← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 84

Sashe 49

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuka?"ya qarashe maganar da sigar tambaya Ita dai babu abinda tace,kusan minti biyar shiru ya ratsa falon hawayenta naci gaba da silalowa shi kuma yan ci gaba da kallonta yana jin 2ani abu kamar ya zaqe da yawa why?,a hankali ya juya yana barin gurin hadi da cewa "silly girl" Abincin da bai iya ciba kenan a ranar ita da kanta kuma sai taji bubu dadi,koma mene tasan batan ta ne ya bata masa rai shi kuma ya jawo mishi,da bacci ya dauketa ma kan kujera da asuba anan ta farka ta ganta bai tashe ta ba kenan *mrs muhammad ce* [10/16, 1:59 PM] Salma *WA YASAN GOBE?..* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 2* Kwana uku tsakani tana zaune ya kawo mata foam ,gefan ta ya ajjiye bata san na mene ba sai da ta bude sannan ta duba sosai ta gani ashe na wata instute ce, sabon corse ne kan aikin jarida zasu fara wata uku ne kacal za'a kammala,daga qarfe goma na safe zuwa daya na rana,zaka iya attending classes dinsu kokuma ka dauki lecture din online kana daga gida Tsalle ta dinga yi cikin murna bata san aliyyu na tsaye ba qofar kitchen ashe ita ya zubama ido,a hankali suka hada ido tayi saurin komawa ta zauna kunya ta kamata shi kuma ya ya dauke kai ya shige kitchen din,a nutse ta dinga cike foam din har ta kammala da maida cikin envelop Sosai fadila ta soma jin dadin karatunta duk da online take daukan lecture ko yaushe tana gaban computer din ta,koda ta kammala daukan lecture sai tayi zamanta tayi ta research,tun daga lokacin da abin ya faru itama bata sake gigin fita ba,iyakacinta gidan nadiyya ita din ma ba sosai don gidan mr lin ma sau daya ta taba leqa mata,sai dai su turo mata yaransu suyita taya ta hira don ma bata gane yaren nasu tafi hira da mashkur don ya iya yarensu na larabci sosai Zaman garin yanzun bai fiya takurata ba sosai tun lokacin da ta fara daukan lecture dinta,sosai computer din ta sake zama abokiyarta shi kansa uban tafiyar ya lura da yadda gaba daya walwalarta ta koma kan laptop dinta,haka nan sai ya soma jin haushin computer din gani yake kamar ta tsare masa wani abu da ya rasa mene shi gaba daya bata da wani sukuni sai ta zauna a gabanta Shi yasa wani lokacin da zarar yaga ta dauko da niyyar yin karatu sai ya tsiro wani aikin na babu gaira babu dalili,cikin zuciyarsa yake gulmar "reading like machine"karatu kamar ranta,(hmmm kaji fa gwano baijin warin jikinsa shi da yake wuni zirga zirga da kai kawon bude company dinsa) Kamar kullum yauma tara daidai ta kammala dukkanin ayyukanta sabida goma zata zauna lacture,tana sanye cikin kayan sanyi na turawa ta yane kanta da dan qaramin hijabi fari tas iya kafada,shigar orange and white tayi sai ta haska chocolate colour skin dinta,tana tsaye a dining area tana zuba masa farfesun kan rago cikin plate ta hada masa tea cikin cup don ya dan sarara kafin ya fito Taa cikin rufe flask dinne taji takun tahowarsa ,a dabarance ta saci kallonsa ta gefan ido cikin rashin sa'a ya kamata,da sauri ta dauke idonta ya qaraso dining din ya jawo kujera daya ya zauna hadi da dora briefcase dinsa a dayar ya ajjiye wayarsa kusa da cup din tea ,itama kujerar ta ja ta zauna kamar yadda yakeso kenan idan zaici abinci( hmmmm) Ta sake satar kallonsa a karo na biyu suka sake hada ido "hold on ur sight"ya fada yana kai cup din bakinshi,sai ta danji kunya ta kamata duk da shi din ma tasan satar kallon nata yayi har suka hada idon,tsakanin jiya da shekaran jiya zuwa yau gani take mood dinshi ya canza,duk da dama bawai mai fara'a ne ba amma taga sauyi cikin walwalarsa da kuzarinsa,hakanan ayyukan da yake tahowa da su yayi ta lodawa cikin laptop dinsa ya ragu sosai Haka nan cin abincinsa ya ragu daga kusan kaso saba'in cikin dari,cikin ranta take ganin bata da wani matsayi gurinsa bare tayi gigin binciken meke damunsa,kamar yadda ta zata kuwa tea din kawai ya shanye ya miqe yana rataye jakarsa ya kuma ajjiye mata yuan 100 kamar yadda ya saba,a hankali yake saukowa daga daga step din dining area din kamar mara laka Tuni qamshinta yayi masa rugu rugu da gangar jiki da kuma zuciyarsa,babu abinda yake buqata a yanzun idan ba mace ba koda samira ya samu ayanzun zai iya maleji da ita,har sai da ya fice sannan ya kauda kanta daga kallonsa ta maida idonta kan table din inda ta hada kayan break,tea kawai itama ta iya hadawa ta sha ta kwashe kayan ta gyara gun takai kitchen ta wanke ta dawo kan computer dinta don yin karatun Qarfe daya da mintina goma sha biyar ta kammala ta rufe laptop din,ta danyi miqa irin ta gajiya tana yar hamma,ta jawo wayarta ta dan duba saqonninta na watsapp na tsawon minti arba'in sannan ta sauka,sallah ta soma yi don biyu tayi sannan ta kwaba alkubus don shi