← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 93

Sashe 93

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Bayan shekara 蓷aya
zaune nake a parlour natasa katon ciki na gaba Ya SALEEM ne suka shigo shi da Naseem da Nasmah da Ahmad.
tun kan ya karaso yake bina da murmushi yaran ko da gudu suka iso in da nake zasu zube kaina, da sauri Ya SALEEM ya 蓷aga kafa ya taro su yana fa蓷in
"Kai ku tsaya kada ku danne baby ciki mana,
ku zauna a nan." ya zaunar da su gefe kana ya zauna gefe na tare da shafo ciki na ya ce
"Wai yaushe zaki haifo mana babyn mun masu mu gansa fa."
baki na turo nace "Nima na matsu na sauke na huta."
Naseem yace "Mommy yaushe zaki zamo mana baby." baki na turo banyi magana ba
Ya SALEEM ya蓷an yi karamar dariya yace
"Bashi amsa mana,yauwa Naseem me kake so a haifo mana mace ko na miji?."
baki ya washe yace "Namiji."
yace "To Aunty Nasmah fa me kike so a haifo mana?."
tace "Daddy na mace."
ya ce "To duk naji naku saura na my Ahmad 蓷ina, kai me kake so?."
yace "Mace na miji."
dariya mukayi dukan mu nace "To kai duka kake so mace da na miji kenan."
rungume shi Ya SALEEM yayi yana fa蓷in
"I love You my son Allah ya kawo su masu albarka irin ku."
dariya nayi ina kwantar da kaina jikin kafa蓷ar sa,
gefen fuska ta ya shafo yace "Inayi miki son da baki ba zai iya furta wa ba, idanuna na lumshe ina sakin murmushi,
nikam nasan nayi dace a rayuwa ta da kallamar sona Ahmad ya mutu gashi a yau gorzo jarumin maza ABDALLAH IDRIS ABDALLAH yana fa蓷a min girman son da yake min a zuciyar sa wan da baki bazai iya furta wa ba sabo da girman sa.
hakika ni HAMDAH nagodewa ALLAH...............!

TAMMATBIHAMDILLAH

Ina godiya wa tabaraka ma 蓷aukaki mabuwayi mai izza da ya nuna min wannan rana da littafin nan ya kawo karshe,
ina yiwa 蓷aukacin masoya fatan alheri....
Chapter 93 · 0% Book details