← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 84

Sashe 60

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kwankin kullum cikin kuka take kwana take wuni,a haka ma an samu sauqi saboda takan kaucewa idon anty hauwa don kada ta dinga jin ba dadi,damuwa sosai ta yiwa zuciyarta yawa,tana jimantawa kanta yadda soyayyar aliyu ta gama illata ta,saidai bata barin damuwar ta tsawaita mata da yawa ba ta tsananta yin addu'o'i,da taimakon hakan ta soma samun kyakkyawar nutsuwa cikin ranta,koda yaushe cikin kula da ita anty hauwa take bata barinta ta zauna ita daya bare ta damu sosai,sau da yawa anty hauwan idan tana bata haquri kunya fadilan keji "nifa babu wanda yayimin laifi don Allah anty ki daina bani haquri,kunya hakan yake bani wallahi" Yara kam murna suke anty fadila ta dawo gidansu sunata tsalle,idan akace babu makaranta to suna liqe da ita wani lokacin har sai anty hauwan ta kore mata su tace su barta ta huta,ita kam dadi take ji idan tana tare da yaran saboda dama can mai son yarance ita,sosai mamansu taja kunnensu da kada su sake su gayawa kowa cewa anty fadilan tana nan gidan saboda yadda taga suna rawar qafa zasu iya subul da baka Ita kanta tayi mamaki qwarai yadda ta soma ragewa kanta damuwa kan aliyun duk da yake ba abun mamaki bane addu'a ai tafi qarfin wasa,sosai tayi yaqi da zuciyarta,bata bari bacin rai ya rusata ba,da zarar ta soma tunane tunane zata datseshi ta hanyar daukan qur'ani ta karanta,idan ta gama kuma ta shiga shafukanta na sada zumunta,komai anty hauwa ta hanata yi,duk da hakan fadilan taqi yarda don kullum tare suke shiga kitchen yin lunch ko dinner,wani lokaci kuma ta shirya mata yaran da safe Gudu sosai ya dinga yi shi daya cikin motar,cikin ikon Allah ya sauka lafiya,saidai tun daga yadda su ya gana ke faman tambayar fadilan ya sare da al'amarin ya tabbatar bata garin ma baki daya bare gidan,sallah kawai yayi ya baro garin,bai damu da yawan tafiyar da yasha ba bare ya nemi hutawa har yaci abinci,juyin duniya ya gana tayi ya tsaya yaci abinci amma qeme me yaqi,ya bata haquri bayan ya ajjiye musu kudade masu dama yace yana da abubuwan yi masu yawa a kano,haka ya kamo hanya ya taho,gudu na ban mamaki ya dinga shararawa ba qaqqautawa,sai da yaji tuqin na neman gagararsa sannan ya samu wani shago kam hanya ya siyi yoghurt yasha,bai fasa gudun nasa ba wanda ikon Allah ne kawai ya kawoshi garin kano lafiya Kwana hudu bai cikin daidanshi,matansa mata ne marasa kulawa,tabbas sunga canji sosai tattare da shi amma babu wadda ta damu da tambayarsa mene damuwarshi,momi kam ganin baice komai ba yasa ta tsuke bakinta ta qyaleshi don ta sani ida dai ya soma zurfin cikin nan nasa bai gayawa kowa komai sai lokacin da yaga dama *G*idan anty hauwa shine gida na qarshe da hankalinsa ya kai kai,anan ya tattara dukkanin fata da tsammaninsa,duk da wata zuciyar na tantamar mai zaya kaita can bayan ko gidansu bata je ba?,qarfe biyar da shirin na yamma ya gama shirinsa cikin qananun kaya da sukayi matuqar yi masa kyau Suna kitchen ita da fadilan suna hada abincin dare sunayi suna hirarsu,yara suka jiyo wadanda suka bari a falo suna kallo da yake alhamis ce suna cewa "ina wuni uncle....ina wuni uncle" gaban fadila yayi mummunar faduwa ta saki mirfin hannunta da take shirin rufe miya da shi,"shikenan