ta shirya yi yau Tana tsaka da aikin nadiya ta shigo nan ta zuba ido tana mamakin me fadilan ke hadawa haka?,dariya fadila tayi tace irin abincimmu ne Sai qarfe uku nadiyan ta tafi fadilan ta rakota bakin qofa tana gaya mata idan ta gama zata ta turo mashkur ya karba mata taci taji,ta saye qofar falon ta koma kitchen din fara aikinta,ta kammala komai da wuri ta gyara gurin ta koma bedroom don daura alwalar sallar la'asar don har tana qoqarin subuce mata Turus ta ja ta tsaya ta kuma saki baki,jakarsa da rigar suit dinsa na watse saman sofa shi kuma na kwance saman gado ko takalmin qafarsa bai tube ba,cikin mamaki take satar kallonsa tana mamakin yaushe ya shigo gidan don ko alamunsa bata ji ba,kuma ma mainya dawo da shi gida a wannan lokacin Rabawa tayi ta shige toilet ta dauro alwalar ta fito ta dauki abun sallarta ta koma falo,bayan ta idar ta koma saman kujera ta zauna sai dai hankalinta ya kasu rabi na kan t.v rabi na bakin qofar bedroom din don har yanzu bata ji motsinsa ba Hankalinta ne ya gaza kwanciya cikin sanda ta miqe ta tura qofar tana leqen saman gadon,har yanzu a kwance yake kamar yadda ta barshi,ta qarasa bude qofar gaba daya a hankali cikin sanda ta qarasa bakin gadon ta duqa ta kama qafarsa a hankali ta zame masa takalman bai motsa ba har ta gama cire masa sai tayi tsammanin bacci yake ta sabule masa socks din ta cusa cikin takalmin ta kwashe su ta maida su muhallinsu Ta juya zata fice ta sake waiwayowa kalleshi idanunsa na lumshe kan hancinsa yayi wani ja irin na farin mutum kamar an murza gun,ta kauda kai ta fice daga dakin,duk abinda take yana kallonta idanunsa biyu,matsanancin zazzabi da yake ji da ciwon ciki mai azaba wanda ya jima rabonsa da shi shi ya hanashi koda yin motsi,yasan yadda ciwon cikinsa yake idan ya kamashi baya masa ta dadi,sai yaji dadin yadda ta sake dawowa ta dubashin ganin bai fito ba,ya tabbata kasa nutsuwa tayi da rashin ganin bai fito din ba Sai da ta shigo daura alwalar sallar magariba sannan ta ganshi zaune kan abun sallah a side din gado duk da bata ga fuskarsa ba kansa na aduqe,ta sake wucewa tayi alwalar Qarfe tara na dare zaman falon ya gundireta ita daya kamar mayya,sabo mugun abune zaman da sukeyi tare duk dare shi ya sanyata kewa ganin yau babu shi duk da ba wani zaman da za'a fadeshi bane kowa harkar gabansa yake duk da da zarar daya yayi wani motsi mai qarfi zaka ga hankalin dayan yayo kansa Sai da ta hada masa coffee ta hada harda abincin cikin babban tray guda daya don har lokacin bai ko leqo koda falon ba bare yaci abincin nasa,ta dauka bayan ta gama shirin kwanciyar ta cikin night gown riga da wando ne wandon har qasa rigar iya gwiwa cotton ne very soft sai hijabi saboda sanyi *Mrs muhammad ce* 3:54 pm 5/09/2016 *WA YASAN GOBE?..* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 2* Ta ajjiye tray din kan bed side tana tunanin ina ne makwancinta yau kuma?,saboda aliyyu na kwancene a kai crossing gadon,bata jin kuma zata iya kwanciyar qasa yadda shi yakeyi domin matsanancin sanyin garin ya girmi qashinta,ta kuma kallinsa karo na biyu yana duqun qune cikin bargo gaba dayan jikinsa kansa ne kawai a waje Sai ta rasa ta yadda zata tada shi tafi qarfin minti goma ahaka kafin dabara ta zo mata,gyaran murya ta taqarqare ta ja har aai da maqogwaronta yayi mata zafi,a hankali ya bude idonsa ya zubesu fes kan fuskarta tsakiyar qwayar idonta,fadila ce ta soma janye nata qwayar idon tana jin wani magnet na fusgarta,tabbas ba don aliyyu mutum bane zata iya cewa wani mayen qarfene cikin idonunsa da duk sanda ta kalla yake fusgarta,cikin ranta taje mamakin yadda fareren qwayar idanun sa kar suka rine zuwa ja Cikin jikinta ta soma jin anya lafiyar aliyyun qalau?,ta kawar da wanna tunanin tana ji a jikinta har yanzu ita aliyyu yake kallo, "na zuba maka ne abincin?" Can qasa ta jiyo shi yace " I don't need",ya maida idanunsa ya lumshe,ta kuma kallon nasa tace "but...." "leave me "ya fada can qasan maqoshinsa cikin katseta,ta ga alamun bai da lafiya ne don haka bata yi zuciya ba tace masa "please ko coffee ne kasha mana" shiru yayi kusan minti uku baice komai ba,hakanne yasa ta gane ya yarda Ta jawo flask din ta tsiyaya masa rabin cup din sannan ta sake matsowa kadan yadda zataji dadin miqa masa "take it pleas",da qyar ya iya miqewa ya jingina da makarin gadon,ta sake miqa masa yasa hannunsa zai amsa ya hade da hannun nata,kamar bashi ya riqe mata hannu ba bai saka ba bai kuma ce komai ba Wani shocking take ji ga kuma dumin zazzabin jikinsa da yake ratsa ta itama,sai lokacin ta sake tabbatar da ashe bai da lafiyar,a hankali ya zame mata hannun sannan ya riqe cuo din sosai ya sale maida idonsa yaumshe kamar ba zai sha ba,illar da turaren ke masa nada yawa haka
Chapter 49 · 0% Book details