Sashe 20
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tashi wani shocking yaji kamar an jashi da wutar lantarki,ya sabata a kafadarsa ta miqe zata soma rigima suna hada ido da shi tayi gum da bakinta ta mayar da kanta kafadarsa ta kwantar ya sauka da ita cikin falom ya kwantar da ita bisa doguwar kujera ya karanta mata addu'o'in bacci na tsari ya tofa mata sannan ya koma Ta tsugunna ta gaida uncle abba ya amsa mata cikin kulawa yana cewa lpy lau diya ta,sannan ta ja kujera itama ta zauna,sumayya tayi serving din kowa sannan akai bismillah aka fara ci,kwata kwata kasa sakewa fadila tayi ta kasa kai koda loma guda bakinta sai juya cokalin kawai take a cikin abincin ,amma ga tarin mamakimta sai taga samira ta saki jiki tana ta kaiwa uwar hanjinta harda tsiyaya lemo da ruwa da kanta,tayi sakewar da ko ita da uncle abba yake kamar uba a gareta ba zata iya irinta ba Abinka da mata momi na ankare da yanayin nutsuwar kowaccensu tana kuma sake godiya ga sarki Allah da ya qaddara fadila ta zamo daya daga cikin family dinsu,afakaice rabi'ah ta qarewa samirah kallo uadda take lodar abincinta ko aliyyu da yake dan gida baiyi haka ba,ki saki jiki mana fadilan ummi kici abincin ki mu fa iyayenki ne ko babu aliyu baki ga yadda yar uwarki ya saki jikinta ba?,cewar ummi,samirah ta amshe cikin tabe baki tace momi kinsan wani akwai qauyanci da rashin wayewa atare da shi"sai kowa yayi dif rabi'ah da takaici ya cikata tace ba rashin wayewa bane kowa dai da irin yanayinsa,ta sake tabe baki tace uhmm,ita kuwa fadila dariya ma ta bata sai daga qarshe ne taga kada suji ba dadi ta kurbi lemon da rabi'ah ta zuba mata Bayan sun kammala momi tasa rabi'ah da sumayya suka gyare gurin suka kwashe kwanukan,suna shirin wucewa don su basu guri momi tace su dau iftihal su wuce da ita,falon yarage daga fadila aliyu samirah sai momi da uncle abba Abba yayi gyaran murya yayi bismillah sannan ya kirawo sunan aliyu ya amsa masa"naam abba"ya dora "aliyyu girma yanzun ya hau kanka duk da a baya kwatan kwacin wannan girman ya taba hawa kanka kuma kayi namiji qoqari wajen riqeshi yadda ya kamata amma bai kai wannan ba,a yanzu dole na sake jaddada maka saboda zama ne da zaka yishi tsakanin iyalinka har su uku wanda ko ni mahaifinka banyi duk da komai tsarin Allah ne Daga samirah har fadila babu wadda gabanta bai fadi ba har sai da samiran yabdaga kai ta kalli abban,uncle abba yaci gaba "lamarin mata ali sai da haquri kawaici da kuma jajircewa halitta ce su maau wuyar sha'ani amma idan ka duba Allah sai komai ya zo maka da sauqi ,aliyyu ina horarka da kaji tsoron Allah ka tsaida adalci tsakanin matanka duk wadda ka cuta wlh wlh sai allah ya bi mata haqqinta sai kuma ya tambayeka,kuma ko ni ban lamunci rashin adalci ba acikin gidanka ka riqe Allah ka kuma ji tsoronsa Ya juyo gunsu fadila da kansu ke qasa kowa da abinda ke cikin zuciyarta yace "dukkaninku ina kallonku ne a matsayin 'ya 'yana na na cikina da na haifa nasihar da zan muku itace kuma ku ji tsoron Allah kuyi zamqn aure a matsayin ibada kuyi biyayya ga mijinku.ku kyautata zamantakewar ku domin kuwa shine muqullinku na shiga aljanna ko wuta idan