yau zan amshi takardar rabuwa da shi" abunda zuciyarta ke gaya mata kenan "anty aliyu ne"ta fada tana kallon anty hauwa dake tace shinkafa "aliyu?" Ta fada tana kallon fadilan cikin kasa kunne,"ina zuwa" anty hauwa fada bayan ta ajjiye tukunyar hannunta ta fice da sauri,komawa fadila tayi jikin drawer ta jingina bayan ta hatde hannayenta a qirjinta tana jiyo sweet voice din sa,batasan me yasa take jin qunci a qirjinta dalilin gaya mata da zuciyarta ke yi takardar sakinta aliyun ya biyota da ita Ruwa aliyun yace ma anty hauwa ta bashi,duk ruwan dake freezer din falonsu ya qare sai lemo,da hanzari anty hauwa ta miqe ta hau sama ta dauko masa a parlour din abban kausar don bata son ya shiga kitchen din,ji yayi bazai iya jiranta ba don haka ya miqe ya shige kitchen din,a hankali fadila ta bude idanunta da a da ke a lumshe,cikin jikinta take jin tahowar tasa,nan da nan tayi wuri wuri da ido tana neman maboya,a asukwane ta shige bayan qofar wadda a kusa da ita freezer din take Kai tsaye ya qaraso ya dage freezer din ya sunkuya yasa hannunsa ciki,cak ya tsaya da qoqarin ciro ruwan da yake yi,sai yake jin qamshinta cikin hancinsa,irin qamshin da ya ji cikin bargo pillow da undies dinta,sakun murfin yayi ya soma kallen kallen kitchen din yana neman ta inda qamshin ke fitowa,ko ina ya kai idanunsa sai yaga babu kowa,tuni fadila tayi surrender bayan qofa numfashinta kamar zai dauke musamman da taji ua jingina a bayan qofar ya kuma qin barin gurin,yafi minti uku cikim kitchen din yaqi fita din qamshin turarenta na ahlamul arab kawai yake ji,hat sai da anty hauwa ta shigo hankalinta a tashe tana tsammanin ya ga fadilan,sai ta tadda shi a tsaye kawai jingine jikin qofar hannayensa harde a qirjinsa,"ina ka shiga ga euwan can na kaimaka" "ok" kawai yace ya gewayeta ta fice daga kitchen din itama ta rufa masa baya Ta maida yara dakinsu daga ita sai shi a falon,zuba masa ido tayi sosai tana kallonsa canji qara ta hango tattare da alin,fara'arsa ta sake qaranci sosai,tsiyayar lemon kawai yake yi yana dirkawa cikinsa,yadda bai tanka ba itama bata ce kamzil ba har sai da ya tashi da roba biyu ta ruwa da lemo,ya dago kai ya kalli antin hadi da sakin ajiyar zuciya "ni wai uncle meke damunka?tunda kazo naga kamar a hargitse kake?"wata ajiyar zuciyar ya kuma saki "fadeelah nake nema mummyn kausar" kamar gaske ta nuna alamun rashin fahimta sosai "kamar yaya?fadilan da kuke tare,yaushe dududu sumayya ta ke gayamin kun dawo daga china zaka ce ita kake nema kamar wadda ta bata" "bata tayi....bacemin tayi"ya fadi yana jingina jikinsa da kujera,yayin da fadila dake labe cikin kitchen ta zaro ido jin cewa wai nemanta yake "yayimin me? Me zayayimin ne?"ta tambayi kanta ba tare da tasan amsar tambayar ba Ya dora cikin wata iriyar murya "tayi tsammanin bana sonta ne bayan nima na dade ina sonta,tayi zatin maqiyinta ne ni alhali duk duniya babu mai sonta kamar ni...ta dauka ina zaune da ita ne bisa dole bayan kan son raina nake zaune da ita.....anty ta yimin gurguwar fahimta,ta gujeni a lokacin da na qara zurfi cikin qaunarta....ta gujeni a lokacin da dukkanmu ni da ita muka fi buqatar kasancewa da juna"ita kanta anty hauwa baki ta saki tana tsammanin ba aliyu bane,aliyyun da tunda take tare da shi zata iya cewa bata taba ji ko ganin yana