← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 84

Sashe 4

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

laifinki ne saiki yi shiga ta janye hankali kuma kice ba wanda ya isa ya kalaki"banza tayi mata ta dauki wayarta dake kan dressing mirror ta fice,farida ta dan daga murya yadda zata jiyota tace"a dawo lpy antyna Allah ya hadaki da mannau ya biyoki har gida "bata dai ce mata ci kanki ba ta wuce dakin ummi don tasan a wannan lkc tana daki tana azkar,daga bakin qofa ta tsaya don ta kusa makara tace"ummi zan tafi""to Allah ya tsare hanya ki kula sosai kuma kuna kammala abinda kukaje yi ki taho gida kada ki yadda kiyi dare a waje"tace insha Allah ummi",acan gidan radion suka hadu,bata shiga ba ta yiwa su Hafsa waya su fito su wuce don a motarta suka tsara za suyi tafiyar,Hafsa na zaune a baya yayin da khalil ya shige gaba,tsaf fadila ta gama karantar manufarsa saidai tayi banza da shi tamkar bata fuskance shi ba,tun zuwanta gidan yake rawar qafa a kanta saidai ya kasa furta mata kamar sauran maza da yawa,tana da wani irin kwarjini ne a idanunsu ita sam baya burgeta,ya fiya surutu shi yasa sam bata son ko aiki ne a hada ta da shi,kamar yanzun ya takura mata sai zuba yake shi ala dole sai ya burgeta,Hafsa na baya tana ta tuntsira dariya don tasan halin kayarta sarai,daqa qarshe c.d plate ta dauka tasa sannan yayi shiru A hankali suke binkwatancen har suka gano gurin,qaton get din gun aka bude musu gu ne a tsare ahankali aka dinga nuna mata inda zata bi har taje inda aka tana da don ajiyar motoci tayi parking suka fito,ta jingina jikin motar tata tana qarewa gun kallo,tamkar ma'aikata gun yake saidai ya tsaru sosai komai neat,khalil ya qarso gunsu bayan yaje yayi tambaya yace muje can sunce mu jirashi yana fitowa,wani dan gune da ka qawatashi da flastic din kujeru da teburinsu kowanne yaja kujera guda ya zauna sun dan dauki mintina har fadila ta soma qosawa da zaman jiran Tun daga nesa da ta hangoshi qirjinta ya hau luguden bugawa,ji tayi tamkar ta tashi ta bar gurinsai kuma taga idan tayi hakan ta bada kanta,don haka sai ta basar ta zarme da bude jakarta ta soma fiddo da kayan aikin da zasu buqata,qashin mayen tutarensa da taji ya mamaye gurin shi ya tabbatar mata da qarasowarsa,sallamarsa ta same tabbayr mata da hakan dukkansu suka amsa saidai ita ta kasa dago ido ta dubeshi ta fake da laluben jaka,ya .iqawa khalil hannu sukayi musabaha hafsat ta gaidashi,sai a sannan ta dago kanta caraf suka hada ido saidai ga mamakinta dauke kansa yayi tamkar bai taba ganinta ba,a hankali ta radawa hafsa"da wa za muyi hirar ne?""gashinan a gabanki a.s maitama "inji hafsat"take taji ta dan rude amma cikin dabara ta gayyato dakiya da nutsuwa ta yafawa kanta,kasancewar Ita ce mai tambayoyin jfsat da khalil na tayata da rubutu dolenta ta jawo kujerarta ta sake matsowa daura da shi ta sanya 'yar qaramar recorder dinta a tsakiyarsu suka sake zama verry close aunyi face to face sosai,wani yanayi ya dinga shiga zuciyarta da gangar jikinta wanda hakan ya haifar mata da kasala,tanason tayi.masa tambaya ta farko saidai ta kasa,har sai da hafsat ta dan dungure sanna tayi ta maza ta dago ta fuskanceshi ,saidai ga mamakinta hannauensa na harfe ne bisa qirjinsa yana mata wannan salon jallon rainin nasa ,da fari munason muji ainihin cikaken sunanka,ta