Sashe 30
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sauri yana tsaye bisa kanta hannunsa harde a qirjinsa shima idanunsa na kan t.v din sai a lokacin ta tuna da abinda ta masa dazu da hanzari ta miqe ta jawo hijabinta ta zira tana neman guduwa sai alokacin ya dawo da idonsa kanta fuskarsa a dinke tsaf,da baya da baya ta soma tafiya yana binta har ta dangane fa qofar bedroom dinta ta fafa ciki tana shirin danno qofar,yasa hannu ya kare ta,yaci gana da binta sai da ta dangane da sif dinta ,qwalla ta cika idanunta idonta tuni ya raina fata,girgiza kanta ta soma yi tana cewa cikin tawar murya"donA....Allahh kay......yi...yih.....haquri...."yasa yatsansa ya dalle mata baki,taji zafi sosai ta sanya hannunta ta dafe bakin ,ya zare mata ido sosai yace"wa kika harara? Ni sa'anki ne?kin raina ni ko?,still tafin hannunta na dafe da bakinta ta girgiza kai tuni hawaye ya balle mata ,ya saka hannunsa ya kama gashinta da ta tufke cikin hijabin har sai da tace "wayyo Allah na!......,hadi da wani dan guntun hawaye da ya silmiyo mata,ya saketa yana sake matsota har tana jin hucin numfashinsa,ta runtse idonta gam tana jiran jin hukunci na gaba,ta yarda aliyyun mugu ne,tasan yau Allah ne kawai zai qwaceta Shirun da taji yayi yawa ya sata bude idonta,ba kowa a dakin hasalima an ja mata qofar dakin sai ita kadai dake tsaye jikinya na kakkarwa,ta sake sakin kukan ta kifa kan gadonta Cikin kwanakin gaba daya ya gama tsanar bangaren nasa,bedroom sin da suke cikin corridor din wadanda bai amfani da su duk sai da ya budesu yayi amfani da su ,duk da alokacin su su samira suna ganin suna qure adaka gun gyaran amma shi sam bai masa ba,don ba wani qwarewa sukayi ba kamar na fadilan,yakan daure ne kawai ya nuna yabawarsa,ya tabbatar wa ransa nata yafi wannan kimtsuwa Kowanne dan adam wani lokacin kakan tsinci kanka cikin rashin jin dadin rai hakanan to haka yau aliyu ya tashi,alhamis ce wadda aka wuni garin lullube da hadari da iska mai cike da qamshin qasa,mutane da yawa yanayin yayi musu amma banda shi,biyar saura yama yi dawowarsa gida,yayi cilli da jakar tasa a falo,gidan dai na nan a yanayinsa na kullum wato shiru,toilet ya shiga ya watsa ruwa ya fitar jallabiya mai sulbi irin ta maza milk colour mai dogon hannu ya saka,ya feshe jikinsa da shamsul imarat ya hada da turaren chastity ya dawo parlour ya fitar da computer dinsa ta tafi da gidanka(laptop)ya jona mata chargy ya jawota har kan kujerar da zai zauna ya dora ta a saman kujerar,ya daddanata ya bude bayan komai ya gama daidaituwa ya soma aikin da ya dawo da shi Munti biyar goma sha biyar sai aikinbya soma gagararshi saboda yunwa,ya dafe kansa da hannu daya yasa dayan ya lallatsa comouter din ya kasheta,ya zubawa fridge dinsa ido yana nazarin me zaici a ciki?komai dai na nau'in ciye ciye akwai aciki Saidai gaba daya sun gundireshi babu abinda yagi buqata sai abinci mai nauyi da gishiri,gaba daya taste din girkinsu salima bai gamsar da shi bare yasa su dafa masa wani abun,koda ranar gikinsu ne yana yin kawaici ne kawai yaci don kada suga rashin kyautawarsa A nutse ya isa gaban freezer din ya bude yana sake kallonta kamar baisan meye da meye a ciki ba,hannunsa yakai kan madarar fresh yo