← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 84

Sashe 36

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

kice har an fara boyonki lallai soyayya ruwan zuma"fadila ta harareta tace "wlh badan kin mun abun kaiba kin bani baby mai kama da ni ba da sai na bubbuge bakinki"su amina suka qyalqyale da dariya sannan suka miqe suka ce bari dai mu baku guri kada a buge mana anti a gabammu"dariyar suka bawa fadila su kuma suka fice kitchen gun inna jummai Fadila ta sake zubawa yarinyar ido tubarkallah masha Allah qatotuwa da ita lallai kam wannan photo copy dinsu ce ta kalli farida tace sister sannu"farida ta ya da kai gefe tana tuno wuyar da ta sha"hmmm ke dai bari sister ansha gwagwarmaya ni kam dan ba qara"fadila ta sake rungume yarinyar a qirjinta tana sake jin qaunarta na shigarta bata qi ace tata bace,ta saki dariya tace "yanzun fa aka fara farida me akai da maza daga ihu daya sai kuma murya ta dashe? "ta qarashe ta sigar tsokana yau dai ta maida raddin tarin tsokana irin na farida da take mata ko yaushe,ko da can dama fadila Allah ya zuba mata son yara,sanda suka tashi muhammad ne kawai yaro a gidansu to har gidan maqofta take shiga dauko yara duk da yanayin unguwarsu irin unguwan nin nan ne da ba ruwa na da kai kowa na qulle shi da ahalinsa cikin gida amma haka fadila ke shiga ta taho da su,miskila ce ako ina magana bata dada ta da qasa ba amma banda kan yara hakanan zaka ga ta sasu a gaba suna ta wasansu,farida kam dama idan taga dama idan suka zo neman anty fadila sai ta korasu tace bata nan zasu zo su dameta ne Farida ta girgiza kai da sauri tana juya ido tace "kai sister is hardly in sake ko zan qara sai after five to ten years,nikam na barmiki ki taba kiji"dariya ma ta bata ganin duk yadda tayi laushi duk rashin tsoro da dakiya irin na farida,murmushi fadila tayi tana ci gaba da kallon yarinyar tayi kissing dinta agoshi,"ina aliyyu ne sister?" af yana waje " farida ta miqe daga kashingidar da tayi tace "kada dai kice mun kuna tare yaushe ya aliyyu boss ya fara kai matarsa unguwa"fadila tace"saboda ya bata min ya fara ta kaina yau kina gani fa kamar gidqn nan yace min wai twenty minutes?"farida tace "wlh am serious ya aliyyu ko salima matarsa ta farko bai taba kaita wata unguwa ba idan ba monthly shopping naku ba(farida ta fi fadila sanin halinsa ne kasancewar tq fita shiga jama'a hakanan ta fita zuwa gidan uncle abba)kuma shine kika barshi a waje ga sitting room nan"fadila ta tabe baki tace "oho masa har get malam salisu ya bude masa yace a maida arufe ba shigowa za su yi ba" "gashi mubarak yanzu ya fita maida hajiyarshi gida da ya shigo da shi"farida ta fada tana lallatsa wayarta,"zancan kike so ki bar mubarak kada ki taso shi idan da rabon zasu hadu zasu hadun don ko mubarak ya zo idan bai ra'ayi ba bazai shigo din ba" Minti goma sha biyar ta shude suna ta hirarsu farida na cin tuwonta a sake kasancewar su mariya sun bar masu dakin,dahiru yaron dake wa farida aike aike ne ya shigo karbar abincinsa bayan ya miqawa inna jummai kwanon ya tsaya bakim falon faridan yace"anty wai baquwa ta fito za su tafi"fadila ta bata rai don tasan aliyyu ne yayi aiken kuma aqa'ida tana da sauran minti biyar Ranta a bace bayan ta bude camera din wayarta ta yiwa baby pic ta sake sumbatarta ta ajjiyeta gefan faridan ta dubeta tace sister zan dawo insha Allah me kikeson na kawo miki"murmushi tayi tace"sister fadila nayi missing din wainar shinkafarkin nan da kike mawa dady,idan zan sameta inaso"dariya fadilan tayi saboda ta tuna mata lokacin da suna gidan idan tayi insha Allahu kan ta gama shiryawa Abban a warmer taci na ci kuma ta bi ta har falon abban suci tare da shi tana hara rarta tana komai amma sai tayi biris,"insha Allah kamar kinci waina ta kin gama"sukayi sallama tamkar kada su rabu Tana fita taga motar mubarak fake kusa da tasu shi dinne kuwa da alam yanzun ya iso don lokacin suke gaisawa da aliyyun ta qaraso suka gaisa ya juya yayi cikin gida yana cewa bari ya dauko ma aliyyun babyn ,hannu biyu yasa ya dauki babin mubarak na gyara masa riqon don da gani bai iya ba,ya riqe ta sosai yana kallinta hadi da fadin"masha Allahu la quwwata illa billah"(yan uwa gaka annabi ya horemu da fada a duk lokacin da muka ga wani abu da ya qayatar da mu to ko kana da kambun baka bazai kama abun ba domin wasu ma auna da shi amma basu san suna da shi din ba,sai kaga abu kayita kodashi ba tare da ka fadi hakan ba daga qarshe sai wani ibtila'i ya saukarwa abun ya lalace don Allah mu kula da wannan) Fadila na satar kallonsa kadan kadan tana kallon yadda ya zubawa yarinyar ido ya lumshe idanunsa daga baya ya budesu ya sumbaci goshin yarinyar sannan ya miqawa mubarak ita yana sake cewa Allah yayi mata albarka,ya amsheta sukai sallama ya shige gida da babyn Aliyyu ya yafito qasimu dake fitowa fitowa daga gidan hannunsa da robar abinci qasimu ya qaraso hadi da rusunawa aliyyu ya amshi bandir din kudin dake hannun nasiru ya miqawa qasimu yace ka kaiwa maman baby ya zaro 1000 daga aljuhun trouser dinsa ya bashi ya shige motar yabar qasimu nata zuba godiya yare da komawa cikin gidan don sada saqon aliyyu ya bawa nasiru umarni ya tada motar suka bar layin fadila nata satar kallonsa don kiwa dubu dari ce ya bayar a kaiwa babyn Mrs muhammad ce 2:08 pm. 24/08/2016
Chapter 36 · 0% Book details