← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 84

Sashe 43

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mutstsika turare ya sauka qasan Muhammad ne kawai zaune kan table din yana buga game a wayarsa ta zauna kusa da shi hadi sa dan dukan kafadarsa,ya dago ya dubeta yana murmushi, "ka shiga aji nawa ne har ummi ta yarda aka baka waya,cikin dariya yace "haba anty nafa zama senior ina s.s one fa,kuma ma yanzu nine babba a gidan nan"dariya ya bata sosai tana cikin darawar ne ummi ta fito,tuni har ta yi wanka ta canza shiga tayi kyau duk da ba make up take yi ba,fadila na shirin tsokanarta tace tayi kyau sallamar abba da ta aliyyu ta karade falon wadda ta yake hirar da suka so farawa Abban ne a gaba aliyyu na biye da shi har suka qaraso dining space din abba ya fara cewa da aliyyu bismillah kai tsaye taga yaja kujerar dake kusa da ita ya zauna sai tayi duru duru har rudewarta taso ta fito,ji tayi ya take mata qafa ta danji zafi ta dago kai suka hada ido yayi mata alama da ido na ta nutsu,sannan ya duqar da kansa ya gaida ummi cikin girmamawa,ita kuma ta amsa masa cikin kulawa tana tambayarsa mutanen gidan Fadila ita tayi serving kowa banda ummi don tasan ba zata ci ba,tazo kan aliyyu sai ya rasa mai zata zuba masa idonta na kan warmer tace "mai zaka ci?" "Zuba min duk abinda zaki ci" ya fada abunsa tamkar ba shi yayi maganarba,da sauri ta dago kai ta kalleshi saboda wata kunya da ya bata amma sai taga shi ko ajikinsa,ta saci kallonsu ummi sai taga hirar su ma suke da abba kamar basu san da su agun ba,sai kawai ya zuba masa fried rice da farfesun naman kaza mai yawa tana son qureshi taga zai cin? Sai kuwa ya shayar da ita mamaki don abincinsa yake ci hankli kwance duk da baici da wani yawa ba yafi shan lemo,bayan sun kammala ita ta kwashe kayan ta kaisu kitchen ta hada ta wankesu kamar yadda ta saba tanayiwa ummin tun kafin tayi aure,tana aikin cikin ranta tana gulmar aliyyu bai da kunya Saman kujera ta tadda su ta parlour ta samu gefan umminta ta rakube,aliyyu ne ya dora kan maganar da sukeyi da abban "sallama mukazo yi muku abba saboda gobe insha Allah zamu wuce china" abban yace "zancan bude kamfanin ne ya taso kenan munyi maganar da abban naku ai wancan watan yake gayamin an dan samu tasgaro ne da tuni cikin wannan watan company n ya fara aiki" aliyyu ya gayada kai yace "eh abba insha Allah wanna karon za'a kammala komai a budeshi daman cike ciken takaddu ne na yarjejeniya tsakani na da gwamnatin qasar ya kawo tsaiko amma yanzun al'a muran saun daidaita Mrs Muhammad ce 1:41 pm 29/8/2016 *WA YASAN GOBE?..* Abban ya jinjina kai yana cewa "kasan qasa ce mai tsari da doka ba irin namu qasaahen ba da sai dai muce inna lillahi wa 'inna ilaihi raji'un,Allahbya taimaka ali ya kuma yi jagora yasa a budeshi a sa'a,Allah yayi ma jagora a dukkanin lamuranka"ummi na amsawa da amin yayin da shima yayi qasa da kansa yana cewa "ameen ameen abba na gode Allah ya qara girma" yana shirin miqewa yasa hannu cikin aljihun kuftanshi na riga ya zaro turare yan ubansu designers ya ajjiue wa abban,albarka yasa masa tare suka qarasa miqewa abban zai masa tattaki kasancewar alhj abbas mutum mai sauqin kai ba ruwansa da wai shi mai shekarune babba ne kowa nasa ne Sai lokacin fadila ta janye idanunta daga kan aliyyu kallonsa tayi sosai don bata taba ganin sa yayi doguwar magana irin haka ba,yanayin yadda yake maganar cike da girmamawa sai ya sake burgeta ta sake lafewa jikin ummin tana saukar da ajiyar zuciya,ummin ta kalleta sanda suka gama ficewa "au sake ma wani rabewa kike ajikina ke da ake jiranki?" Dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki sai kuwa ta saki kuka,ummin ta saki baki tana kallonta "wai wannan wane irin sakarci ne ko wata matsala kike da ita?" Kai fadilan ta girgiza,ance tsakanin d'a da uwa sai Allah hakanan sai tausayin gadilan ya kama ummin don yasan duk mace kimai jin dadinki baki rasa matsala ta zamantakewar aure,a da rance take mata nasiha hadi da lallashi Ganin hankalin ummin ya tashi sai tace cikin son kawar da hankalin ummi daga tunanin ko tana da wata matsala tunda tasan halin iyaye yanzu sai ta fita shiga damuwa"ummi bana son na barku ne har wata hudu" ta saku ajiyar zuciya tana godewa Allah "idan banda quruciya irin taki fadila ko kina nan din ma basai ki kusa wata biyu ma baki gan mu ba ummm.....kiyi addu'a kinji Allah ya kaiku lpy ya dawo da ku lafiya kawai" tace amin tana share hawayen cikin dakiya Ta zuge zif din jakarta ta fito da kudaden nan ta dorasu cinyar ummin,ummin ta kalli kudin sannan ta dubeta "wannan fa na meye?" "Naki ne ke da abba" "ina kika samo su fadila?yaushe kwata kwat kika soma aikin? Ina fatan ba roqonsa kike ba dai ko?", ta girgiza kai "a'ah ummi shi yake bamu kullum idan zai fita" ta dauke kudin ta ajjiye a gefe