← Book details Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 84

Sashe 1

Waya San Gobe Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data Normal [10/16, 12:17 PM] Salma Wa yasan gobe? safiya Abdullahi musa huguma Zaune take dirshan bisa carfet din dake mamaye da qaton dakin nata,ta tanqwashe qafafunta yayin data tallafe kumatunta da dukka tafin hannunta,lokaciguda kuma ta zubawa food flask din abincin dake gabanta ido,a zahiri idan ka dubeta zakayi tsammanin flask din take kallo sai dai sam ba haka bane zuciyarta da ruhinta sun lula wata duniya ne ta daban,da yunwa ta shigo gidan saidai sam ta kasa sa koda loma guda ta abincin a bakinta,cikin kwanakin tana cikin wani yanayi wanda ta kirashi da jarraba ko musifa dake tunkaro rayuwarta Wannan ne karo na hudu a rayuwarta da idaniyarta tayi tozali dashi saidai ya zame mata masifa,tun daga ranar da ta dora idonta akansa wani baqon lamari ya ziyarci zuciyarta da gangar jikinta,zata iya kiran lamarin da zazzafan so wanda ya zamto mata tamkar harara a duhu,dalikinta na fadar haka kuwa shine wanda zuciyarta ke budurin a kansa baisan Allah yayi ruwan halittarta ba a doron duniyar subhana,tayi kukan tayi takaicin yadda zuciyarta tayi mata rashin adalci ta hanyar kamuwa da soyayyar wanda batasan koshi waye ba?,meye sunansa?,a ina yake?,taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta jawo flask din ta bude da niyyar taba wanu abu a ciki kota tsira daga fadan umminta,ilai kuwa tana loma ta biyu taji sallamar ummin tana daga tsaye ta dubeta tace"yanzu fadila tun shigowarki kika damemu da zancan jin yinwu amma kusan aqalla awa guda banga wani abun kirki da kika ci ba?,tadan yamutsa fuska tace wlh ummi da yunwar na shigo amma kinga na kasa ci"ummi tace ,haka dai kika iya kullum kamar wata qanqanuwar yarinya sai anyi fama dake akan cin abinci ko?,yayi miki kyau ai kinsan ulcer dai ba gidanku daya ba bare kice idan ta kamaki zata miki sassauci,tayi dan murmushi tace kiyi haquri ummi insha Allahu yanzu zan kawo miki flask din empty,ummin tadan harareta tace ai jikina kunne ne,fadila tadan qumshe dariyar da keson subuce mata,har takai bakin qofa ta juyo tace"af na manta ki shirya yanzun zaki kaini gidan alh salim kwana biyu su shiru muma shiru"tadan sosa kanta dake a tsefe saidai ta tufke shi da band tace anya ummi zan gane ma gidan?,ungo wannan ja'ira cewar ummi da ta watsa mata daquwa yace"nima in banda abbanku yace in tafi dake zaki maku siyayyar kayan make up da da driver zanyi tafiyata"tayi ko saurin miqewa tace yauwa ummi dama jiya nayi masa zancen kayan,tace ato minti goma ki sameni ina falo ina jiranki,ta amsa tana qoqarin shiga toilet dinta dake manne da bedroom din Tsaf ta shirya cikin abaya baqa mai sulbi saqar qasar dubai wadda aka mata ado da jajayen dutsina masu sheqi,ta nannade tulin gashinta tayi a cuci dashi sannan tayi rolling da wani dan kyakkyawan jan mayafi,simple make up tayi amma kasancewarta tana da wani sassanyan kyau sai ta fito gwanin sha'awa,ta daura agogo na fata ja sai plate shoe da tasanyawa qafarta mai ja ne mai baqaqen igiyoyi,wayar hannunta kawai ta dauka hade da key din motarta ta sake kallon kanta a madubi,cikin zuciyarta ta qaryata masu cewa abu mai duhu baya giwa baqi kyau,duk da cewa ita din ba baqa bace irin matan nan ne masu launin fata(chaculet colour)wasu kuma suce black beauty,fatarta batayi haske can ba