← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 84

Sashe 24

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya aka kaya ko kada dai ku gaji ku biyo safiyya insha Allah don jin kanun labaran Mrs muhammad dinku ce 07066139278 [10/16, 12:38 PM] Salma WA YASAN GOBE? Written by safiyya Abdullahi musa huguma A bakin mudubi ta yada zango ta fara shafe loko da saqo na jikinta da turare dama ta saba da yin hakan kwalliya irin ta zamani mai tsari ta shiryawa fuska fuskarta bata cikata da jagwalgwalo ba ta taje gashinta mai tsaho da sulbi ta daureshi da ribbon ja swiss lace ta saka orange mai adon ja riga da skirt dinkin rafa wanda yayi masifar fito da sharp dinta,ta bata lokaci tana zana dauri a kanta ya zauna gwanin sha'awa fashion ta saka na dutse na sarqa da dan kunne sannan ta cika hannunta da awarwaro irin na india ja mai ashirin da hudu ya ahmad ne ya taho musu da tsarabarsa sati biyu da suka wuce,plate shoe ta saka orange and red ta sake feshe jikinta da turaruka sanna ta kalli kanta a mudubi,masha Allah ta fadi ba tare da tasan ta fadi ba sai murmushi ya subuce mata ita kanta yau ta sake gasgata kyawun da ake fadar tana da shi,kiran sallar magaribar da taji shi ya sata saurin fitowa ta shiga kitchen ta shirya kayan abincin ta kulle sashen nata ta fito tana tunanin qila ma aliyyu har ya dawo,ta cikin balcony din ta ta isa sashen ba alamun ya dawo don haka ta sa key dinta ta bude tana shirin shiga tajiyo alamun tsayuwa mota ta waiwaya sai taga samirah ce ke shirin fitowa daga motar tata wani irin kallo samiran ta watso mata wanda fadila ta gaza gane mai take nufi,dauke kanta tayi abinta ta shige don ba ita bace a gabanta tana mamakin masifaffen yawo irin na samira Cikin qwarewa ta shirya table din sannan ta sauko cikin falon ta kunna tafkekiyar t.v plasma din dake manne a bango cikin sa'a kuwa malaminta ne ke karatu a saudi qur'an ta dan qaro volume matsakaici ya game falon ta koma gefe ta tada sallarta cikin nutsuwa bayan ta idar ta koma ta zauna tana kallon yadda mahajjata ke dawafi Mintina biyar da zaman nata taji ana bude get jikinta ya bata Aliyyu ne jikin window taje ya dage labulen tana kallonsa har ya fito daga motar dukkan alamun dake nuna gajiya ga mutum sun bayyana a tare da shi,duk da ya gajin amma a nutsenshi yake kyawunsa na nan saidai fara'a da tasake yiwa fuskarsa qaura hirar da fadila keyi kenan ita da zuciyarta nasiru ne ya kulle motar bayan yafito sanna ya miqa masa kayayyakinsa da muqullan cikin rusunawa kamar ko yaushe aliyu ya karba yana cewa kada kowa ya jirani gobe ka sallamesu don bazan fito da wuri ba idan ka sallamesu sai kuci gaba da list din suna yan wadanda suka karbi kayan amma a cire sunan alhaji hamza wannan mun gama da shi ,nasiru yace ok insha Allahu ya juya yana shirin wucewa yace Allah ya tashe mu lafiya,ameen ya amsa masa Burinsa ya isa gida yayi wanka ya samu abinda zaici ko da tea ne donshi kam har yau cikin matan gidan babu wadda zai nuna yace girkinta ya masa har gwara salima yakan qoqarta yaci indomie dinta don kore yunwa,yayi mamakin ganin qofar tasa a bude amma sai yayi zaton ko salima ce,ba wani dadi da yaji don ason ransa so yayi ya zauna shi daya ya samu hutu Saidai yana tura qofan wani daddadan qamshi ya daki hancinsa wanda ya tilasta shi lumshe ido kasancewarsa ma'abocin son qamshi sai ya shiga tunanin inda ya taba jin qamshin amma ya kasa cankowa idanunsa suka sauka a kanta bata anakara da ya shigo bane ko tsorone ya hanata motsi?ya dan tabe bakinsa yana tunanin mai ya kwao ta kuma? Ya qarasa shiga falon yana sallama a nutse ta dago tana amsawa ya dan zubawa fuskarta ido zuciyarsa na son yaba wani abu amma ya rasa meye shi?ita kuwa gabanta ke faduwa cike da fargabar kada ya wulaqanta aniyarta yadda ya saba ganin yaddda ya hade rai kamar ya ga kashi,sai kuma taga ya dauke kansa ya nemi kujera can gefe ya watsar da kayan hannunsa sannan ya zauna har baisan sanda yace wash! ba ya sake lumshe ido yana ci gabada sheqar qamshin da ya ji yayi masa har cikin zuciyarsa ya rasa kuma ta Inda ya samu don dai shi har ya bar falon baiji qamshin ba sai yanzu da ya dawo Sannu da zuwa tace cikin cool voice dinta,ya bude idonsa tana durqushe gabansa riqe da cup da jug na glass baice komai ba yabi hannun nata da kallo dake riqe da cup din tana tsiyaya masa lemon zobon dake ta tsatstsafar sanyi da qamshin abarba ta janyo center ta dora a kai sanna ta balle murfin gorar ruwa na c'bon ta cika masa shima cup da shi ta ajjiye masa duk baice komai ba cikin dari darin kada ya gwasaleta ta miqe ta dauki briefcase dinsa safa takalmi key dinsa da duk ya wurgar din ta yi cikin daki da su Tana shiga tayi maza ta maida qofar