← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 84

Sashe 42

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mata kewa?sam ba zata iya wannan tsari nasa ba Sai bayan sallar isha'i ta samu nasarar tadda farida cikin bedroom dinta zaune gefan gado tana canzawa baby da taci sunan maman mubarak wato(aisha humaira)pampers ta zauna itama a gefan gadon tana duban pampers din da faridan me sawa humairar ,da fara'a farida ta juyo a fuskarta tana duban fadila zata dan tsokaneta sai fara'ar ta janye sakamakon qwalla da ta gani tana bin kumatun fadila tayi hanzarin sauke humaira da ta aza akafadarta tana cewa"lafiya sister?"tamkar ma ta tunzurata sai hawayen suka dadu Tafin hannunta take sawa tana share su da nufin tsaidasu saidai turereniyar fitowa ma suke abinsu,sai da farida tasa hannayenta ta kamo hannayen fadilan ta sa cikin nata sannan ta sake tambayarta,da qyar kuma cikin muryar kuka fadila ta bude bakinta tace"yanzu tsakani da Allah abinda aliyyu kemin yana kyautawa?"tayi tambayar wasu hawayen sabbi na shirin sake zubowa,farida ta sake fuskantarta a dan kidime tace"meke faruwa sister me ya miki?"ta girgiza kanta cike da damuwa"wai china zai dauke ni mu tafi har kuma na tsawon wata hudu Sai farida ta sake ta hadi da sakin dariya tana tafa hannu" yanzu sister fadila wannan abun farincikin kikewa kuka kamar wata teddy?"fadila ta katseta"ba zaki fahimta ba farida kwata kwata wata na nawa da soma aikina?"farida ta sake dubanta" aikin banza sister fadila,ga inda zaki samu aljannarki kike zancan wani aiki"sake girgiza kai fadila tayi"still farida baki fahimceni ba,zan gaya miki abunda babu wanda yasan yana faruwa sai ke,har yau sister aliyyu bai sona,aliyyu bai qauna ta kalma mai dadi bata taba hada ni da shi ba kallon arziqi bai taba shiga tsakanin mu ba amfani na daya agunsa shara da girke girke tamakar wata 'yar aikinsa tun muna kusa da iyaye kenan tun muna qasarmu kena ina ga nabishi can wata uwa duniya mai kuma kike zaton zai faru a ni?" Ga mamakin fadila sai taga farida tayi murmushi mai kaa da dariya sai fadila ta saki baki tana binta da kallo tan tsammanin farida bata damu da halin da zata tsinci kanta ba kenan ko yaya?,sai da ta gama dariyarta sannan tace" bravo! bravo! bravo!,wallahi aliyyu yayi miki gata ba da qarami ba"zaro ido fadilan tayi har ya mamakin bai sake ta ba ,ganin haka yasa farida ta kama kafadar fadila ta sake juyowa da ita ta fuskanceta sosai,ganin yadda fadilan ta tsure sai ya sake bawa farida dariya daga baya kuma sai ta dawo serious dinta ganin kallon sakarcin da fadila ke mata,ta kuma kama hannunta sannan tace"ni na gano abinda qila ke baki gano ba,kuma ba zaki gano shi ba yanzu,sister duk abin ya aliyyu koya nuna ko kada ya nuna ko ya yarda ko kada ya yarda kina da muhammanci da wani tasiri a rayuwarsa komai qanqantarsa koda kuwa ya qaryata hakan da bakinsa,sister a iya hangena da tunani na na fuskanci cewa don kada ya aliyyu yayi missing girkinki ne baya so yayi nesa da abincinki wanda yasan zaiyi wuya ya samu kamarsa nima shaida ce"ta qarashe maganar cikin sigar tsokana wadda ta zame mata jiki Ta nuna fadila da yatsa sannan ta dora ke zaki canza wannan manufar ke zaki sauyata da kanki,ke zaki canza wa aliyyu wannan lafazin nasa na bazai soki ba