Sashe 55
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya duba kitchen,shi yana nan kamar yadda ya barshi da safen babu wani abu da ya canza,sai ya sake komawa bedroom din yana bawa ransa tana toilet to Gefan gadon ya zauna yana zaman jiranta wanda daidai yake da a kirashi da zaman jiran gawon shanu,har sai da ya dan soma qosawa ya miqe bayansa sama gadon fuskarsa na kallon ceiling,sai yaji qayau qayau kamar ya kwanta kan wani abu,yasa hannun nasa qasan bayansa ya zaro ta yadan jujjuyata sai ya wullata daya gefan gadon,ya mirgina kansa da niyyar duban qofar toilet din sai idanunsa suka sake kaiwa kan takaddar,sai ya tsinci kansa da son budeta yaga mene a ciki don bata barin komai saman gadonsu Yana daga kwancen ya jawota ya warwareta yakai idanunsa ciki ganinta cike taf da rubutu ya bashi mamaki,paragraph din farko kawai ya karanta sai gashi zaune dirshan tsakiyar gadon ba tare da ya san yaushe ya tashi ba,kafin aliyyu ya kammala karanta saqon tuni ya jiqe da gumi duk da ragowar sanyin dake qasar ta sin,ya kammala karanta layin qarshe na takardar gami da cukuikuyeta cikin tafin hannunsa da qarfi,rawa kawai jikinsa yake tamkar sojan da aka bugawa kugen yaqi,launin idanunsa tuni sun canza daga ainihin fararen nan qal masu haske zuwa jajaye,babu launin na alamun tashin hankali a lokacin da bai bayyana bisa fuskarsa ba,tsananin tashin hankalin da yake ji a lokacin bazai misaltu ba "why?why fadilah?me yasa kika yimin gurguwar fahimta?,me yasa kika fahimceni a abaibai?,ina zaki tafi?ina zaki tafi ki barni?,ba haka bane fadilah....ba haka bane abinda kike zato"shi kadai keta wadannan sumbatun ya dunqule hannayensa cikin junansu takardar na tsakiya Wurgi yayi da takardar,tamkar an zungureshi ya fice daga dakin cikin matsanancin sauri,"ina zata yanzun?batasan kowa ba cikin qasar? " Tambayar daya takura yake ta faman nanatawa kansa ita bayan yasan shi kansa ba sanin amsad yayi ba,yana gab da fita a gidan wani tunani ya fado masa,cikin zadin nama ya juya ya koma ,kai tsaye inda yaga passport dinta shekaran jiya ya nufa ya hau dubawa wayam baya gurin,cikin zafin nama ya juya ya fice daga gidan,taxi ya tsayar ya shige shaf yama manta da cewar ana gayawa mai abun hawa inda za'a,gani yake ma tamkar taxi driver din yasan inda zai kaishi, saida yayi ta nanata Tambayar inda zai kaishi sannan ya tuna ya gaya masa airport zasu je Safa da marwa take cikin departure din,hankalinta a tashe yake gani take tamkar aliyyu zai biyota ne ya hanata tafiya,wani bangare na zuciyarta ke tunatar mata babu yadda za'ayi aliyyun ya biyota,abunda kake qauna shi kake nunawa kulawa da damuwa da halin da kake ciki,koda sace ta akayi bata tsammanin aliyyun zai biyo sawunta bare tafiya tayi da qafafunta,duk da haka hankalinta bai kwanta din ba sai da suka hau layin shiga jirgi,ko anan din ma bata fasa sharar hawaye ba,sam bata damu da yadda jama'ar keta kallonta ba har wasu kan gaza shiru suce mata "sorry" kallon da suke mata bai dadata da qasa ba don ji take tamkar ansa mata wani hijabi ne cikin zuciyarta,tuni kowa ya kama sit din sa ya zauna tana sit 34 A,sanarwar daura belt ta biyo baya bayan an rufe qofar jirgin,a lokacin ta tuna tahowarsu da aliyyu qasar ranar da ta kasa daura belt dinta,kuka ne sabo ya sake qwace mata *kukan baqincikin rabuwa da shi ne ko kuma na farincikin rabuwa da shi ne?kukan shaquwa ne ko kuwa na kewa ne?