kuka saba masa Allah ya tsare mu,magana ta biyu kuma na dakatar da shi ne daga gaya muku don inason na gaya muku ni da kaina ta hanyar da ta dace,nasan kowacce mace haka Allah ya halicceta da kishi kuma ba zaku so abokiyar zama ba a yanzu amma ba yanda muka iya da hukuncin ubangiji kuma aure rai ne da shi matuqar bai qare ba komai dadewar zamani sai an dawo anci gaba da yinsa to ina mai baku haquri a madadin aliyyu,mahaifiyar khadija(sunan iftihal na gsky haka abba ke kiranta yawancin lokuta)zata dawo dakun aurenta ina fata zaku hada kanku ku zauna lpy,samirah ta dago kanta a gigice tana fiddo da idanu waje tace"abba mai kake fada ne?dama da gaske aliyu yake da yafara zancen?" aliyyu ya juyo ya kalleta wani huci ya saki abba ya lura da yadda yanayinsa ya canza ya san yadda fishin aliyyu yake don haka ya danne shi,cikin tausasawa ya kalli samira yace ki kwantar da hankalinki yata insha Allahu ba zaku fuskanci rashin adalci ba daga gun aliyu ni kaina bazan lamunci hakan ba shiru tayi tana muzurai idonta ya kada yayi ja saboda ganin yadda aliyu ke gasa mata hara ra tamkar zai cinyeta danya,itakam fadila gabq daya jikinta ya saki tunaninta daya ta ina zata samu aliyyu bayan ga wasu na farautarshi ? Jin sunyi shiru dukkaninsu abba yace da momi"kina da magana momin yara?" Ta danyi murmushi tace" aikace komai abban yara,saidai nace aliyu kaji tsoron Allah kamar yadda abbanka yace sannan ku kuma Allah yayi muku albarka kuyi haquri kuma kuyi biyayya sai.kuci riba"suka amsa da amin banda samira da ta kasa furta komai sai tafasa da zuciyarta keyi,abban ya sake basu dama akan idan da mai magana ya yi,ba wadaa tace komai sai aliyu da yace"abba da momi na gode muku kuma insha Allah zaku sameni mai amfani da duk nasihar da kuka yimin zan zamo mai adalci da yardar Allah"Allah ya amince suka ce,fadila ta fito da kayan data taho musu da su ta dorawa abba nasa a gabansa sann ta dorawa momi nata Duk da ranta babu dadi amma ta ji dadin yadda suka nuna jin dadinsu suka sa mata albarka,aliyyu kansa can qasan zuciyarsa yaji dadin hakan don shi mutum ne mai dake qaunar wanda ke kyatatawa iyayensa,haushi ya sake cika samira tayi dana sanin zuwan ta gidan yafi sau cikin carbi bata son taga wani yana yabo ko son fadila kwata kwata Cikin mota ma kowa da irin zaren da yakr saqawa zuciyarsa shikam ya dake abinsa kamar bashi ya sanar da mata har biyu zai qara musu abokiyar zama ba tuqinsa kawai yake a nutse,fadila tata saqar na yadda zata juyo da hankalin aliyu take bata so kuma bazata so ace kishiyoyi har biyu su fuskanci raahin qauna da jituwa dake gudana tsakaninta da shi ba,samira kuwa wani mahaukacin kishi ne ke taso mata zuciyarta namata saqa da baqin zare,tana shirya mata irin mummunan matakin da ya kamata ta dauka abu guda ke taka mata burki idan ta tuno yadda aliyyu ya birkice mata da yanayin da ya sameta a daren farkonsu tasan har yanzu dafin na sukar zuciyarsa somin kuwa duk wani tanadin soyayya da sukayi wa juna tn daga ranar ya rushe,duk kuma waa qauna tata dake zuciyarsa wadda ta rage tuni ta rushe Cikin satin komai ya fara kankama abubuwa suka cedewa baiwar Allah fadila ga zirga