← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 84

Sashe 45

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsammanin ta yaba zuwa,ya dawo da baya a hankali ya isa ga makunnin na'urar dumama daki ya kunna ta ya sake juyawa ya zuge gami da rufe duk wasu qofofi windows da labulaye dake abude na gidan sannan yasa kansa ya fice hadi da sa key ya kulle gidan A hankali ya soma bude idanunta tanajin yanayin dakin ya sauya mata,sanyin da ya takura mata dazu da zata kwanta ya ragu sosai da sosai,ta kasa tashi illa idanunta dake bude tayi zuru tana jin yadda cikinta ke qugin yunwa,idan bata manta ba rabonta da abinci tun a nijeria sai drink da take ta sha har acikin jirgi Wanka a qa'ida take da buqatar yi da ruwa mai zafi don ta samu ragowar gajiyar ko zata sake ta amma rashin ganinsa afalo yasa take tsammatar yana bedroom din,kasa kunnenta tayi sosai bata jo motsin kowa ba don haka ta miqe akasalance,cikin sanda ta tura qofar bedroom din ,babu kowa ciki daki ne babba yalwatacce ba wani tarkace cikinsa cupboard ce sai dressing mirror hadi da dressing chair sai sofa qwaya daya madaidaicin gado ne mai rumfa wanda aka kafashi daga jikin window sai center carfet da center table daga gaban gadon kenan,komai na dakin shima farine kamar dai falon hatta da kalan furniture din zuwa ga bedsheet Ta sako kanta ciki bayan ta tabbatar babu kowa akwatunansu na saman gadon a ajjiye nashi akwatin ne ta gani a bude kayan sun dan hargitse kadan da alama ya bude ne ya debi wasu abubuwa,gefe ta zauna ta fiddo da duka kayan nasu ta shirya su cikin cupboard,nashi ne auka cinye fiye da rabinta ta tsaya tana kallon yadfa kayan suka tsaru ita kanta sun burgeta ta karkade hannayenta ta rufe qofofin sannan ta shige toilet din bayan ta ciro kaya kala daya da zata sanya Ta fito daure da towel wanda ya sauko mata qasan gwiwarta yayin da ta yafa qaramin saman kanta tana goge ruwan da ya dan taba mata shi da wanda ya shigar mata kunne,sam bata yi tsammanin ya shigo dakin ba shi din ma haka yana zaune ne kan bedside hannunsa riqe da lemon kwali yana dan zuqa kadan kadan ,gabanta ya fadi sosai don ta tsorata da ganin nasa,da azama ta juya don komawa toilet din garin haka towel din kata ya zame ya fadi qasa kanta zuwa kafafunta suka fito sarari,gashinta ya kwanta luf bisa dan dogon wuyanta zuwa gadon bayanta wanda ruwan da ya tabashi ya sake sashi kwanciya,da sauri ya dauke qwayar idanunsa ita kam ko ta kan towel din bata bi ba ta koma hadi da tura qofar Ta hudar dan maqulli take leqensa tana gani ya daga lemon maimakon shan ganin dama irin na dazu dai taga ya daga kwalin bai sauke ba saida ya daddake shi tas sannan yayi cilli da kwalin yayi qas da kanshi yafi Minti guda ahaka sannan ya miqe da sauri ya five a dakin,sai da tabbatar ya fita sannan ta fito da sauri ta sawa qofar key sannan ta shirya cikin doguwar riga mai dogon hannu cotton ce sosai ta yane kanta da mayafi ta duba jakarta don dauko turarenta na shamsul imarat da blue lady Kaf jakar ta lalube da hannunta ta nemi su sama ko qasa ta rasa,cikin shakku ta zazzage jakar gaba daya babu babu blue lady din babu shamsul imarat din sai wani da ta gani cikin kwalba cikin takaici take kallonsa tasan dai ita ta sayeshi amma ta manta a ina?,ta zumbura baki tana maida kayan da ta zazzage din cikin jakar,ta dauko shi shima zata maida saita shanshana"ba laifi shima qamshinsa"ta fadi haka tana ajjiyeshi a gefanta Kuyi haquri da aliyyu kudai kuci gaba da bina komai daki daki yake a rayuwa Na gode Mrs muhammad ce [10/16, 1:53 PM] Salma *WA YASAN GOBE?...* *written by safiyya Abdullahi musa huguma* *part 2* Ta dade a tsaye tana takaicin rashin sako turaren nata da batayi ba don gaba daya tayi tsammanin ta sako su,taja tsaki yafi a qirga ita ba sanin gari tayi ba hasalima yau ta soma shigowa qasar ko da ta sani din ma ai dole sai dai ta yiwa aliyyu magana wadda ita kuma hakanne bata so,to idan kuwa haka ne bata da zabi illa saka wannan turaren tunda sam bata son zama a rayuwarta ba tare da taji jikinta na tashin qamshi ba haka take qamshi a jininta ya ke,ai shima wannan din turarene,sam fadila ta mance aikinsa tama manta a inda ta sayeshi tunda abun bai gabanta tunda ta wulla shi a jaka ta manta da babinsa Ta kammala shafawa tana lumshe ido gami da cewa "hmmmm" saboda yadda qamshin nasa ya yi mata dadi sosai,qanshi ne mai sanyi ya karade jikinta da ma dakin gaba daya,ta maida shi cikin jakarta ta rataye jakar a abun rataye jakankuna ta jawo qofar dakin ta dawo falo,yana zaune a gaban laptop dinshi (agogo sarkin aiki )cewar fadila cikin zuciyarta,aliyyu hardworking person ne komai yasa a gabansa yakan zama serious akai har sai ya kai ga cimma burinsa,yana jin fitowar tata amma bai daga kai daga abinda