← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 93

Sashe 20

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Numfashi na sauke cike da alhinin labarin da Bappa ke bani nace
"Ikon Allah to shi wannan makiyayin naku yaya iyayen sa sukayi dajin shima 蓷an fashin ne, yanzu ku duk zaman ku da shi bakusan shi ma 蓷an fashi bane?".
yace "Sam bamusan 蓷an fashi bane, to ai shi asalinsa ma ba bafulatani bane, zuwa yayi rugarmu tun yana yaro yace zai rika yi mana kiwo muna biyan sa, shekaru 16 muna tare da shi, muka bashi duk wani yar da ashe macuci ne bamu sani ba, yana ha'intar mu, har sai da Allah ya turo mana Ahmad Tijjani Sabil."
kai na jinjina cike da mamaki ina fa蓷in
"Tab lallai to shi ya akayi yasan 蓷an fashi ne shi da yazo bai jima ba, ku da kukayi shekara da shekaru da shi baku sani ba?."
Bappa yace "Wlh duk kanin mu kowa abun da yayi ta fa蓷a kenan bayan komai ya lafa, sai dai bamu sami amsar tambayar ba, dan ko shi Ahmad 蓷in da muka tambaye shi bamu sami wani kwakkwaran amsa ba, sai muma muka bar shi bamu tsanan ta masa tambayar ba, munji da蓷i da farin cikin da Allah ya nufa shi zai zame mana karshen matsalar mu."
Bappa yana maganar ne cikin nuna tsantsar farin ciki da jin da蓷i...
na ce "Lallai kam to Allah ya tsare na gaba."
ya am sa da amin amin kana yamike yana fa蓷in "Bari na shiga ciki."
yana tafiya naruko hannun su muka haura sama...

Yauma kamar kullum narako su Naseem ina tsaye har sai da naga fitar su,
kana na koma ciki, wanka nayi ina gama kimsawa nayi breakfast, wan da nasa Zulai takawo min shi cikin 蓷aki,
ina gama breakfast 蓷in nahaye gado dan bacci ne a idanuna
ban farka ba, sai wajen karfe shabiyu saura 拼an mintina dabasu fi 20 ba, wayata na janyo na kira Number Yakubu, kasan cewar yau juma'a da wuri ake tashin su, bugu 蓷aya ana biyu ya 蓷aga, nace
"Kayi maza kaje ka 蓷auko su Nasmah." yace "To Hajiya da ma nima yanzu ina kan goge motar kenan yanzu zan tafi."
"Kabar wani goge mota katafi kaje ka 蓷auko su." nayi maganar tare da kashe wayar, mikewa nayi nashige bathroom nayi wanka tare da dauro al'wala, ina fita na sauya kaya. ganin lokacin salla da saura sai na nufi kofa nafita kasa na sauka.
Talatu da Zulai duk suna parlour'n suna ganina sukayi min sannu da fitowa,na amsa ina yi musu yaya aiki, suka ce alhmdllh, an tsaftace gurin ko ina yayi tsaf sai kamshe ke tashi.
ina jin matukar da蓷in zama da su sabo da suna baiwa aikin su kulawa sosai.
a 蓷aya daga cikin kujerun parlour'n na zauna, tare da saka idanuna kan TV ganin shirin da ake.
zamata baifi da minti 10 ba najiyo muryar su Naseem daga kofa ta waje suna kwa蓷a sallama, kallon kofar nayi da murmushi akan fuska ta, suka turo kofar da gudu suka shigo suna fa蓷in
"Mommy mun dawo Mommy mun dawo."
fa蓷a蓷a murmushi na nayi tare da fa蓷in
"To sannun ku da dawowa."
in da nake suka taho da gudu na bu蓷e hannuna suka fa蓷o ciki na rungume su, ina dariya da fa蓷in
"An yi karatu sosai dai ko?."
kai Naseem ya gya蓷a. nace "To madallah." na dubi Nasmah nace "Likita na anyi karatu sosai ko?." itama kai ta gya蓷a tana washe baki, Naseem ko baki ya turo yace "Mommy ni baki ce min tojan ki ba."
cikin muryar dariya nace "Oh soja na."
shima dariyar yayi cike da jin da蓷in sunan dana kira sa da shi.
Nasmah ko mikewa tayi a jikina tarike kugu tare da jujjuya idanun ta tace
"Ai nafi Naseem yin kayatu da yawa yana ta wasa da wani yayo, ni nayi kayatu da yawa dan yika yima mutane ayyuya kuma."
ido na waro yan da take yi da ido ya bani dariya nace
"A.a.a Naseem 蓷in wato wasa kaje ka zauna kake yi ba karatu ba ko?".
nayi maganar tare da rike ha蓳a ina kallon sa, yace
"Hum kaiya ne take yi, nayi kayatu da yawa kuma Daddy yace nayi kayatu da yawa idan nayi da yawa da yawa, yace dai jo ya auke mu a gida."
Nasmah tace "Um ai Daddy yace ni ne dai jo ya auke ni nafika kayatu da yawa, ai nayi mishi kayatu da yawa ma yau kuma."
Naseem yayi kamar zai ture ta yana fa蓷in
"Ai nima nayi ma Daddy kayatu da yawa."
ido na waro da mamakin kin sunan da suke ambata sunan da nayi ta musu barazana kan kuma fa蓷ar sa, nace
"Kai kurafa min baki, wani Daddy'n."
nayi maganar cikin tsawa dan ni a tunani na ma wani ne daban ba wancan mutumin da na kwa蓳e su da shi ba.
Yakubu da yashigo rike da school bag 蓷in su yakaraso ciki Talatu ta amshi jakar tayi cikin bedroom 蓷in su da shi, ya washe baki da fa蓷in
"Ai Hajiya Ahmad Tijjani Sabil suke nufi, ai ina isa na iske su tare da shi abakin get din makarantar su tare da shi, naji yana tambayar su karatu suna ta zuba masa karatun da aka musu, nace kai ashe fa yaran nan za'ayi masu ilimi ne anan wlh kuwa."
yayi maganar yana mai cigaba da washe baki.
fuska na tsuke sosai tare da mai da dubana kan yaran kana na mike tsaye na ruko hannun su na janyo su muka haura sama,
muna shiga 蓷aki na sake su ina fa蓷in "Ni 拼asu yazan yi da yaran nan wato ku bakwa ji, duk abun da zanyi ta fa蓷a muku bazaku jiba shi wannan Ahmad yake ko wane wlh dole na 蓷au mataki a kansa, idan bana 蓷au mataki akan lamarin ba zai rushe min ginin danake ta gina shi,
yana ta kokarin rushewa ya haka ne kam, ina ruwan shi da su meye ha蓷in shi da su da zai rika sanya musu wani ra'ayi a cikin zukatan su."

