← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 84

Sashe 6

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

zai gice daga falon,ta miqe tsaye ta yi masa kallon sama da qasa ta yatsina fuska ta tofar yawu a gefanta sannan tace"see you wane mashahurin maqaryacin ne ya gaya maka ina maraba da kai da zaka zo kanata soki burutsu,ni dinma ba yimin kayi ba don baka wuce dan aiken gidana ba a tsarina,amma ni nasan darajar dan adam banga a gidammu ana tozartashi ba kuma na iya darajatta zancan magabata na shi yasa ban tozarta mutumin da mahaifina ya zabamin ba,idan banda qaddar ina budurwa sabuwa dal a leda mai zanyi da bazawari ragowar wata.......... Wata iriyar wafta ya kawowa bakinta wanda ta tabbatr da ya sameta sai lebunanta sun fashe,da gudu ta bude daya qofar falon da zata kaita cikin gida ta baya ta shige ta bankowa aliyu qofar ta batshi tsaye zuciyarsa kamar zata fito saboda fushi,ya ga alamar akwai rainin wayo tattare da yarinyar,yayi qwafa cike da zafin zuciya ya fice,kai tsaye da inta ta nufa ta kulle qofarta gam tayi zaman dirshan saman carpet dinta,wani irin kuka ta saki tayi qasa da kanta ,ta rasa me zayayi farinciki ne ya kamaceta ko baqinciki?ta jima a zaune tana kukan tate da tambyat kanta da kanta shin dama baqinciki da farinciki na haduwa loka i guda cikin zuciyar bil'adama?yau kam ta fahimci hakan na faruwa tunda gashi yau ta tsinci kanta a ciki Aliyyunta mafarkinta na kullum?burin zuciyarta muradinta yau shine zai zama mijin aurenta babban burinta kenan dama anan duniya,sai dai kash yazo mata ta wata iriyar fuska da sigar da bata tsammatar mata ba,baya sonta baya qaunarta abin har ya kai tsananin da bazai iya boye qinta a zuciyarsa ba harsai da ya tsaya a gabanta ya fesar mata,baya ga haka ba ita kafaice zata zama mall kinsa ba?zata yi sharing aliyunta da wata?ga ahi har waya ma ta rigata samunshi(maman iftihal) Da qyar ta iya janye jikinta ta gada saman gadonta,ba abinda ke mata amsa kuwwa akunnenta irin kalaman aliyu,kafin azahar zazzafan zazzabi ya rufeta,sau biyu farida na shigowa dubata tana ganinta a duqunqune tayi tsammanin bacci take,a shigowarta ta uku ne tace"kai yaya fadila wani irin bacci ne haka tun ten o'clock har one thirty?"tasa hannayenta ta janye bargon tana fafin"ba sanyi ake ba ba komai ba kuma kin....... maganar ta maqale mata sanda idonta yakai kan fadila ta zaro ido tana cewa"kinga idonki kuwa?"ta juyar da idonta daya side din sannan tace"kaina ke ciwo" Mrs muhammad bello [10/16, 2:39 PM] +234 706 914 1005 Wa yasan gobe? Safiyya Abdullahi musa huguma
Chapter 6 · 0% Book details