← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 84

Sashe 65

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jima tana bege da yaqin samu gashi yau a gabanta,yau ga aliyyu zaune dirshan a gabanta,yauga aliyyu zaune ya zamo kalar tausayin a qasan qafafunta,bayan babu abinda ya rasa a rayuwarsa soyayyarta kawai yake nema,aliyyun nan dake bata tsoro,aliyun nan dake da girman kai aji da kuma kwarjini yaushi yake roqon soyayyarta?,to itakam idan bata sallama ba tayi haqurin ai ta yiwa Allah butulci,me take nema dama idan ba wannan din ba?,tasan wasu daga halayensa sarai kamar yadda kowa ya shaideshi bai iya qarya ba....shi din kaifi daya ne da ko gaskiyarsa ba zata faranta maka ba hakan bai dameshi ba Cikin cool voice da wani irin kunya da nauyi kanta a qas tace "na yafe maka,komai ya wuce "lumshe idanunsa yayi wani sanyi na kwara cikin ransa,ji yake kamar an masa gafara da bushara da aljanna,me yafi so dadi?,me yafi qauna faranta rai?,amma duk da haka yana neman qarin bayani,ya bude idanunsa ya sake matsowa jikin gwiwoyinta,"fadeelah kalmomin da zan miki godiya da su na tabbata sunyi kadan,bani da su saidai na kwatanta yin hakan don bani da abunda zan iya saka miki da shi,na gode na gode Allah ya miki sakamako da aljanna,but I need more fadeelah I need more,please tell me kina sona kina qaunata kuma zaki koma gida na"kafin tace komai aka sake knocking,da sauri ta daga kai ta kalleshi "please ka tashi daga qasa ka koma kan kujera,za'a iya shigowa a ganka a haka fa" ya noqe kafada ko matsawa baiyi ba yana ci gaba da kallonta "no,I don't care ko waye ma zai ganni a haka,a gaban fadeelah ta nake kuma ta cancanci komai har ma fiye da hakan,idan tana sone ma na kwanta ta dinga taka gadon baya na tana tafiya am ready if I can make her happy"dariya ce ta subuce mata tasa tafin hannunta tana qunshe bakin,ya kalli qwayar idanunta da suka sake yin kyau da 'yar ragowar qwalla aciki wadda tasa shi ya koma kamar oily eyes ya dage girarsa "oh,kina tantama ne?,let me show you"tuni ya soma qoqarin ruf da ciki a qasan,batasan lokacin da ta kama hannunshu ba tana qoqarin hanashi ba"no haidar,I trusted you"yabi hannayen nasu da kallo yadda ta riqe masa hannu da tattausan hannunta,ganin yana kallon yadda ta riqe shin sai kunya ta kamata tayj saurin janye hannun hadi da yin qasa da kanta tana murmushi,shima murmushin yake sannan ya nufi bakin qofar ya bude,fauziyya ce har ya dawo tace cikin fara'a "ina fatan kun kammala ban sake katse ku ba karo na biyu duk da takaddu kawai na shigo diba zan wuce gida"yasa hannu ya dauki baby iman dake ta miqa masa hannu taba masa dariya tamkar dama can ta sanshi ya soma mata wasa,baice mata komai ba sai hanya da ya bata yace"bismillah" Yana ji tana tsokanar fadila haddi da yi mata sallama "yau dai ban sani ba ko anan office din zaku kwana ke da ogan" cikin murmushi ta mayar mata "a haba fauziyya,gida za muyi yanzu muma"ya sauke mata iman hadi da zurawa yarinyar five thousand cikin awarwarayenta dake hannunta,yaro ba wayo sai kallon kudin take gami da qoqarin zarosu tana ganinsu kamar abun wasa ne,yana ta murmushi son yara na dada kamashi,fauziyya ta masa godiya,shi ba ma'abocin son ayi masa godiya bane don yayi kyauta don haka baice komai ba ya dauke kansa ya maida kan fadeelah