fada yayin da ta mayar da dubanta kan radio dinta taga tana nadar sautin yadda ya kamata,shiru taji har yayi yawa ta dago ta sake dubansa a karo na biyu,saia taga ya saki hannunsa ya dauke idonsa daga kanta ya kalli khalil yace"ko zakuyi musayar aiki ita ta ta karbi rubutun kamar ba zata iya aikin ba"khalil ya dan rusuna yave ranka ya dade zata iya haka tsarin aikin yazo"ya kalleta cikin gatsali yace"zaki iya?"batayi qasaaqwiwa ba tave aisai an gwada aknsan na qwarai"ta mayat masa da irin yanayim yadda ya yi mata tambayar,cikin ransa yake jinjina rashin kunyarta tare da fafin nasan maganinki" a zuciyar sa ya fadi hakan Ku biyoni muje...... [10/16, 12:21 PM] Salma Wa yasan gobe? Safiyya Abdullahi musa huguma Ya dan gyara zamansa cikin isa ya amsa mata"Aliyyu salim maitama shine cikakken sunana""sunan ya dace da maishi"ta fadi a ranta,cikin nuna qwarewa da gwaninta ta shiga jefa masa tambayoyi daya bayan daya,sai da suka kwashi kusan awa guda sannan ta saurara masa,ta katse abun recording din nata ta jefa a jakarta,ta miqe tayi gaba abinta,saidai can qasan zuciyarta farinciki ne fal ranta,yau ta zauna daf da shi ta shaqi qamshinsa ta saurari muryarsa son ranta,shi kam bin ta yayi da kallo cike da mamaki da takaicin raininta don a gurinsa wannan raini ne. Zaman ta tayi cikin mota tana dakon zuwansu hafsat Dukkaninsu suna gidan alh salim,kasancewar yau ake birthday din iftihal,rabi'ah sumayya farida da fadila anty hafiza sai anty hauwa'u(babbar yar haj maimuna)duk suna bedroom din momi,fadila na kwance bisa gadon momin,dakin ya kaure da hayaniya amma banda ita,sam gun ma baya mata dadi,tun jiya da Abba yayi mata da ya ahmad suka yi masu magana ita da farida kada su kammala attachment dinau ba tare da sun kawo mijin aure ba,farida kam ko ajikinta tunda dama irin wannan damar take jira ita da masoyinta mubarak Ta sake juya kwanciyarta hannun damanta kanta yayi mata gingirin zuciyarta a cunkushe,anty hafiza ta juyo ta kalleta "fadila ki saki ranki don Allah kiyi addu'a shine kawai mafita "fadila ta lumshe idonta hadi da sake qanqame pillow tana sake jin nauyi cikin qirjinta,anty hauwa tace "me ya sameta ne tun dazun na lura bata cikin sukuni",anty hafiza ta gaya mata hadi da cewa"na rasa irin farida kwata kwata bata kula kowa,nan da kika ganta bata da wani gwani"farida tace " anty itama fa da laifinta ya za'a ce duk mazan dake mutuwar sonta ace babu daya da ya mata"a fusace fadila ta kalleta "anty kinganta ko ko da ita ake magana? "dama zuciya kusa a kusa sai hawaye wani na bin wani "anty hauwa'u tace"duk ku tashi ku fita ku bamu wuri"tsam suka fice dakin ya rage daga ita sai fadilan sai anty hafiza,anty hauwa'u taja ajiyar zuciya tace"sai nake gano dacewa tsakanin fadila da Aliyyu Abban iftihal ba don kada nayi muku shishshigi ba da na hada wannan alkhairin"gabanfadila yayi matsananciyar faduwa jin an ambaci Aliyyu,inama ace shine aliyyun da anty hauwa'u ke magana akai?,ina ma ace shine zai taho da neman soyayyarta?,ina ma ina ma.........taci gaba da zancen zuci Anty hauwa taci gaba da cewa"shima anyi anyi da shi ya fidda mata tayi aure ya qi,sai jiya ya kawo wata yarinya mai zubin yare ba alamun tarbiyya a tattare da ita wai ita yake son aura,hafiza yarinyar bata da maraba da matarsa ta farko,amma sai ya kakkareta da cewar wai zaman