da tayi sanyi sosai tanata fidda tsatstsafar sanyi yasa daya hannun ya maida murfin freezer din ya rufe,ya maida kallonsa kan rob dake riqe a hannunsa yana jujjuyata tamkar mai karanta rubutun dake jikinta Ya saki tsaki hadi da cillar da robar kana yayi tattak ya isa bakin window dinsa yajanye labulayen jiki gefe daya ya dora idonsa a harabar gidan,idanunsa suka sake kaiwa kan bangaren nata a karo na barkatai,tarwai yake da haske alamun tana nan,ji yayi y gaji baAi iya jutewa ba sole ne yazo tayi masa aikin da tasabar masa idan yaci gaba da jurewar yana jin qila yunwa da tsantsami na iya illatashi,ya juya ya zira slipper dinsa ya fito.... Mrs muhammad ce [10/16, 1:41 PM] Salma *wa yasan gobe?.....* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* Ya juyabya zira slippers dinsa ya fito Gaba daya tana ma gida babu inda ta fita saboda ba ba abinda zatayi a gidan radiyon shi yasa bata shiga ba,zamanta tayi ta dinga bacci abunta sallar azahar kawai ta tashi tayi ta dan sha yoghurt ta koma baccinta Qarfe hudu da rabi ta farka tayi wanka,tq gabatar da sallar la'asar din da ake binta,riga da skert ta saka hade da mayafinsu sannan tayi kitchen da azama saboda wata hadaddiyar yunwa dake sakadarta A tsaitsaye ta hada jallop din taliya da tasha kifi ta watsa mata carrot piece da grean beans,da zaman jiran dahuwar abincin da zata yi sai taga gwara ta hada lemo,cikin lokaci kadan ta hada lemon kwakwa da yasha madara ta bude freezer din kitchen din ta sanya ta a ciki,bayan ta kammala ta juye a plate ta kalli plate din tana murmushi hadi ya tsina fuska don ita kanta tasan ba iya cinyeta zata yi ba ta mata yawa"let me try"ta fada tana gyada kai ta hado da lemonta dake cikin jug din ta taho dashi parlour ta zabi kujerar da zata zauna akai don haka ta jawo centre table ta dora su a samansa Ta juya ta koma daki don daukar wayarta ta tashi ne ta tarar da missed call din fauziyya colleague dinta ta barshi da niyyar idan ta gama abinda take ta kirata Ya kama handle din ya murda hadi da tura qofar ta bude ya shiga,qamshin freshner din parlour hadi da qamshin jallop din ya dunqule ya daki hancinsa wanda hakan ya sake haddasa masa yunqurowar wata matsananciyar yunwa,idanunsa suka kai kan plate din dake dauke da jallop din dake ta tururi da qamshi, Fadila ta fito hannunta dauke da wayar tana duba missed calls din data tarar ciki harda na rumasa'u da farida,,sam bata lura da shi ba agun sai da yayi gyaran murya,adan furgice ta dago don bata zaceshi ba,a dinke fuskarsa take kamar kullum ya cillo mata muqullai suka sauka a kusa da qafafunta,yayi gefe da kansa sannan cike da ginshira yace"ki gyara min bangarena sannan ki sama min abinda zanci yanzun nan tunda sai an koya muku abinda ya dace" ya nemi kujera ya zauna hadi da jawo wani dan qaramin table din na glass ya miqe qafarsa akai A hankali ta sunkuya ta dauki muqullan,cikin zuciyarta tace"ka gama qunbiya qunbiyarka ka ma,mutum sai shegen jin kai ka fito kawai kace kazo neman taimako guna,ki banza dai ina da muhimmanci tunda.duk cikinsu babu mai iya maka haka sai ni duk da dan banzan jin kanka"ta shiga daki ta canza mayafin zuwa hijabi sannan tazo ta wuce shi yana zaune yadda ta barshi Kamar jira