← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 84

Sashe 57

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'yar ciki ya fito cikin haushin kaza huce kan damiSuna hada ido da andin yasan cewa babu lafiya fa,don kalli daya zaka yima aliyyun kasan ya koma wani hargitsatstsen aliyyu,cikin tsawa yace "what doyou want?!" Cikin girmamawa yace "sir d time is passing,u have to prepare........." "leave me alone!" Aliyyun ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu cikin wata tsawar,ya ja qofarsa garam ya kulleta ya koma cikiSaman kujera ya koma ya zauna yana nishi,sai a alokacin idanunsa suka sauka kan wayarsa da ya tarwatsa jiya,yasa hannunsa ya tsince ya maida layukan ya sanya batirin ya kunnata,servicena gama hawa massage suka yita shigowa sun kusa hamsin,ko guda baiyi sha'awar budewa ba bare ya karanta,hasalima hankalinsa bai kanta nashi tunanin daban,cikin haka kira ya shigo,bai ko kalli wayar ba bare akai ga batun dagawa,sai da tayi ta katse har sau biyu,cikin jan tsaki ya sanya hannu ya janyo wayar da niyyar kasheta,number din uncle abba ya gani,bau damar kashewa kenan,luguden bugu kawai zuciyarsa ke masa,ya danna ok,ya gama bada amannar cewa fadila taje musu ne,ba qaramin rudewa yayi ba saboda sanin halin abban nasa sarai bashi da sauqi kan wasu lamuranYa kara a kunne jiki a sanyaye,tambayar da abban nasa ya masa ta sake sashi cikin wani halin ha'ula'in"me kake yi haka ne aliyyu?,lafiyarka kuwa qalau?" Cikin rawar murya yace "abba...wallahikuskure ne....kuskure aka samu kuma....."ya dakatar da shi"ya isa bana son jin komai maza ka tashi ka shirya,mr lin ne ya kirani ya gaya min komai har mutum ya aiko maka ka koreshi,damar da ka ka jima kana jira yanzu don ka sameta shine kakeso kayi wasa da ita?,maza ka ahirya kafin lokacin yayi kamar yadda aka tsara"wata boyayyar ajiyar zuciya ya saki ya maida bayansa jikin kujera "to abba inshaAllahu" suka qare wayar yana masa addu'ar samun nasara tare da sanya masa albarkaYa kashe wayar sannan ya zuba mata ido,yana ji a jikinsa da zuciyarsa bai kyautawa abban nasa ba ma,bai san da qanne ido zai kalleshi ba,cikin kasalartasa ya miqe ya shiga toilet ya hada ruqan wankanshi da kanshi don cika umarnin abban nasa,awanni biyu ya dauka ya kammala shiryawa,komai da yakeyi babu walwala a fuskarsa,dama yaya lafiyar kura bare tayi hauka? Hakanan babu kuzari ko qanqani tattare da shi,shigarsa ta suit yayi saidia wannan ta musamman ce 'yar ubansu,wadda dama an tanadeta ne domin wannan rana,maqudan kudade aka kashe gun siyan nata,kai da kanka idan ka kalleta ba sai angaya maka ta lashi kudi ba zaka baiwa kanka amsa ash ce mai cakude da yarfin baqi rigar ciki kuma da tie dinsa kuma light pink ne,agogo da ya daura da takalmi na qafarsa ma kawai abun kallo ne,sumarsa tayi kyau sosai kamar yasa mata relaxer,sosai aliyyun yayi kyau tamkar balarabe,yaya dama mai kyau yasa abu mai kya?,saidai cikin zuciyarsa sam babu nutsuwa ko farinciki ko dayaSuna waje suna jiransa cikin dalleliyar sabuwar baqar mota,sabuwar qira ce don a shekarar aka farahawanta,yana daya daga cikin kutane na farko da suka mallaketa ko a qasar chinan,mutum uku ne suka miqe ya watsa musu harara don yana ganin susuka takurashi zuwa gurin tamkar su suka yi laifin,dayan ya bude masa inda zai zauna yayin da ragowar biyun suka bishi da gaisuwa,baiko kallesu ba sun san ba lafiya son haka basu sake cewa komai