* oho ita kanta bata sani ba,ita dai kawai ta tsincin kanta tana yinsa,a hankali jirgin ya soma qugi yana motsawa sannu sannu har ya ware sosai ya fara shawagi kan kwaltar dake doron qasa Ko ta kan security dake ta tareshi da tambayoyi bai bi ba har sai fa ya dangane da inda yake son zuwan,duk ma'aikatan gun suka miqe saboda girmamawa don tuni garin na guangzhou ya soma gane wane aliyyu cikin qasar ta sin,sanarwar bikin bude katafaren kamfaninsa ya riga ya karade ko ina cikin qasar,cikin sakanni qalilan ya basu umarnin duba masa list na sunayen mutanen da suka tashi zuwa Nigeria tun daga safe zuwa yanzu,girmansa yasa suka masa haka don kuwa ba kowa ke samun haka ba sai idan jami'in tsaro ne da kyakkyawar shaidar neman wani mai laifi Tafi yafi har suka zo list din qarashe wanda suka sanar masa jirgin yana daf da cillawa sama,daga qarshe sunan fadila Abbas Bashir ya bayyana,cikin azama ya dakatar da su yana fadin"mai wannan sunan nake nema" "ai tana cikin wadanda jirgi zai daga da su nan da yan sakonni" cikin sauri ya tashi yana fadin yana son a dakatar da tashin jirgin,cikin girmamawa yace "sorry sir bazai yiwu ba mun riga mun gama handling din komai,duk ma'aikatan mu sun san da tashin nasa,haka na qasar da zai sauka" da qarfi ya doki sama table din cikin zafi yace " I said stop the flight now!!!" Ya sake rusunar da kansa yace "sorry sir it can't,but idan kana buqatan tafiya zuwa nijerian ne sai amaka printing ticket" Ya harde hannayensa a qirji ya lumshe ido yana maida numfashi,shi kadai yasan yadda zuciyarsa ke masa zafi da quna,shiru yayi tamkar baza ya furta komai ba "hasbunallahu wa ni'imal wakeel" yake karantawa cikin zuciyarsa,a hankali ya soma jin temper din na nasa na raguwa,still idanun nasa na alumshen yace"ok ina son jirgin da zai kuma tashi anjima" "sorry sir yau babu jirgin da zai kuma zuwa nijeria" "gobe da safe " "sai da yamma sir" "noooo!!!" Ya fadi sa qarfi hadi da bude idaunsa wadanda suka kuma zama manya ya ware su sosai kan ma'aikacin,ya sake dan rusunar da kansa gami da cewa"sir sai da yamma kayi haquri"shirun ya sake yi yana ci gaba da kallonsa,cikin ransa yake dana sanin rashin mallakar jirgi na kansa da yaqi yi a baya bayan yana da damar hakan,sai da ya gaji don kansa sanan ya sanya hannu cikin aljihunsa ya fito da kudi wanda baisan nawa bane ya ajjiye masa,ya miqa masa ticket sannan cikin sauri ya irgi kudin su ya muqawa aliyyun sauran saboda gudun kada ya karya dokar qasarsa,wani irin wawan kallo aliyyun ya watsa masa wanda ya sashi janye hannunsa shi kuma ya fice abinsa Tafiya ce mai tsawo tamkar a zuwan ta kawosu airport din addis ababa,hamdala tayi da taji cewar nan da awanni biyu jirgi zai sake kwasarsu ya miqa su nijeria kanon dabo babu batun kwana kenan a ethopia,hakan yayi mata dadi sosai don burinta kawai shine ta bude idanunta ta ganta cikin nijeria zuwa lokacin idanunta sun sake yin luhu luhu saboda kuka wanda ta kasa tsaida shi Qarfe takwas na dare agogon nijeria jirginsu fadila ya landing cikin aminu kano international airport,sannu a hankali passengers suka soma saukowa,tun sanda suke kusa da sauka ta