tana cewa "za'a dai juya miki zan bawa abbanki ko yayanki zasu san inda zasu sa miki su" ta langabar da kai tace "don allah ummi to ko dan wani abu ne ki cira aciki ke da abban ku samin albarka" ta bita da "to naji" Idonta fal da hawaye zuciyarta a raunane ta fito ,suna tsaye jikin motar aliyun ta qaraso ta tsugunna har qasa idanunta rau rau muryarta na rawa tana yiwa abban sallama "to fadila Allah yayi muku albarka ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya,ki zauna lafiya agidanki bana son fitina kada na ji kada na gani" tuni kukan ya qwace mata "insha Allahu abba"kasa tashi tayi har sai da abban ya daga ta da kansa,aliyyun ya zuba musu ido wani abu yaji ya taba ransa shi ya bude mata motar Abban ya sata ciki da kansa,aliyun ya rufe qofar sukayi sallama da abba ya zagaya ya shiga gun zamansa ya tada motar Shiru cikin motar sai sautin kukanta danke tashi kadan kadan hadi da sheshsheqa,burki taji yaja bayan ya gangara gefan tati ya kashe motar sannan ya dan kwantar da kujerar da yake kai din ya kwanta rigingine idanunsa alumshe yana sauraran sautin kukan,sai da suka kusan kwashe awa guda ahaka lokacin tuni har kukan nata ya tsagaita,ya miqe a kasalance ya gyara zaman kujerar baice uffan ba ya tada motar suka wuce Cikin daren bata kwanta ba sai da ta hada duk abinda take da buqata cikin babbar trolly dinta sannan ta kwanta zuciyarta fal da saqe saqe kala kala Cike da kasala take janye da akwatin nata har ta iso bakin motar qirar sienna dake fake a harabar gidan,yadine a jikinta mai sulbi blue tayi rolling da red din mayafi ,sosai rigar ta bude daga qasa takalminta red ne hill sosai ,motar na bude duk suna ciki nasiru na mazaunin driver aliyu na kusa da shi sai salima dake sit din can baya bisa dukkan alamu ga fuskarta nan ta sha kuka,fuskar samira ba yabo ba fallasa tana sit din tsakiya,yayin da fadila ta zauna a sit din farko nasiru ya karbi troly din nata ya sanya a baya Cikin hanzari nasiru ke ruqin aliyyu ya sake duba gaogonsa yace "nasiru qara sauri zamu iya missing flight" ya sake qarawa motar gudu don bin umarnin ogansa Ba dadewa suka isa aminu kano international airport nasiru ya ajjiye motar inda aka tanada don ajiyar motoci,dukkaninsu suka fito daidai lokacin da airport din ta karade da sanarwa neman masu tashi a jirgin ethopian airline,hakan ya tabbatar ma da aliyu sun kusa makarar kam,tuni nasiru ya ciro musu jakankunansu,ya dubi samira da salima da fuska take adinke musamman salima da takejin kamar ta dora hannu aka ta zunduma ihu,"sai na dawo" yace kamar mai jira salima ta fashe da kuka ta taho a guje ta fada jikinsa,ya saki dan qaramin murmushi hadi da sa tafin hannunsa yana dan bubbuga bayanta alamar rarrashi,ya miqawa samira daya hannun alamar ta taho,dauke kai tayi tana turo baki zuciyarta babu wani takaici sosai Idan ta tuna da maqudan kudaden daya barwa kowaccensu tasan zasu sha bushasha don ma yayi misu gqrgadi da jan kunnen akan fita"sai ka dawo"tace kawai,ya dan janye salima daga jikinsa sukayi sallama da nasiru,ya wuve fadila ta rufa masa baya saluma ta bita da harara kamar ta fincikota,batasan itama fama take da fargabar bin aliyyun ba Reception suka wuce suka qarasa departure ta farko suka shiga layin screening,aka kammala da su aka basu boarding pass suka qara gaba,immigration suka sake duba visa dinsu suka buga musu stamp suka shiga dan dakin jiran jirgi,mintina qalilan jirgi yayi ready suka bi layin shiga jirgi tana gabansa yana tsaye a bayanta Mrs muhammad ce [10/16, 1:51 PM] Salma *WA YASAN GOBE?...* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *part 2* 25 and 26 ne number din sit din nasu don haka sune maqotan junansu,aliyyu ya daga yar trolly din da aka barsu suka shigo da ita saboda kilo din ba wani mai yawa bane ya sanyata a inda mayafiyan ke ajjiye jakankunan nasu,yan kallo fadila nata kiciniyar sanya tata saboda ta dan yi mata nauyi,sai da ta soma gajiya sannan ya sa hannu ya janyeta ya fada kan kujerarta ya daga trolly din tata ya sanya mata ya koma sit dinsa ya zauna yana gyara zaman suit din jikinsa Kowa ya zauna a mazauninsu,fadila na bakin window ta zubawa filin airport din ido tana fargabar yadda jirgin zai Lula da su sararin subhana duk da yawansu kasancewar wannan shine shigarta jirgi na farko a arayuwarta A hankali aka zare matattakalar aka maida qofar jirgin aka rufe bayan sun gama duk wasu yan tsarabe tsarabensu suka bada sanarwar daura belt,fadila ta jawo belt din saidai bata san yadda zata sata ba,tana satar kallon aliyyu ta gefan ido yana daura tasa,ya kammala ya fito sa laptop dinsa ya dora bisa cinyarsa A hanakali jirgin ya soma qugi hadi da shawagi a doron qasa na kimanin minti goma sha biyar sannan ya yunqura don rabuwa daa doron qasa,fadila ta runtse idonta saboda
Chapter 43 · 0% Book details