ba suka shiga mai tuqi ya tafa motarTafkeken dakin taro ne dake cikin ginin kamfanin*maitama factory*,hall ne da yaci sunan hajiya*maimunatu ibrahim muhammad* mahaifiya gareshikenan,cike yake da al'umma mahalarta taron,sosai aka qawata gun,decoration aka masa mai azabar kyau da tsari,kowanne table kujeru hudu ne suka zagayeshi,kusandukka mahalarta taron sunyi shiga ne ta baqaqen coat kamar masu ashobi,maza ne damata jinsin yarw da qabila daban daban,kowanne zaune gurinsa a nutse cikin tsari suna sauraran bayanai daga bakin mai gabatarwa duk cikin dakon isowar aliyyu,babu wata hayaniya kai sai ka rantse babu mai numfashi cikin hall dinShigowar tasa ya sanya duk wani dake dakin taron miqewa tsaye cikin girmamawa,tafi ya cika hall din raf raf raf,tamkar ya zura da gudu ya bar hall din haka yake ji don tafin nasu wani kuda yake masa akunne,sai da ya hau step din da ka tanadar musu don zama gefan hannun hagunsa mr lin kusa da shi miss sisineo ce hannun damansa kuma ramzan ne kusa da ramzan kuma mukhtar ne,sai da auka kmmla zama sanna kowa ya koma.mazauninsaya zaunaDakin taron ya sake yin shiru,mai gabatarwa ya yi wa aliyyi barka da isowa,sannu a hankali aka ci gaba da gabatar da taron yadda aka tsara daki daki,duk anun nan da kae maganar minti biyu aka ritsa aliyyi da bindiga aka ce ya maimaita saidai a harbeshin don baya gurin *gangar jikinsa* ce kawai zaune,hankalinsa na kan fadila da agogo,duk bayanminti guda sai ya duba lokaci,jawabai masu muhimmanci da ka tsara shi zai gabatar babu ko daya da ya iya yi,sai ya bada uzirin baijin dadi sosai,drinks da kayan ciye ciye da ka cika gaban kowa da shi babu qanda ya iya kalla balle ya tantance yana sha'awarsu ko baya yi bare akai ga batun zai ci ko zai shaAwanni biyu aka dauka sannan aka zo gangara,su mukhtar suka tilastashi kan dole ya karba yayi jawabin godiya ga dimbin al'ummar da suka.tako gari ya gari suka zo masa,yana ture lasifiqar yana komai haka mukhtar ya manna masa ,idanu da sukamasa ca yasa ya sa hannu cikin kasala da rashin sanin a halin da yake ciki ya amsa"Fadeelah!" Abinda ya soma mabata kenan cikin bututun maganar,tsit suka yi fiye da wanda sukai dazun tamkar wanda yayi calling attention nasu,ido kowa kr binsa da shi don dai sun san suna.ya ambata "fadeelah ta soni matuqa cikin rayuwarta.....na zauna da ita cikin boyayyen nuni gairin tawa kalar soyayyar gareta",ya danyi jim sannn ya shaqi numfashi ya dora "fadeelah ta barni a lokacin da ya bayyana gareni na dade nima ina sonta ba tare da nawa sanin ba....ta barni a lokacin da nake da buqatar yi mata mafificiyar soyayyar da ba'a taba gwadawa wata 'ya mace irinta ba......ta barni da wani nauyi mai azabar nauyi cikim zuciyata ba tare da na samu na sauke mun raba tare ba......fadeelah ta zama ruhina da gangar jikina"dora hannun sa yayi saman qirjinsa saitin zuciyarsa "fadeelah ta mallaki nan ba tare da saninta ba,ya dade da zama mallakinta ba tare da sanin ku mu duka biyun ba""Na tsinkayi fushi fusata da rashin fahimta masu tarin yawa qunahe cikin kalamanta,qunshe cikin takardar da ta zamo baqa aguna,cikin saqon dake bayyana bankwana da abinda zuciya ke so,cikin shafin takarda qwaya daya tal saidai sun yimin nauyi fiye da littattafai dari masu shafuka dari dari"ya hade tafukan hannayensa guri guda yana yinsa ya sauya soaai da alamun abinda yake fadi din na taba zciyarsa sosai,da alama zancan daga ainihin