har abada ki qaryata lafazin nasa ta hanyar nuna masa ba wanda *_yasan gobe_* sai Allah,sosai ta gamsu da maganar farida dari bisa dari kaso sittin cikin dari na damuwarta ya tafi,ta jinjina kai hadi da sakin ajiyar zuciya sannan tace"batun aikina fa sister?" "So easy"inji farida ta gada tana murmushi "k8na iya daukar excuse a gurinsu ki musu bayani tafiyar gaggawa ce ta sameki zuwa china zaki ajiye aiki amma da manufar zaki je course ne na wata hudu,idan hakan bai samu ba su barki a matsayin wakiliuarsu ta qasar china ta tsawon wata hudu" "great sister!"fadila ta fada cike da farinciki,tabbas dan uwa na gari dadi ne da ahi gashi xikin 'yan mintina qalilan ta warware mata damuwarta,ta rungume faridan tana cewa"thank you sister ya barmu tare ya raya mana humaira"tace "amin Allah yasa kema ki samo mana tsarabar dan china nan da wata tara ko goma mu dauki sabon baby " dariya sosai ta bawa fadila tana jinta ne kawai Sanda ta dawo gida yana zaune cikin balcony dinsa,tayi maza ta dauke kai gami da qara sauri don ta shige shi Washegari qarfe 6:40 pm ta dawo daga aiki sun gama settling komai da managing director na express da freedom sai damuwarta ta sake raguwa qwarai da gaske,tana toilet din falo tana wanka taji moysi kadan kadan a falonta,da sauri ta kammala tana son taga waye don a bude tabar bangaren nata,kacibus sukayi da shi tsaye yake tsakiyar falon yana sanye da kufta dark coffee wadda tasha aikin sarauta sai hukarsa baqa abinka da fari sai yayi matuqar kyau kyansa da jaskensa ya sake fitowa shigar ta amshe shi sosai fadila ta lumshe idonta tana jin wani abu na zagaya jikinta"ki shirya na kaiki gida ki masu sallama,gobe zamu bi jirgin yamma insha allah zamu wuce china"duk maganar nan da yake idonsa na kan wayarsa dake hannun hagunsa damansa kuma cup ne cike da maltina mai sanyi ,ta dan langabe kai kamar bata ji mai yace din ba"ina zamu je?""kaiki zanyi na siyar"ya fada yana ci gaba da danne dannensa ta faki idonsa ta manna masa harar ta zagayeshi ta wuce zuwa bedroom A sanyaye ta kammala shirinta cikin atamfa dinkin riga da zan8 simple style hakanan fadila take bata fiya son abimda ya cika ado da yawa ko daukan hankalin jama'a ba yadda take bata da hayaniua haka dabi'unta suke saidai idan ta so,ta lullube kanta da wadataccen mayafi kalar kayan,ta jawo locker dintabta debo kudaden da suke ciki ire iren kudaden da aliyyun ke basu ne duk qarashen wata da kuma na cefane acewarsa tunda komai suna da shi a ajjiye hatta magi ba zasu buqata ba ta watsa su cikin jakar sannan ta rataya ta ta fito,yana zaune a mazaunin driver tasan bata isa ta shiga baya ba ko ya shiga zai maidoto ne gaba don haka ta bude gaban ta zauna,yadan kalleta hadi da dauke kai ya daga glassan motar gaba daya sam ya rufe su ruf hadi da kunna a.c,wani irin tuqi yake slowly tamkar baza'aje ba tayi tsammani zaiyi irin tuqin nan nasa mai gudun tsiya,a hankali suke ratsa titi nan har suka qaraso cikin anguwarsu fadila Muje zuwa masu karatu Mrs muhammad ce [10/16, 1:50 PM] Salma *WA YASAN GOBE?...* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *part 2* A qofar gidansu yayi parking,bata ce masa komai ba kamar yadda bai tsinka mata ba,ta bude murfin motar ta nufi bakin get din gidan cikin doki ta dan tsaya suka gaisa da malam mai bude masu qofa idan zasu shige da motarsu Parlour din babu kowa sai qamshin fresher da ya gauraye da na girki ,murmushi fadilan tayi kai tsaye ta nufi kitchen cikin zuciyarta tana cewa"ummi na bakya tsufa kullum gida kamar na budurwa" (haka haj amina take ma'abociyar tsafta ce da gayu,don bata yarda wai don tana da manyan yara harda jikoki ta zauna haka ba,baka raba qafarta da hannunta da jan lalle mai ado irin na yanzun wanda akeyi,hakanan kullum kalolin girkinta daban ne masu dannkaren dadi hakan ne yasa yaranta sukayi gadonta suma,tun aurensu ita da alhj abbas koda wasa bai taba tunanin qaro aure ba donba cewarsa ta isheshi duk dashi qarin aure qaddara ce rubutacciya idan Allah ya qaddaro maka sai kayi Muhammad ta tarar ciki riqe da babban spoon na qarfe yana ta faman juya fried rice,dariyar da fadila ta tuntsure da ita ita ta saka shi juyowa don bai ankara da shigowarta ba sai lokacin,ya saki murmushi yace"anty fadila yaushe kika zo?" Ta kama baki" ina zaka san na shigo ka taqarqare kana ta jagwal gwalawa ummi abinci,wai yaushe ma ka fara shiga kitchen?"ya saki spoon dinnyana share zufa a goshinsa" ni wallahi ma gwara da Allah ya kawomin dauki ,please anty karbi girkin nan,haka yanzu ummi kemin ko ta daina sona ne ma oho?,amma don Allah anty fadila ina ni ina wani kitchen?,wai gwara na iya tunda ku kun tafi saura ni da ita kawai a gidan"dariya fadila ta sake saki ,ta qaraso kan girkin tana gyara wasu abubuwa sai da ta hada komai ta rufe ta rage mata wuta don ta turara sannan ta tambayeshi ya haye saman freezer yayi zamansa"ina ummi" "tana gun Abba yanzu ya dawo daga kasuwa ne amma tunda an fara kiran sallah yanzu zaki gansu" Yana rufe baki kuwa saiga dariyarsu cikin falo,da hannu Muhammad yayi mata nuni da falon cikin salin gulma,dariya ma ya bata ta miqe da sauri ta isa falon,ita da abban ne kuwa yana tsaye riqe da abun sallah ummin kuma na dauke da hularsa,da murmushi suke kallonta ta durqusa ta gaida su abban na tambayarta yanzu take tafe?,ta gyada kai yace masha Allah ya mai gidan?,tace abba tare muke yana waje,"ashshsha banda abin fadila shima ai gidansu ne amma don sakarci kika barshi a waje "ummi tayi saurin qwalawa Muhammad kira tace ya zo ya shiga da shi,abba yace barshi naje na sameshi in yaso idan mun idar da salla sai mi shigo tare,a shirya mana abinci kafin mu shigo din Ummin ta dan rusuna tana miqa masa hularsa tace"insha Allah abban Muhammad a dawo lafiya"ya karba yana dora ta a kansa yace "Allah yasa Allah yayi miki albarka" cikin dariya yaran suka taya ta amsawa da amin Sai da fadila ta taya ummin suka shirya komai kan dining sannan suka tafi yin sallah ummi ta ahige dakinta fadila ma tsohon nata dakin ta bude ta shiga,bin dakin tayi da kallo komai yana nan kamar yadda yake,dan fridge dinta na boye ice cream 'yar kwanar da take ibadunta,inda take boye kanta idan zatayi kukan Aliyyu,sai komai yake dawo mata"Allah sarki" ta fada a fili tana shafa filonta da take cusa kanta a qasansa ,qwalla ta dan taran mata a ido ta sa yatsanta ta dauketa,toilet ta tura ta shiga ta daura alwala ta dawo inda ta saba yin sallarta tayi,bayan ta idar ta duba kan mirror dinta powder ce kawai akai ita ta dauka ta sake gyara fuskarta sannn ta
Chapter 42 · 0% Book details