dake qoqarin miqewa don hada kan komatsanta da niyyar tafiya gida,wani jiri ya debeta duhu ya gilma idanunta tayi baya luuuu zata fadi,cikin zafin nama ya qaraso gareta ya mata kyakkyawan masauki cikin faffadan qirjinsa yace "subhanallah",fauziyya dake yunqurin jan qofar ta dakata gami da juyowa "sannu fadila jirin ne dai?" Da mamaki a fuskarsa ya kalli fauziyyan "dama jiri take yi?" "Wallahi tunda ta dawo aiki take fama da shi,kullum haka take yi,matuqar tayi dogon zama ko zirga zirga,nayi zaton ma ta gaya maka,don nayi nayi da ita taje taga likita sam taqi,don ko jiya sai da na dan riqeta na wasu mintina sannan ta zama normal" "Thank you" yace ya maida idanunsa kan fadilan wadda ta sake cusa kanta cikin qirjinsa tana shaqar daddadan qamshin da jikinsa keyi,dadi qamshin ke mata sosau kamar su dawwama ahaka haka take ji,maidata yayi ya zaunar saman kujerar ya hada mata dukkan takardun da take buqata din cikin hand bag dinta ya dauka sannan ya zo ya miqar da ita ya rungumeta ta kafadarsa yadda zasu iya tafiya a hakan *ku yimin afuwa makarata rashin chargy* *Mrs muhammad ce* [10/16, 2:14 PM] Salma *WA YASAN GOBE?....* *WRITTEN BY SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *PART 3* Ganin ya nufi qofa alamun ficewa za suyi ya sanya fadila zaro ido "a haka zamu fita?" Ya dubeta "yes ko yayi miki kadan na daukeki ne?" Ta kuma zaro ido cikin marairaicewa tace "no,please ka cika ni ka ban jakar,ai na daina jin jirin zan iya tafiya da qafata" Girgiza kai shima yayi"no,bazan iya barinki ba,bazan bari kisha wahala ba indai ina tare da ke,ko ki bari mu tafi a haka ko na daukeki gana daya na kaiki har cikin motar" Ta san halin aliyun kadan ne daga aikinsa,zai iya aikatawa ba tare da yaji ko dar ba,tilas tayi shiru suka fita tana sunne kai Motarsa taga ya nufa da ita,ta dago da kanta tana ce masa "amma da ka bari tunda a motata na zo sai na koma aciki ko?kada momi ko uncle abba su gammu tare" Ya tabe baki sannan ya saki dan qaramin murmushi dake qayata fuskarsa "kada su gammu tare?,so what?,ai ni dama haka nake so,kinga daga nan sai su tarkata min mata ta mu koma inda muka fi wayo"murmushi ta saki ta maida kanta don dariya aliyun ya bata,ya bude mata gidan gaba kusa da shi sai da ta shiga ya dan kwantar mata da kujerar ya sumbaci goshinta duk tana kallonshi "ki zauna a haka don bani so a ganemin ke a hanya"murmushi kawai tayi cikin jin kunya,cikin zuciyarta tana cewa"idan banda abun sa wa zaya ganni mota duk baqin glass"ya zagaya nasa bangaren ya bude yana shirin shiga Wasu 'yammata su uku suka fito daga reception,daya daga cikinsu ta finciko hannun dayar tana nuna mata aliyyu,damar da ta jima tana neman kena taga aliyun don haka ta jawo hannunta ta rakota har bakin qofar motar,yana shirin sanya qafarsa yaji ance "ranka ya dade ya kai kyakkyawa" kusan ha saba jin irin wadannan babatun abakin 'yammata saboda haka bai juyo ba sai da ya shiga motar ya rufe qofar sannan yayi qasa da glass din,fuskarsa a yamutse kamar ya ga kashi yake kallonta,yayin da ita kuma ta harde hannaye ta zuba masa ido tamkar mayya tana zabga murmushin neman shiga "kina da matsala da ni ne?",cikin murmushin tace "yes,babba ma kuwa"aliyu ya fasa kunna motar da yake qoqarin yi da dayan hannun nasa ya dogara hannun jikin murfin motar