yake ba bare ya dubi sashenta Sannu a hankali qamshin ya soma karade falon ya soma kuma fisgar hankalinsa,ya rasa daga inda qamshin ke fitowa,sannu sannu kasala ta soma rufeshi idanunsa suka soma lumshewa,ya daga kansa ahankali ya dubi sashen da take waya ce a hannunta tana danne dannenta saqonni take dubawa da suka shigo mata,ya maida ido runtse sosai yana qaryata kanshi game da feelings din da yake ji,ya sani tun usul haka halittarsa take yana daga cikin mabuqata,gaba daya ya mance da wannan matter din sanda zai taho aiki ne kawai a gabansa da kuma tsaftar inda zai zauna da abincin da zaici Cikin lokaci kadan mood dinsa ya canza sosai he needs something really, idanunshi sun jima a rufe aikun da yake ya gagareshi saidai still mood din da yake ciki bai canza ba,ya sake kallonta karo na biyu bata san ma me ake ba har yanzu wayarta na hannunta tana latse latsenta,"take dis bags ki samin nawa a plate ki dauki naki Juyowa tayi don jin muryar tamkar ba tasa ba,amma sai taga latse latse yake bisa laptop idanunsa na bisa screen din,bata ce komai ba ta ajjiye wayar a gefanta ta debi kayan ta shiga kitchen,shawarma ce da Chinese spaghetti sai roasted chicken ta saka kowanne a aplate din ta hada masa da ruwa da lemo ta jawo dan side table gabansa ta dora masa akai,zuwanta gabansa ya sake sa qamshin ya cika masa hanci,ya sake runtse idonsa hadi da qanqame hannayensa gu guda cikin wani irin lust moode,sam bata lura ba ita dai ta kammala hada masa ta dauki tata ledar ta koma mazauninta,duk yadda ya kai ga son cin abincin haka ya dinga tsakurarsa a kasalance girman kai kuma ya hanashi ya sake koda duban sashen da take Ta sake duban agogo karo na uku kenan sha daya da rabi na dare ,tuni bacci ya sake cika mata idanu kamar ma batayi shi dazun ba duk da dama ba wani jimawa tayi ba ta farka,tunaninta daya ko ina makwancinta? Tasan dai ko giyar wake ta sha bata tafiya kai tsaye su hada dakin kwana da aliyyu ba bare ya yarfata kasa daurewa baccin da take ji tayi saboda haka ta ware mayafinta ta lullube kafadarta zuwa qafafunta ta ja filin kujera qwaya daya ta tada kanta da shi tunda shi kam lura aikinsa yake tuquru hadi da amsa kiran dake ta shigo masa wanda dukka da harshen turanci yake maganar hakan ya tabbatar mata yan qasar ne masu kiran,batasan yayi hakanne bane ko zai samu feeling da yake ji ya sake shi shi uasa ya takura kansa da aiki,ba abunda yake sai faman dirkawa cikinsa coffee flask guda ta hada masa amma ya kusa tafiya abun har yaso bata tsoro Tsaye yayi a kanta baccinta take sosai,bai taba qarewa fuskarta kallo ba irin yau,gashin gaban goshinta ya sake kwanciya kamar relaxer ta shafa masa komai nata medium mai kyau tamkar ma ba baccin take ba,a hankali abun nan da yake son ya danne ya ci gaba da taso masa,ya tabbatar idan yaci gaba da kallin nata a yanayin da yake ciki din nan zai iya aikata abinda yame ganin ita din ta masa kadan ta iya daukarshi gane yake zai iya nakastata,ya janye ida nunsa daga kan fuskarta yana maida numfashi,yasa hannunsa ya zare filon da take kai kanta ya sauka saman kujerar Firgigit tayi ta farka don ta dan tsorata ya kalli idanunta wadanda bacci da ta soma da tsoratar da tayi yasa su sukai wani kyau ya dauke kansa gefe guda zuciyarsa na dan bugawa da sauri, ganinsa tsaye bisa kanta yasa ta dan sukuyar da kanta "idan kinga dama ki koma bedroom ki kwanta"ya fada yai gaba hannunsa dauke da cup da flask din tea Ta dauki a qalla minti talatin a zaune tana doubting din aliyyu ne kuwa ma ya tasheta?idan shi din ne ma ya zata iya kwana daki guda da aliyyu? Aliyyun da yaqi jininta? Bai sonta bai qaunarta?,wani benefit nata kawai yake so tayi masa girki da shara ba wai ainihin ita fadilan ba,ganin babu mafita ga wani sanyi da yake sirarowa falin saboda kashe na'urar falon da yayi ya sanyata miqewa jiki a salube ta njfi bedroom din Kamar wata munafuka ta tura ta shiga,ga mamakinta yana kwance ne aqasa saman dan qaramun carfet din nan na gaba gado mai dauke da center table ya sauke center din shi kuma ya maye gurbinsa,trouser ne kawai ajikinsa da singlet,yayi ruf da ciki,hannun hagunsa da damansa duka pillow ne ya jajjerasu ya kuma matsesu ajikinsa,faffadan bayansa mai cike da siffar qarfi ya bayyana,ta dauke kanta cikin sanda ta zagayeshi gami da hayewa kan gadon tana mamaki cikin ranta shi kam wannn baijin sanyin garin nan ne? Ga kuma sofa a dakin doguwa amma bazai hau kai ba?bata da courage din da zata magana don haka ta maida gulmarta ciki ta tattara tafukan hannayenta tayi addu'ar bacci ta shafe ilahirin jikinta da ita ta jawk bargon ta rufa tayi matashin kai da hannunta kasancewar duka filon dake kan gadon aliyu ya kwashesu zasu taya shi kwana Idanunta fes a kansa
Chapter 45 · 0% Book details