kwatanta qaunar da yakewa wata diya mace ba aduniya koda uwar 'yarsa,fadila kam dake cikin kitchen duburburcewa tayi,sai jikinta ya fara rawa qafafunta suka gaza daukarta ta lallaba ta ja jikinta ta zauna kan kujerar roba bakinta rufe da tafin hannunta yayin da hawayen da sukayi kwana da kwanaki tana qumshe su yau suka samu qofa. Lallai ma yaudararta aliyu keson yi?,dama shi din shahararren mayaudari ne,shine a yanzu zai furta cewa yana sonta?wanne irin zama ne basu yi ba baice yana son nata ba sai ayanzu?sai yanzu da ya kwanta da ita?,ya tabbata kenan jikin nata yake so kamar yadda tayi zato tun farko? (Illar zato),sha'awarta yake kenan ba qauna yake mata ta cikin zuciya ba?,kuka ne sosai mara sauti ya kufce mata yayin da shi din ma ke can zaune dirshan gaban anty hauwa yana fayyace mata irin zaman da sukayi da fadilan,kunne sosai ta saka tana jinsa duk da yake tamkar tishi yake mata,duk yadda fadilan ta fada hakanne harda wasu abubuwan da fadilan ta boye ta qi fada Kafin ya kammala tuni har qwalla ta cika idanunsa duk da bata gai ga zubowa ba amma qiris take jira,soyayyar 'yan uwan taka sai Allah tuni tausayinsa ya kamata don zata iya dafa qur'ani kan aliyyu bai taba shiga makamancin wannan halin ba akan wata mace,ta karanto gaskiyarsa qarara,don dama ko ada bai iya qarya ba tun yana qaraminsa,zai gaya ma gaskiya ne ko za'a tsireshi don haushi,to saidai bata jin kuma zata shiga haqqin fadilan ta karya alqwari da ta daukar mata don aliyyu nata ne,bata jin zata sarayar mata da haqqinta tunda nata din ne,ita ke da iko da abunta,ita kadai tasha haqurinta ita kadai tasan me ta hadiya Cikin sanyin jiki da qunar rai yace"wai anty roqona take na saketa,tana tsammanin sakin nata abu ne mai sauqi har irin haka a gurina?" Ya kada kai yana cewa"bazan iya ba,bazan iya furta wadan nan kalmomi gareta ba koda duka duniya zata taru a kaina" dole ka sake ni aliyyu dole mu rabu ,bani kake so ba jikina kake sha'awa" ta fadi haka qasa qasa cikin kuka mara sauti,ya miqe "zan tafi tafi tunda kema bata gunki zan ci gaba da nemanta",tuni ya juya ya fice daga gidan,tausayin dan uwan nata ya kamata don tasan wahla kawai qanin nata zaici gaba da sha tunda fadila na tare da ita Kifa kanta tayi kan cinyarta ta sake sakin wani sabon kukan mai dan qaramin sauti,wani qunci zugi da radadi data rasa na meye take ji cikin ranta,anty hauwa ta kama hannayen fadila tana kallin qwayar idonta "fadila.....fadila,naga abubuwa da dama cikin qwayar idanun aliyu,naga soyayya naga qauna cikin cikin idonsa irin wadda ban taba gani ya yiwa wata 'ya mace ba,kinji komai da kunnuwanki no need na maimaita miki" Kada kai fadilam keyi,"anty na yarda aliyu na sona a yanzu bazan qaryata ki ba,anty amma ba ni fadilan yake so ba wani abu dake gareni yake so,tun yaushe anty....tun yaushe nake tare da shi nake kyautata masa bai taba cewa yana sona ba sai yanzu?sai yanzu da wani dalili ne ya jawo hakan?...Thank god aliyu na sona yanzu anty,saidai ......is too late anty I already displaced him from my heart,na goge cikin kundin rayuwata zan rayu da shi" kalmar ta fito daga bakinta hade da hawaye Sai dariya taso kama anty hauwa amma ta gimtse,with confidence fadila ke fadin maganar saidai qwayar idanunta kadai ta ta qaryata ta,bata sani ba ita
Chapter 60 · 0% Book details