soma tunanin ina zata nufa?gata dai a nijeria?,ba zata nufi gidansu ba ko giyar wake ta sha,ta sani idan dai har taje din babu shakka babu ruwan abbanta ko umminta zasu maidata ne gidan aliyyu hankali kwance,ta tabbata ko ta bakinta ba zasu buqaci ji ba,bayan ta riga ta yiwa aliyyu da ita kanta alqawarin yanke zamansu,ta masa alqawarin yin nesa da rayuwarshi,a yanzun bata da muradi ko digo kan ci gaba da zama da shi *"ta inda aka hau ta nan ake sauka"* haka zuciyarta ta gaya mata,take ta amince da batun zuciyar tata,ta yiwa daya daga cikin direbobin airport din magana kan inda zaya kaita,take ya amince tare da tsula mata kudi,bata damu ba ko a duska din ita ba wannan ne a gabanta ba,ba ta wannan take ba ta kanta kurum take yi Har a lokacin hawaye bai daina bin fuskarta ba kamar yadda bata fasa gogeshi ba,har ta soma jin babu dadi saboda kukan da take,har qofar get din gidan mai taxi din ya ajjiyeta,ta fidda kudinshi ta bashi,unguwar ba kowa shiru kasancewar haka yanayinta yake koda da rana ma balle dare,ta qarasa ta qwanqwasa get din,mai gadin ya yaso yana tambayar wane? dare ya soma a lokacin don tara ma ta gota,"nice" ta amsa masa bai dai gane wace din ba har sai da ya leqo ta 'yar qaramar qofar dake maqale jikin get din,cikin rawar jiki ya soma ture wagegen get din yana fadin sannu da zuwa hajiya,ga tsammaninsa a mota take,shigewa kurum tayi ta ajjiye masa dari biyar canjin da mai mota ya bata bisa bencinsa tana cewa "rufe get dinka bada mota nazo ba"yawan kyauta da fadila ke dashi yasa yake daukin zuwanta din bata taba ahiga ta fita bata yi musu ihsani ba Tana shiga anty hauwa na fitowa daga kitchen da yake qofar shigowa falon opposite qofar kitchen din ta ne na qasan,hannunta dauke da food flask guda biyu,baki ta saki galala bayan ta tsaya cak tana kallon fadila,har ta bude baki zata yi magana sai ta lura da yanayinta a hargitse taje ba kamar yadda ta santa ba ba lamaun nutsuwa tare da ita,mamakinta yaushe suka dawo daga china babu labari?,kan tace komai din fadilan ta share wani qwallar "subhanallahi" anty hauwa tace ta qaraso da sauri ta dire flask din saman kujera ta kama hannayen fadilan tana fadin "lafiya fadilah?"a rude,"daga ina haka?" "Daga airport nake anty" ta bata amsa murya a dashe Bata kuma cewa komai ba don tasan ba lafiya ba ta ja hannunta suka bi ta wani dan madaidaicin corridor dake hannun hagun falon,dakunan bacci ne ciki guda uku,daya na baqi wadanda baza'a kaisu boys quarters ba daya na yaranta wanda du sun kwanta bacci kasancewar da wuri take sasu suna yi saboda makaranta,daya kuma nata ne duk da ba kwana take ciki ba sosai ko yaushe suna sama a tare da mi gidan ta saidai idan yayi tafiya ne,ta tura qofar dakin suka shiga tare,daki ne mai kyau kamar sauran dakunan bakin gado ta zaunar da fadilan hadi da cewa"kiyi wanka kiyi sallolinki,nasan cewa ba lafiya ba lo baki gayamin ba"ta miqe ta fita jim kadan ta dawo dauke da wani cooler madaidaita guda biyu na baincin daya hannun nata kuma sabuwar abaya ce ta ajjiye mata,"ga abinci kici,ga kaya ki sauya don kifi jin dadin jikinki,zani na sallami abbansu kausar right?"ta qarashe da tambayar fadilan,kai kawai ta gyada mata kamar qadangaruwa a sanyaye anty hauwan ta juya ta fice Cikin abinda anty hauwan