ta jingina jikinta ta dafe qirjinta tanajin yadda yake bugawa da sauri da sauri idanunta a lumshe tana dan murmushi , cikin zuciyarta tana cewa wai Allah na! Sai da ta dan nutsu sannan ta ajjiye kayan a inda ta tsara musu kai tsaye ta wuce toilet ta kashe makunnin heater din don har jar danja ta kama alamar ruwan ya tafasa ta hada masa ruwan wankan a bathtub ta saisaita shi ya zamo mai dumi sosai yadda zaiyi saurin saukar da gajiya sannan ta zuba masa turarukan wanka a ciki A hankali yasa hannu ya dauki cup din zobon yana tunanin meye wannan? Ya kai bakinsa da niyyar dandanawa sai gashi ya shanye har da qari sai da yasha cup uku sannan ya saki ajiyar zuciya saboda yadda dadinsa da sanyinsa ya ratsa shi sai yaji kaso goma na gajiya da qishirwarsa har ma yunwar sun fara sakinsa ya samu relief har a qwaqwalwarsa ya jingina bayansa da makarin kujera Sai a yanzu ne ya lura da canjin da falon ya samu ko ina tsaf tsaf kamar yadda yake so,tunanin wa ye yayi aikin yake don shi kqm daga samira har salima yasan cewa matane masu azabar ganda da ko ruwan sha sai ya tambaya ake iya tashi a dauko masa,ga ruwan wanka can a toilet ko kana da buqatar yin wanka,ya dago da kansa tuni har tayi hanyar kitchen fadila tayi hakanne don gujewa baqar maganarsa ko da ziyi mata ta maqale a window din kitchen tana leqensa Sai da ya bata lokaci sosai har fadila tayi zaton bazaiyi wankan bane ta soma dana sanin shishshiginta sanna ta hangoshi yana kwance agogon hannunsa hadi da cire suit dinsa ya riqesu a hannu ya shige dakin tabi bayansa da kallo,ta janye idanunta hadi da lumshesu ta dafe goshinta da tafin hannunta tana cewa a can qasan maqoshinta"wo hoho Aliyyu badai miskilanciba?.... sai kuma ta sake sakin murmushi tana cewa"Allah ka mallakamin Aliyyu"tayi saurin dafe bakinta tama zare ido saboda ta fuskanci maganar zuci ce ta fito fili Sak yayi ya tsaya yana kallon dakin baccin nasa komai kamar yanzu aka jerashi ko tsinke babu a farin tiles din dake mamaye da dakin ya jinjina kai ya ajjiyr kayan hannunsa a gefan gado ya fara binciken inda ya ajjiye rigar wankansa sai ya bude wardrobe donnya dubata a ciki,canji idanunsa suka masa karo da shi,wardrobe ce ta jikin bango mai hangar komai ya canza bangaren shadda daban yadi daban suit dinsa haka kai hatta socks dinsa da handkerchief an masu nasu tsarin bai san sanda ya saki murmushi ba don tsarin ya burgeshi kasancewarsa dan gayu ya tabbatar babu tsarin rigar wankansa a gun don haka ya haqura ya wuce toilet cikin ransa yace wonderful cikin wani glass dake manne a kwanar bandaki ya hango rigunan a tsare jikin hanger bai bata lokaci ba ya shige cikin ruwan wankan duminsa da qamshinsa suka ratsashi sai yaji kamar kada ya fito,ya shafe kusan minti talatin sannan ya sabe jikinsa ya dauraye ya fito bisa gefan gadon ya zauna ya tsane jikinsa ya nemi farar jallabiya yasa don yafi son sata idan ya dawo daga aiki ya taje kansa ya feshe jikinsa da turare sanna ya bude jakar computer dinsa ya cirota yayi waje da niyuar shiga kitchen ya tafasa ko tea ne ya sha Ganin ya zauna yana aikinsa ya sanyata debo kayan ta shimfida babbar ledar cin abinci a gabansa baisan me takeyi ba sai da yaji qamshin abinci nata shiga hancinsa sanna ya dago kansa ya dubi gabansa ta jera tuwon a farin kyakkyawan plate miyar na wani dan kwano na tangaran shima fari ne tasha man shanu ta cika wani plate din da farfesun ragon ruwan ta zuba ruwa na sha da na wanke hannu ta tsiyaya masa lemo sanna ta janyo tissue box ta ajjiye masa tace bismillah ya kalleta yace " ce miki akayi da yunwa na zo? Ko an baki labari ina buqatar abincinki kinga malama kwashe abincinki ki ban wuri, Ba qaramin sosa mata zuciya maganganun suka yi ba bata san sanda hawayen da take boyewa suka silalo mata ba karo na farko kenan tun sanda ya fara mata cin kashi,batayi qoqarin maidasu ba ta barsu suka ci gaba da zuba Cikin zuciyarsa addu'a yake allah yasa kada ta kwashe din don tunda yaji qamshin sha'awar cinsa ta kamashi ai kuwa aadu'arsa bata karbu ba don a zuciye ta soma maida abincin cikin warmers din Kuyi haquri da wanna yau bani da chargy wadatacce Mrs muhammad na muku fatan alkhairi [10/16, 12:39 PM] Salma WA YASAN GOBE? Written by safiyya Abdullahi musa huguma Sai da yaga da gaske take cikin daurarriyar fuska yace kinga malama zuba kada a qarani gaba ace bani da adalci tunda kin kawo kanki" ya fadi kamar wanda da gasken tilastashi akayin,kalmar tunda kun kawo kankin tayi matuqar bada gudun mawa wajan qona mata rai don haka hawayen da suke zuba suka qara gudu Malmala daya ta saka masa da miya ta miqe wata zuciyar na zugata kiyi tafiyarki kawai wata kuma na lallashinta
Chapter 24 · 0% Book details