yake ta fita din ya jawo abincin gabansa,ya dauki cokali mai yatsu yana jujjuyata yana qare mata kallo,a zahiri shi taliya bata dameshi ba don haka ya ture plate din gefe sai kuma qamshin ya addabeshi don haka dole ya jawo yakai loma daya bakinsa Lumshe ido yayi dadin na zagaya kunnensa ,ya tabbatar wannan ne taste din da yayi missing kwana da yawa kuma shi yake nema wasa wasa saiga gashi ya tashi da plate din gaba daya,ya shafa cikinsa take yaji yana buqatar qari bai qoshi ba, ya miqe ya nufi kitchen kasancewar tsarin ginin nasu daya ne shi yasa ya fahimci inda yake,ya daga tukunyar gaba daya ya juye ta ciki ya cinye ya dawo falon dauke da ruwan roba na faro a hannunsa ,sai yaji ya samu nutsuwa ba shakka yunwa bata da hankali inji dan almajiri Ya miqe a kan three sitter saboda yanaji har cikin zuciyarsa yanayin qamshi da tsaftar falon sunyi.masa,idanunsa a lumshe yana tunane tunane har aka fara kiraye kirayen sallar magariba sannan ya miqe ya bar sashen,kafin ya qarasa nasa suka ci karo da samirah na shigowa da motarta,ya tsaya qam yana dakon qarasowarta hannunsa zube cikin aljihun wandonsa,tunda ta hangoshi tace da qawarta sa suka shigo tare "na shiga uku kubra mai gidan nan ya dawo"kubra da hankalinta ke kan waya ta ja tsaki tace"mtswee to sai me?ni wlh samira mamaki kike bani tunda.kika yi auren nan duk kin canza komai adarare duba fa dazu da zamu fita fitted gown fa kawai nace ki saka amma kika qi bayan kinsan gun manyan mutane zamu ji,tsoron mutumin nan kike ji kamar wani Allahn ki ke yadda ma kike tsoronsa baki tsoron Allahn naki ma,nidai gwara ma dai yau naga wanne dan mulkin nan ne wannan da.kike masa biyayya haka kamar shi ya tsuguna ya haifoki Cike da gadara da rashin kunya kubra ta fito yayin da samira keta.rabe rabe don kuwa riga da skert ne a jikinta na shadda kana kallon shaddar kasan an kashe mata naira mai tsada ce saidai anci mutuncinta ta wajen kacalcalata da yi mata matsatstsen dinki,ga mayafin jiki ta sai kace wadda aka yiwa gorin lullubi Kallo daya ya yiwa kubra da ta tsareshi da ido duk wata rashin.kunya da ta fito da ita tayi nata gun,hakanan aliyu yake Allah ya bashi baiwar kwarjini masifa,ta sake kallonsa karo na biyu"wow"ta fadi a hankali don gaba daya ya tafi da tunaninta,sai ta mance mission din ta fito da shi,ta zuba masa ido gaba daya,sai a lokacin idonsa ya kai kanta bayan ya dauke kansa daga samira,takaici ya kama Aliyu ganin irin kallon qurillar da take masa ya sake dinke fuska tamau,sai lokacin ta kula da ta bada kanta fa ashe, Ta dauke kai cike da duniyanci da niyyar bin bayan samira dake ta zuba sauri jiki na rawa,tsawa ya daka mata hadi da nuna mata qofar get sannan yace"get out of my house idiot kada na kuma ganin wadannan lalatattun qafa fun naki a gidana"murmushi ma ta saki ta juya ta fice cikin karairaya wai ko zata janyo hankalinsa, bata san wani takaicin ne ya sake qumeshi ba yaja wani dogon tsaki ya juya ya nufi sashen samira Mrs muhammad 3:37 pm 8/11/1437 *wa yasan gobe?.....* Kubra ta tsaya a bakin get din tana jinjina kai ita daya take sumbatu"kut lallai yarinyarnan dole ta matowa gayen nan shi yasa take ta faman rawar qafa?ai kuwa wlh baza'ayi bani ba"tayi qwafa sannan ta ja