kuma kai tsaye ba zaka kirata baqa ba tamkar irin black american haka yanayinta yake,fadila nada wani irin kyau mai sanyi wanda tashin farko bazaka gama tantance kyawunta sai kuna tare wato qananun kyau ne da ita,ba abu mafi daukan hankali a tare da ita irin qirar jikinta cocacola shape,idanunta manya masu dauke da gazar gazar din gashi wanda hakan ke taka muhimmiyar rawa gun tafiya da zuciya gami da ruhin mazaje da dama,goshinta kam irin qananun Gashinnan ne kwance luf wanda ko tayi dauri basu boyuwa,muryarta a sanyaye take cike da wani sirri wanda idan tayi magana take janye hankalin jama'a da dama,fadila tako ina Allah ya bata zubi da tsari wanda yasanya take burge mutane ba maza kawai ba hatta ga yan uwanta mata ma,sai dai gwanar miskilanci ce,sam magana bata dameta ba,tafi ganewa tayi karance karance maimakon zaman tadi,fadila yanzu haka daliba ce a jami'a bayero kano tana karantar mass com,duk da cewa abbanta yayi mata sha'awar karantar medicine ganin cewa mass com bana mutum ne mara son magana ba amma data nuna masa tafi sha'awar mass com din sai ya barta da zabinta kasancewarsa mutum ne mai sauqin kai,sai ya maida zabin nasa kan 'yar uwarta farida,alh abbas ahmad shine mahaifin fadila dan kasuwane mai rufin asiri,domin Allah ya bashi wadata irin wanda ko wane dan adam ke fatan samu ba abunda aka nema a gidansa a ka rasa,asalinsa bafulatanin bauchi ne,yana sana'ar sai da shaddodi da yadiddika cikin kasuwar kwari,yakan tura babban dansa wasu lokutan china ko india domin shigo da kayan su kuma zuzzuba a shagunansu dake cikin kasuwar,ya auri mahaifiyarsu haj amina a maiduguri cikakkiyar shuwa ce wadda Allah ya qaddari aurensu tun bayan da yayiwa manemanta dintinkau a zuciyarta,anan garin kano suka ci gaba da zama tunda anan kasuwancin nasa yake,haihuwar farko suka sami da namiji inda yaci sunan ahmad,baiyi wani tsawon rai ba Allah ya karbi abinsa,shekara daya tsakani suka sake samun wani yaron aka mayar masa da sunan ahmad din,daganan haihuwar tayi musu dif tamkar aun daina,wanda a tsakanin har amina ta soma fuskantar qananun maganganu irin na dangin miji duk da cewar ba a kusa suke ba,sai bayan shekaru goma Allah ya sake qaddara musu samun wata haihuwar,ta haifi 'yar kyakkyawar budurwa taci sunan fadila,shekara biyu tsakani Allah ya sake kawo wani rabon nan ma mace ta haifa aka sa mata farida,kasancewar fadila mara saurin girma sai suka taso kai daya da farida idan ka gansu zakayi tsammanin twince ne don kamarsu daya saidai farida tafi fadila garin jiki da kuma farar fata,tasowarsu tare yasanya komai daya ake musu hatta makaranta tare aka sanya su,sai da suka shiga jami'a ban bancin course ya raba su,shekara shidda da haihuwarsu umminsu ta sake haihuwar da namiji inda aka sa masa muhammad tun daga lokacin kuma haihuwar ta musu bankwana Babban wansu ya ahmad yayi aure tuni da matarsa anty hafiza harsun samu albarkar twince duka mata ,rayuwar gidan rayuwa ce mai ban sha'awa cike take da son junansu suka taso girmama juna da qaunar juna,sai dai tsakanin fadila da farida akwai tsokana fada da wasa na tsakanin sakuwa da sakuwa sai dai duk da haka farida na respecting din fadila S.A huguma [10/16, 12:18 PM] Salma Wa yasan gobe? Safiya Abdullahi musa huguma Sun fito kenan daga gidan farida ta shigo da motarta layin (da yake ya ahmad yayi qoqari bayan kammala secondry sanda suka samu admission a jami'a ya