Sashe 40
Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
take kamar tasa hannu ta fisgo abinda ke cikin ta jefar ta huta,wani takunkumi ya kafa mata ya hanata fita ko ina hakanan ya hanaduk wani mai zuwa zuwa gurinta,makaranta ma shike daukarta ya kaita ya kuma tsaya a bakin inda da zata dau lecture din har sai ta kammala ya daukota ya maidota gida ya kuma kulleta sannan ya fice sabgoginsa Da wannan rikici ta kammla karatunta yayi clearing din komai nasa ya dawo Nigeria shi da ita gaba daya sai dai idan wani abu ya kamashi na yaje indian sai ya tasata agaba suje tare su dawo tare don kada ma ya barta tsautsayi ya gifta tayi abinda ranta ke raua mata,don baijin idan ta aikata hakan zai iya qyaleta ko ya daga mata qafa, Ita kuwa ta samu sake rigima harda mara dalili yinta salima take dom dai taga duk ya dora burinsa kan cikin,ya zuba mata ido ne saboda albarkacin yaronshi da take dauke da shi gashi mai tausayi ne qwarai da gaske kan mace mai ciki,hakanan tsakiyar dare sai ta tashi ta zauna ta kuma taahi aliyyun suyi kwanan zaune ta kuma kwana tana rusa masa kuka da ihu ita wai cikin ya dameta ya hanata sakewa Cikin haka ne ranar wata juma'a aliyyubya fito a masallaci aka masa waya asibitin doctor sa'adah yazo salima ta haihu,yayi matiqar mamaki don kuwa cikin watansa takwas da sati biyu kuma lafiyar Allah ya fita ya barta a gidan babu wasu alamun naquda tare da ita don baccinta ma take shirga,baiyi qasa agwiwa ba ya isa asibitin cike da murna doki da koma mamaki,yana zuwa ya samu qarin bayanin zuwa tayi aka turo naqudar ta qarfin tsiya wai ta gaji da zaman cikin ajikinta don lafiyarta lau ta iso asibitin,yayi fada sosai don sunga doctor sa'adah bata nan ne da ko bakin salima zai cire don roqo bazata yi mata ba har sai da yarda da kuma izinin aliyyun Ransa yayi mummunan baci saidai yana yin tozali da santaleliyar baby girl din da Allah yayi masa kyautarsa sai farin ciki ya mamaye gurbin bacin ransa tuni yama mance da abunda ya faru,sak kamammin family dinsu tayo ya rungume yarinyar tsam tsam a qirjinsa qaunarta na mamaye jinin jikinsa,ya dinga kissing din yarinyar da tofeta da addu'o'in tsari kala kala,tuni gidansu ya cika da yan uwa mominsa farin ciki tamkar akan yarinyar ta fara jika,duk wani uatsina da salima keyi da daga kai ita da yam uwanta hakan bai dami yan uwan aliyyu ba domin su gadon arziqi ne ba taka shi sukayi suka haye ba rana tsaka,harkar girma kawai sukeyi Suna akayi na tserewa sa'a,yarinya tayi albarka sosai don daga salima jar aliyyin babu wanda bai ga hakan ba,khadijatu shine sunan da ya mominsa ta zaba mata don abba ya bawa zabi shi kuma yace ya bawa momin ta zabawa kishiyarta sunan da kanta tayi murmushi tace ta bata khadijatu tana fatan Allah yasa ta yi gadon hali irin na mai asalin sunan,salima dama wannan bai dameta ba ita dama ta rabu da cikin shine agabanta alaqaqai kamar yadda ta laqaba masa Aka gama wannann ta wuce salima ta sake qirqirar matsala ta biyu wadda ta tunzurashi ta koma jawo igiyar aurensu ta guntule Mrs muhammad ce [10/16, 1:48 PM] Salma *WA YASAN GOBE?...* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *Part 2* Yadda abun ya faru shine salima sam taqi shayar da iftihal,anty hauwa ita ta gani ta yiwa salima magana cikin nasiha da kuma fadakar da ita illolin dake tattere da qin shayar da yaro nonon uwa indai ba lalura ba mai qarfi wadda zata jawo hakan koda hakan ta faru wasu basu yarda da madarar suna kai dansu ne ga wata wadda suka amincewa halayenta ta shayar musu da yaro balle ita da lafiya lau ne babu wata lalura,qememe salima tayi da ranta taci gaba da dirkawa iftihal baiwar Allah madara ba tare da masaniyar aliyyu ba Ranar da lamarin ya faru sati biyu ne da yin haihuwar cikin yan suna wata ta sanar da ummi halin da ake ciki don haka ta aiko anty hauwan takanas da roqo da kuma lallashin salima tayi haquri ta shayar da iftihal don abun ya daga hankalin momin tace ko lafiya ce bata da ita tayi magana sai a a samo mata magani cikin tsiwa da rashin kunya salima tace"ita momin ce ta aiko ki?to ki gaya mata babu dan iskan da ya isa ya jawomin abinda zaisa jikina ya lalace lafiyatq qalau saidai tun farko na gayawa ubanta ban shirya haifarta bane,don da na samu dama da tuni tabi rariya ba zata ma zo duniyar ba bare azo ana min iyayin banza da wofi akan........... Bata qarasa ba taji saukar lafiyayyun mari hagu da dama na kumatunta,da sauri ya daga kai din taga wanda yayi mata irin wannan aika aikar,aliyyu ne tsaye bisa kansa cikin matsanancin fushi fuskarsa tayi jajur abunka da fari huci kawai yake fitarwa kamar wani zaki ya dora da cewa"bansan baki da mutunci ba sai yau ashe ke 'yar iska ce ban sani ba? Mahaifiyata kike fadawa wadannan mugayen kalaman?.....to bari kiji salima..... har yau ba'a haifi yarinyar da zata ci mutuncin iyayena ba wallahi duk son da nake mata,yarinyata kuma daga kin bar bata madara indai ni ke aurenki" Cikin hasala ta miqe tana nuna kanta tace ni ka mara aliyyu?....ni ka mara?,to an fada din yarinya kuma wallahi ko sama da qasa zasu hadu ba zata sha min nono ba,ai kana da yan uwa mata kana iya basu ita su shayar maka ko ka samar mata wata uwar ko kuma ka maidata cikinka ka sake haifeta"ya harzuqa matuqa ya daga girarsa yana kallonta "oh haka kika ce! Indai kuwa haka ne baki da wani amfani" "to ba sai ka yiwa tufkar hanci ba"a zafafe ya gyada kai yace "ok,well kije na sake ki saki daya" Maganar tayi matuqar girgizata tayi zumbur ta miqe ta dangwarar da iftihal da da take riqe a hannunta tace"tafi nono fari ai" ta shige bedroom dinta,yarinyar tamkar kuwa tasan meke faruwa ta tsandare da kuka,ko waiwayo ta bata yi ba,anty hauwa tuni ta qame hannunta aka saboda sakin da aliyyun yayi Ta fito dauke da akwati tana shirin fita,sai lokacin anty hauwa ta samu bakin magana "kiyi haquri don Allah ki dauki yarinyar nan"ta juyo a fusace sannan tayi murmushin takaici ta dubi anty hauwa"ai burinku ya cika ko?kuma ina tsammanin kema macace akwai nono a qirjinki kamar nawa to kina iya bata naki"a fusace aliyyu ya sake tasowa da niyyar kai mata wani marin anty hauwa ta tare gabansa "a'ah aliyyu kada ka sake dole taji haushi its our fault dont beat her again mu lallabata ta dauki yarinyar dai"cikin harzuqa da tsawa wadda baisan yayi ba yace da anty hauwan"ni ni zan lallabata