zuciyarsa yake fita ba daga harshensaa yakeba "ku yimin alfarmar sani a addu'o'inku....ku yimin alfarmar roqa min Allah ya huci zuciyarta,na gode muku baki daya...."ya fadi yana qoqarin komawa ya zauna,gaba daya suka.miqe suna tafi,yanayin salin ne ya burgesu,fuskarsu da zuciyarsu cike da tausayinsa,abunka da mai jajayen kunnuwa akwai girmama soyayya komai tsufanta,miss sisineo ce tabude 'yar jakarta ta fiddo da bangles na gwal guda biyu danqara danqara ta ajjiye gaban aliyyu tace ga kyautar ta a isar da ita ga fadilaSosai abun burgeshi ta yima fadilansa kyauta duk da yana da arziqin da zai siya mata ninkin wanann amma ayi kyauta wa masoyinka ma abun faranta ranka ne,yasa hannu ya dauke yayi masu kyakkyawar ajiya..........*mrs muhammad ce* *PART 3* Bayan ciye ciye da akayi a gun suka soka fita gun ainihin ginin kamfanin wanda aka zagaye shi da wani yadi mai kyau aka daure bakin qofar shigar da shi,aliyyun ne a gaba a tsaye andi ya miqo masa qaramin almakashi ya amsa ya dora saman yadin ya datse,tafi aka saki sannan suka dunguma gaba daya sukayi ciki,guri guri suka dinga shiga daya bayan daya cikin kamfanin,sosai ginin ya tsaru yayi kyau matuqa da gaske,komai cikin fasali gwanin sha'awa Ba qaramin qaguwa yayi ba,duk bayan minti daya idanunsa na kan agogo,gani yake kamar yanga lokacin yake masa,binsu kawai yake ba tare da fahimtar abinda suke yi ba,sam hankalinsa bai tare da su,cikin dabara ya zame jikinsa ya koma office dinsa wanda aka tanadar masa ko da zai zo wani lokacin,yasa key ya bude ya shiga sannan ya koma ya kulle ya koma saman kujera ya zube,awoyi uku ya rage jirgin nasu ya tashi,baya tsammanin zai iya zaman jira,ya zaro wayarsa cikin hanzari ya kira jumong da mukhtar Tare sukayi knocking ya tashi ya bude musu,kan kujera mukhtar ya qarasa ya zauna yayin da jumong ya rusuna yana jiran jin umarni,"ka shirya mota zan fito yanzu zaka kaini airport" "ok sir" ya fadi hadi da juyawa cikin hanzari ya fice,yayin da mukhtar ke kallonsa yana son tambayarsa me zaya yi a airport?,bai bashi wannan damar ba ya soma masa bayani da kansa ba tare da ya tambayeshi ba "nijeria zan wuce mukhtar nan da awa uku,ina son na bar komai a hannunka kayi handling dinsa,bazan yi sallama da kowa ba its urgent,ka wakilceni please"cikin rashin fahimta yake dubansa "like how aliyyu baqin naka zaka bari ka wuce nijeria?" "Pls mukhtar if u cannot help just tell me directly" yasan halin kayan sa sarai saboda haka ya gyada kai "is ok,is ok I will" ya miqe tsaye ya sake duba passport nashi da ticket dake cikin jakan sa,yaga komai na nan yadda zai buqace shi,ya dauka gami da zaro master card platinum ya ajjiyewa mukhtar din sukayi hand shake "thanks" aliyyun ya fada a gaggauce sannan ya bude qofar ya fice,mukhtar da mamaki ya cika shi yabi aliyyun da kallo galala,gaba daya aliyyun ya fita daga hayyacinsa sam ya fice daga nutsuwarsa Ta get din baya ya fice don baison kowa ya tsaidashi,don kuwa baiga abinda zai tsaida shi daga tafiya nijeria ayau din nan ba saidai ikon Allah,ko cikin motar ma gani yake jumong baya sauri laqaqai laqaqai kawai yake,gaza haquri yayi har sai da ya soma masa maaifa kan ya qara gudu "sorry sir ida mukayi gudu ya wuce qa'ida camera na kallon mu za'a iya kama mu" sai a lokacin ya tuna ba'a nijeria yake ba dole ya haqura a haka har suka isa airport din,ko jirgin ma gani yake ba sauri yake ba
Chapter 57 · 0% Book details