yana shafa sumarshi hadi da tsareta da ido,ya sani sarai qarya take don yaci karo da mata irinta sunfi dari Sai yayi mata kwarjini domin shi din ba kalar wasa bane,ba tare da ya sake tambayar tata ba ita da kata cikin diriricewa tace "zuciyata ka sace min ne,kuma na jima ina jiran rana irim wannan da zan sanar da kai"fadila dake kashingide cikin motar kalaman suka shiga kunnuwanta,amma sai taga meye nata tunda ba'asa da ita ba,bari taga ya drama din zata kaya,sake kallonta aliyu yqyi cikin raini "ke! Ki shiga hankalinki,ni ba sa'an wasanki bane,bana son shashancin banza" yaja tsaki yana shirin tada motar ya kunnata ya fara dan janta yana duna inda zaiyi ribas,"ko baka sona ni ina sonka wallahi kuma suna na mansurah"ya leqa kansa ta window "sai ki bada himma ko,stupid" "Iove you idan baka soni ba bazaka hanani in soka ba aliyyu salim kuma sai na aureka na shigo gidanka"zuciyar 'yan maza ta motsa ya tsani mata masu naci irinta haka,niyyarsa ya fice yayi maganinta ta kama hannunsa dariya na shirin subuce mata "haba sonka fa tace tana yi ba qinka ba,masoyi ai yafi maqiyi meye laifinta?" Tana gama fada dariyar ta kubce mata Qyal qyala dariyarta take sosai,cak ya tsaya yana kallonta,kyawunta ne ya fito sosai,tuni ya mance da wasu ya shagala da kallonta,ita kam bata ma lura ba dariyarta take har da toshe baki,a hankali ya kai yatsansa lobawar nan ta tsakiyar habarta da ta dauki hankalinsa sannan ta farga ita yake kallo,ta yi qoqarin gintse dariyar ta janye fuskarta a kunyace,ajiyar zuciya ya saki kana ya tada motar,tuni ya manta da wata halitta wai ita mansura,fadila ce ma idanunta suka kai gun tayi sakato a tsaye tq zuba musu ido ita mansuran sai lokacin ta kula bashi kadai bane cikin motar,tamkar ta fashe da kuka takaici ya cikata,'yar rakiyar tata kam dariya take ta qyalqyala mata"ai na gaya miki mansura,banda abunki ki duba fa kanki ki dube shi ki dubi kuma wadda suke cikin motar tare,wanda yake da kamar wannan ai baki isheshi kallo ba,ke babu lallaima ko a 'yar aiki ya daukeki indai zaki hada kanki da wada suke tare din nan" ashar ta lailayo ta dirka wa qawar,ita kuwa tayi gaba ta fice abunta Tuqi yake amma gaba daya kaf hankalinsa na kanta,duk second biyar zuwa goma sai ya juyo ya kalleta,sai daga baya ta lura da hakan "please ka maida kanka gun driving,kaga muna kan titi ne"ta fada idonta na kallon kan titi,gani tayi yayi gefan titi a hankali ya gangara gefan kwalta yayi parking din motar sannan ya kashe ta,ta juyo ta dan dubeshi don bin ba'asin abunda suka tsaya yi din,amma sai ta kasa furta komai saboda wani mayen kallo da yaje binta da shi wanda ya haddasa mata jin wata matsananciyar kunya mai kashe jiki,ya sake raunata mata zuciya da gangar jikinta da wani kurman saqon soyayya mai zafi,bata san sanda ta maidq bayanta jikin kujerar ba ta lafe hadi da langabar da kanta gefen kafadarta hagunta A hankali yasa hannunsa ya juyo da fuskarta zuwa gareshi, "no,kada kimin rowar fuskarki baby na,barni in more abuna" bata ce komai ba sai dan qaramin murmushi da ta saki wanda ya sake shagaltar da aliyyu,sannu a ahankali ta dora qwayar idanunta cikin nasa tana morewa kallon aliyyun,rana ta farko da hakan ta soma kasancewa tsakaninsu,dukkaninsu kallon so qauna aminci da yarda suke
Chapter 65 · 0% Book details