cikin yare ne yasa aka ganta haka amma da nutsuwarta. Fadila tayi hanzarin tashi don batason zancan da anty hauwa'u ta dauko yayi ma wani nisa,tayi qasa da idonta tace"anty ba wai inason watsa miki qasa a ido bane a'ah,bansan ya Aliyu ba sani na da shi tun ina qarama ne wanda a yanzu na manta shi gaba daya,shima kuma nayi imanin ba sanina yayi ba,ba ta wannan ba anty a zamanin nan auren soyayyar ma ya aka cika bare auren hadi,matar cushe anty ba ta daraja,kawai ku tayani addu'a Allah yayi min zabi mafi alkhairi"suka amsa da amin suka kuma bar maganar suka shiga wata badan maganar ta bar ran anty hauwan ba Kwana biyu da yin maganar anty hauwa na juya maganar cikin ranta sai ta kasa hadiye maganar har sai da ta niqo gari ta dawo gidan don tattatunawa da abba"tana zaune gaban abban bayan sun gama taba hira tace"abba nazo maka ne ne da wata muhimmiyar magana"abban ya bada dukkan hankalinsa kanta sannan yace"uhm ina jinki maijidda"ta dora"abba kasan fadila 'yar abba abbas tafida?"yayi murmushi irin na manya yace"banda abinki maijidda idan ban san su farida ba ai kuma bansan kuba,"tayi dariya ita da momi tace hakane abba"tiryan tiryan take gaya masa halin da yanzu fadila ke ciki game da zancen fiddo da miji,sannan ta dora"abba inason ne na haska muku abinda tuna nina ya hasko min game da wannan lamarin""uhn"cewar abba,anty mai jidda ta dora"abba Ali ya kawo muku yarinyar da azahirin gaskiya baku yadda da halaye da nagartarta ba,ali abba ya riga ya fada soyayyar yarinyar wadda da zarar kunce zaku hana shi auren ta dama ce tq zo masa ta yaci gaba da zama babu zancen aure,zai kafa hujja da cewa ai tun tuni ya kawo ku kuka qi abun"abba ya gyada kai cikin gamsuwa maijidda ta dora da fadin"to abba mai zai hana ku bashi damar ya aureta amma abba ku hadashi da fadila?,abba kai ganau ne ba jiyau ba ka fini sani kasan fadila kasan irin kyakkyawar tarbiyyar da suke da ita,mai zai hana muyi kwadayin hada zuri'a da su abba?,abba kada mu bari ta subucewa family dimmu saboda fadila macace ta gari wadda nake da yaqinin samun alkhairai masu tarin yawa da zuriyya dayyiba tattare da ita?" Shiru sukayi gaba dayansu bayananta na ratsa su tabbas duk abinda maijidda ta fada gaskiya ne,sun gamsu matuqa da bayananta,abba yaji dadi matuqa sosai tare da sawa maijidda albarka gameda zurfin tunanin da tayi akan makomar rayuwar dan uwanta Washegari alh salim da kansa ya taka ya nufi gidan amininsa alh abbas tafida,suna babban falon sa bayan sun gam gaisawa alh salim yace"abbas nasan zakayi mamakin ganina ko da daddarennan bayan jiya da azahar ma muna tare"alh abbas yayi murmushi yace ai nasan akwai dalili,kuma ma mene a aciki don dan uwa ya ziyarci dan uwansa aduk sa'adda da yaso?"alh salim ya gyada kai yace"hakane dalili ne kuwa babba ya taso da ni"alh abbas ya vyara zama yace"ina jinka Allha yasa lpy"alh salim yace"danka Aliyyu nazo nemawa auren'yata fadila"alh abbas yace"fadila?"ya gyada kai qwarai fadila ko anyi mata miji ne?"alh abbas ya girgiza kai yana murmushi yace"ko daya wlh,rigimar da nake ma da ita kenan a 'yan kwanakinnan kenan akan sai ta fito da miji,maganarka alh ta yimin dadi sosai wlh,amma ina fatan da amincewar alin?"a'ah ko daya wannan hasashe nayi na son hada zuriyya da aminina"alh abbas ya saki dariya yace"yayi wlh wannan
Chapter 4 · 0% Book details