana turo mata kansa"Nina mamee a samun albarkar"cikin hararar Soyayya take kallonshi
Sai ya kwabe fuska shims kamar tarin"kunga maminku taqi shafa min kaina ko?"
Nan suka rude da ce wa mamin mu a shafawa Abbu shima,dariya tayi shima ta shafa masan
*Mrs Muhammad ce
[1/29, 9:57 AM] My Mom: *
*WA YASAN GOBE?......*
*WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*
*part 3*
4
Sai lokacin baba ta dawo,taji dadin ganin sun sasanta kansu ,nan taja hankalinsu su duka har yaran,cikin gamsuwa sukayi mata godiya
Ya kalli fadilar cikin marairaicewa"to ataimaka azo a yimin Garin pepper chicken din nan mana mai dadi, ni da abokaina duka zamu tayaki aikin"
Ta noqe hancinta tace"a dauri kashi ko a bata igiya,babu abinda kika biya sai qara wa mutum aiki"da sauri Islam ta kalli mamin nata tana nuna kanta da yatsa"banda ni ai ko mamee?"
"Har ke mana"jin haka yasa su Muslim suka qyalqyale mata da dariya,sai ta kwabe fuska ta soma diddira qafafu kan Dariya da su Kayi mata,aliyyu ne ya taba fadan ta hanyar daukarta ya sabata a kafada aka tafi yin paper chicken din baba talatu ta musu a dawo lafiya bayan sun mata tayi Zuwa tace lazumi zata yi sai sun dawo,islam tace zata kawo mata qashi,Duk suka sa dariya
Haka suka cikata da surutu cikin kitchen din,ba ga yaran ba ba ga babansu ba,aiki dai na surutu kawai suka tayata ta,har ta samu ta gama ta tura musu,ya tasa yaranshi a gaba bayan kowannnensu ya wa ke hannu suka soma ci cikin plate guda
Sai da suka ci kusan Rabi sannan ya dubeta tana zaune gefensu tana lura da yanayin can abincin yaran nata,Duk Wanda ya gutsuro kafin ya ci sai ya miqawa abbunsa, yaran na da matuqar son iyayensu
"Ke baki ci ne mamee?"
Ta zumburo baki "sai da ya rage saura qasusuwa wannan za'a yimin t
yi?"
Sai suka soma rige rigen bata a baki,kuwa yana ce wa nashi zata ci
Murmushi ta saki tace musu duka ta gode,Allah ya yi musu albarka ita ta qoshi,taci zogale gun baba,aliyyu yayi qasa qasa da Maurya bayan ya dubeta"anya baby na lafiya qalau kike?,ina lura dake rashin son cin abincinki ya qaru akan na ainihi,fruit salad kaw
i kike bawa muhimma
i,anya ba wani cikin gareki ba?"
Kai tsaye ta Daga masa gira tana murmushi,cikin zumudi har baisan sanda ya daga murya ba yace"are you serious baby?"
"Yes"tace da shi cikin wata iriyar murya mai taushi
Ya lumshe ido a fili yace"alhamdulillah,alhamdulillah"
Sai ya tara yaran yana fada musu sun kusa yin qani,ihun murna da tsalle suka dinga yi abbun na su na biye musu,ta saki murmushi bayan ta dau ke ido
daga Kansu
Gaba daya aliyyu ya maida yaran abokanshi"
Chapter 81 · 0% Book details