sai masu yan qananan motoci rio,yace tunda fadila baqace ta dauki fara farida kuma ta dauki marun)farida ce ta soma jan burki ta tsaya don tasan halin mutuniyar zata iya shigewarta tace"ummi ina zaku je?" "Gidan alh salim kwana biyu haduwa tayi wuya shine zanje dubasu"cikin tsokana ta kalli fadila tace "wlh ummi gwara da kika banbaro kifin rijiyar nan kika fito da ita inaga tafi shekara dubu bata je gidan uncle abba ba"fadila ta watsa mata harara tace"ni sa'arki ce"ta qyal qyale da dariya tace sorry yaya fadila"fadila tayi saurin yiwa motar key suka wuce,suna tafiya a hanya suna hira jefi jefi da ummi abinsu gwanin sha'awa har suka isa gidan,gidan na jerin gidajen kundila housing estate dake maiduguri road,gidane irin na masu naira da suka ci suka tada kai,mai kula da qofa ya dage masu wakeken get din gidan cikin fara'a suka shige kasancewar akwai sanayya mai yawa tsakaninsa da ummin Ummi ce a gaba fadila na binta a baya har suka isa tafkeken falon gidan ,haj maimuna na zaune bisa luntsuma luntsuman kujerun dake kewaye da falon kallo suke ita da yaranta sumayy da rabi'ah,sallamar su ita ta dauki hankalin su suka juyo hade da amsa musu,haj maimuna ta miqe cikin girmamawa tana cewa lale marhabin haj kune tafe da yammarnan ,ummi tayi murmushi tace ai kuwa dai kam"ta sake fadada fara'arta tace sannunku da zuwa ai......,maganar haj ta katse ta kama baki tace"a'ah yarannan yau yaushene?,ta fadi tana kallon fadila,dukkansu sun fahimci me take nufi suka qyal qyale da dariya suka ce momi yau laraba,ta gyada kai tana cewa lallai ba shakka ta bawa ranar samu,wlh haj bazan iya lissafa yaushe rabon fadila da gidannan ba,"ummi tace"hmmmm to wlh yauma da qyar na banbarota don taji zamu biya store ne zata kwaso kayan make up shine ma qarfin biyonin"momi ta sake gyada kai cike da mamaki tace lallai yau mun tashi da bismillah haj ku zauna mun tsaya zance na barku a tsaye,dukkansu suka zauna sannan suka fara gaisawa fadila ta gaida momi a kunyace ,ta amsa mata tana cewa"kyaji kunya mana mara zumunci ,sam farida ta fiki zumunci "sumayya dake kusan sa'a ga farida tace"wlh anty fadila faridammu ta fiki zumunci"fadila ta dan harareta da taga idonsu ummi baya kansu tace"ta dai fini qafar yawo yaufa sai da zamu fita ta dawo tun azahar wai ta tafi gidan qawarta "sumayya tace "to ai zumunci taje"fadila ta dan tabe baki tace"ke ni qyaleni yawon farida yafi qarfin qafata ko ina a kano kika kwatanta mata ta sani "sumayya da rabi'ah sukai dariya suka ce "kai anty don dai ke bakison fitarne shi yasa kikace sister ta fiya yawo" Hira suke suka tsinci qanqanuwar muryar yarinyar na sallama ,ta saki hannun wanda ya riqota da gudu ta fado falon,momi ta cewa wanda ya kawota din sannu isah,yace yawwa haj ya juya ya fice,rabi'ah tace oyoyo ifti na,muga kitson,da gudu ta fada cinyarta ta janye hular da ka rufe mata kanta da ita tana nuna mata,kalbace mai kyau twisting wadda aka lafe jelar ta da beads masu kyau,kasancewar yarinyar nada tsawon gashi sai ta kwanta lub tayi kyau har dokin wuyanta,tace anty sumy tayi kyau"sumayya tace gsky qawata ba magana "ta bata hannu suka tafa,ta miqe tayi gun momi ganin ummi yasata duqawa ta gaidata,ummi ta amsa fuskarta dauke da fara'a momi tace"har yanzu fushi ake kenan da ni shi yasa ni baza'a nuna min kitson ba"cikin magana irin tq shagwababbun yara tace "ba cewa kikayi ayimin mai
Chapter 1 · 0% Book details