Duban yaran nayi nama rasa wani irin masifa zan musu, ko da na musu ma abanza gobe zasu kuma,
zubewa nayi bakin gado da tunanin yan da zanyi na 蓳ullo wa lamarin, yazama dole na 蓷auki mataki kan lamarin idan ba hakaba, to kuwa tabbas ginin da nake ta kokarin gina shi domin yayi karko to kuwa zai iya rusa min shi, tabbas zan 蓷auki mataki kansa, "Amma mene ne mafita?. nayi wa kai na tambayar ina gyara zama ta,
"Mafitar kenan kawai ki canza musu makaranta."
zuciya ta ta bani amsa, kai na jinjina da gaskata abun da zuciya ta ta fa蓷a min, hakanne kawai mafita ta yadda zasuyi nesa da shi, idan kuma ba haka ba to kuwa abun da nake ta kokarin cire masu kwa蓷ai tar sa a zukatan su shine zai faru, dan kuwa in har hakan yaci gaba da faruwa zasu tashi da sanin wani mahaifi a ransu wan da bana son su san haka, nice nan uwa kuma uba a rayuwar su, sam bana son su tashi da jin cewa zasu sa mi uba ni zasu cigaba da jina uwa kuma uba a rayuwar su.
bana so su sanyawa ransu abun da baza su samu ba a rayuwar su, to mene ne amfanin sanya wa ransu hakan,
gara kawai su san cewa ba su da uba, su ji a ransu ni ce uban nasu kuma ni ce uwan su.
wannan ka蓷ai shine mafita in sauya musu makaranta in nesan tar da su daga gare shi, in ma koyarwa yake a makarantar imma mene ne baya sake ganin su bare ya cigaba da cusa musu wani ra'ayin, ai dai sun rabu bashi basu, bazai sake ganin suba suma haka bare su sake kiran shi da wani Daddy,
"茒an rainin wayo har da cewa surika ce masa wani Daddy, sai kace wani uban su ko meye gamin sa da su oho."
naja dogon tsaki tare da yin kwafa kana na mike, nashiga tu蓳e musu uniform 蓷in su, ina fa蓷in
"Ku da shi 蓷in duk zanyi maganin ku."
bathroom na jasu da kai na nayi musu wanka yau, muka fito na saka musu wasu daga cikin kayan su da yake bedroom 蓷ina, sai da na nagabatar da sallar azahar kana na janyo su muka sauka kasa.
dinning area muka zarce bayan munci abinci najasu muka tafi part 蓷in su Inna wuro, nan muka tarar da Faty ita ma dawowar ta daga school kenan, nan muka yada zango mukata hira...
da yammacin ranar zaune nake a parlour'n sama na 蓷ago wayata na lalu蓳o number shugaban makarantar su Naseem.....!

Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:54 - Ummi Tandama馃槆: Yan da idanun sa yasarkafu cikin nawa haka babu zato ko sammani shi yasani shiga yanayin,
sai kuma na gyara tsayuwa ta da kyau, wani kallo yake bina da shi daga sama har kasa kana yace
"Na 蓷auka kafin kiran hukuma ihu zaki yi ta yi kitara jama'a kice ga 蓳arawo yazo satar yara, ke ba'a yi miki ihu ba har ke zaki wa wani ihu? karfe nawa ne yanzu wai wannan lokacin ne lokacin zuwa 蓷aukar yara a makaranta,abar yara can kowa ya watse sai su ka蓷ai a cikin makaranta, sabo da baki san abun da kike yi ba an turaki 蓷aukar su kin tsaya kin 蓳ata lokaci a hanya kina damuwar ki wata kila ma kinbi gidan kawayen ki kin gama sharholiyar ki,
kafin nan kika zo wai ke a hakan kinzo 蓷aukar su a makaranta, karfe nawa yanzu?. karfe nawa ne yanzu?!".
yakuma nanata tambayar, yana maganar ne ida nunsa a kaina da kuma alamun jaddada tambayon da yake jefa min,
gashi dai maganar cikin fa蓷a yake yin sa amma lam蓳ansa a hankali suke motsawa.
dogone yana da faffa蓷ar kirji da zubin kakkarfan maza, fuskarsa na 蓷auke da 蓷an siririn saje wan da ya zagaye fuskar nasa har zuwa 蓷an gemun sa da bai wuce rabin kamu ba, irin gemun da gayu suke bare.
baza a kirasa da fari soll ba sanna kuma ba baki bane, hasken sa dai-dai.
kwantaccen gashin kansa baki sitif yasha gyara mai tsamtsi da tsul蓳i sai wani yal-yal yake, sabo da iskar dake ka蓷awa.
Chapter 20 · 0% Book details