don ta dauki iftihal god forbid anty"ya fada yana kada kai"ko zata nemi hakan ba zata samu ba"bai san ya sake tura ma salima wani baqincikin ba da sauri ta ja akwatinta ta fice,a sanyaye anty hauwa ta juya ta dauki baiwar Allah iftihal dake nannade cikin showel tana ta tsanyara kuka kamar tasan abunda mamanta ke yi ,sanyata tayi a kafada tana jijjigata tana kallon aliyyu dake zaune saman kujera dafe da kansa idanunsa alumshe jijiyoyin kansa sun fito sunyi rada rada tasan alamun tsananin fushin aliyyu kenan tun yana yaro ,a hankali tana shafa bayanta har yarinyar ayi shiru da yake mai haquri ce bata da rigimako kadan matuqar ta qoshi Zaman sukayi tamkar na makoki na kusan minti talatin sanann tace"aliyyu tashi mu wuce gida dole su abba suji irin aika aikar da kayi,ya kada ki bayan ya bude idanunsa da suka koma ja ya kalleta"ban yi laifi ba wannan shine hukunci da yafi dacewa da ita,ni nasan me dame salima ta yimin bayan wannn tun alokacin ta cancan ci narabu da ita amma na daure"ya maida kasa kujera yana maida numfashi ya daga mata hannu alamun ta tafi kawai Ta girgiza ki tace "a'ah bazaiyi na qyaleka ki kadai ba kana cikin irin wannan mood din"ita tayi driving shi kuma ta bashi iftihal din ya riqe,ido sosai ya zuba yana kallon yarinyar tausayinta matuqa ke shigarsa yana tausaya mata na rashin dacen uwa da bata yiba ya rungumeta tsam tsam a qirjinsa cike da qaunarta Fa babu irin wanda momi bata yi ba tamkar ta ari bakin wasu,kamin abbansa ya dawo ya dora da nashi,ce masa auke ai haquri shine mafita ba saki ba,shi dai uffan bai ce ba don baijin koda salima ta dawo tofa ta rasa shi shi da 'yarsa har abada To kuma sai aka taki saa ko rashin saa zance ne?uncle abba me ya nuna dattako da kansa ya taka gidansu salima don yin bikonta,qara ra a gabansa abban ta ya nuna masa shifa ba ruwansa bazai tursasawa 'ya 'yansa ba don suna da 'yancin yin duk abinda suka ga ya dace da rayuwarsu,amma zai kira salima atambayeta idan zata koma to,da yake a cikin zafin kanta take a lokacin bata ji kunyar budar ido tace da uncle abba ba itafa ba zata koma ba"abban nat ya kalleshi yace"to kaji mai zaman tac3 bazata iya ba"abba bai sake tofa kanzil ba ya bashi hannu sukayi musabaha ya dawo gida Lamarin rayuwar gidan nasu yayi matuqar bawa uncle abba mamaki,rayuwar'yancin kai suke irin ta mai jan kunne?ba rayuwa ba irin ta addininmu wadda fiyayyen halitta ya koyar da mu ba?,wanna wane irin masifane da a yanzu muka qaqabawa kanmi?,bayan ya dawo ya sanar da momin yadda sukayi,ita kanta da ake mace abun ya daure mata kai amma kasancewarsu iyaye masu dattako da basu so dansu yayi saki sai ta nemi izini gun uncle abban akan ita ma zata je ko za'a dace"uncle abba bai hanata ba yadda mai akai da mahaifin salima exactly haka akayi da mahaifiyarta don aqidar duka iri guda ce Saidai ita an samu dan bambanci kasancewar salima tafara saukowa har ta fara kewar aliyun sai mamarta tace wa momi saidai aliyyun yazo da kansa,nan momi ta saka shi gaba akan lallai lallai ya shirya yaje,shi dai kullum yana binta ne da to don kuwa ya riga ya gama yankewa ransa cewq ko itace autar mata yq haqure mata don gaa daya