zirgar shirye shiryen fara zuwa aikinta ga kuma lamarin na dake mintsinin zuciyarta duk da shiryr shiryenta ya tafi da kaso.mafi tsoka daga damuwar dake cin xuciyarta,tuni tayi waya gidan an ma motocinta service daya tsohuwar tata ce tun ta gida aka sake mata fenti da wasu abubuwa sai ta tashi ta dawo sabuwa dal don tana qaunar motar bata son rabuwa da ita yanzu sai kuma wadda aliyyu ya sa musu a lefe wadda ta sam ira tuni ta dade da cin uban tata ta mora qawaye su ara suma su mora Kira ta dinga samu daga su anty hauwa anty hafiza har da farida kowannan su nasiha ce da jan hankali ne nasa har farida ta so karayar mata da zuciya saidai tayi qoqari matuqa wajen nuna dakiya da mai da komai ba komai ba Wa yasan gobe? Samira kuwa abun nata sai ya zamto tamkar mai qaramin ciwon hauka kamar a kanta aka fara kishiya kasancewar ta samu gudun mawar zuga daga qawaye da yan uwa kala daban daban duk da wasu ba don Allah suke bata basuna baqinciki da rufin asirin kawai da take ciki ne(qalubale a garemu mata sai azo ayita baki shawara akan za'a miki kishiya ko wani harkar wani ahaka kamar mai sonki amma da zaki ga cikin zuciyarsa game da ke tsoronsa ma zaki koma ji,sanin haqiqanin mutum sai Allah,sai ki auna da hankali da Allah ya baki a matsayinki na mutum mai tunani)sai ta sake zama kamar zararriya ita kadai ma abangarenta sai ka jiyota tana bala'i tana zunduma ashariya(wa'iya zu billah)cikin satin baqi ta dinga yi kala daban daban kowanne da tasa guzuri da salon hudubar waccan ta shiga waccar ta fita Tun Aliyu na zuba mata ido idan tana salon rashin mutuncinta da haukanta har sai da ya zamto idan tazo sai dai ta gajibda bugun sashen nasa ta juya da haukanta ta koma inda ta fito,tuni fadila tabgama tsarawa kanta yadda zata tafiyar da rayuwar aurenta ta gama tanadar komai,tana hango cewar itama fa maca ce tana da duk wani abu da da duk wata ya mave maiji da kanta ke taqamar tana da shi,tana da duk wasu qualities da ake buqatar mace da su kafin ta amsa sunan ta na mace,to me yayi saura banda itama ta shiga fagen a dama da ita?? Me zata jira banda ta shiga ta karbo aliyyunta? Ta gaji kuma lokaci yayi da take ganin ya kamata ace ta kasance da da shi ta gaji da dako da rainon soyayyarsa ita kadai Biki ya zamto saura kwana uku wanda yayi dai dai da sauran kwanaki bakwai fadila ta soma zuwa aikinta A ranar ne bayan sallar magariba aka shigo mata da akwatina set shida masu matuqar kyau maqarenda kaya nasiru yace mata inji maigida,ta jinjina kai ta rufe qofar sashen nata ta koma kan kujera ta zauna daya bayan daya ta budesu ta zubawa kayan ido duk budurin da ake sai yanzu zuciyarta ta tsinke hawaye suka soma zarya a kuncinta a hankali take sa yatsunta tana sharesu tabbasa an jarrabci rayuwarta da jarabta mai girma ta sani cewa son aliyu jarabta ce daga ubangiji acikin jininta yake kuma bata fatan Allah ya dandanawa wata mace kwatankwacin yadda take ji a zuciyarta,nan saman kujerar ta lafe tana hawaye a hankali take furta HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL har taji zuciyarya ta soma sanyi Haya niya da hargowa take jiyo wa maau qarfi suna karade filin gidan hakan ya