← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 93

Sashe 82

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A parlour mukayi salla dukan mu har da su Bappa, dan Bappa yaki matsawa ko nan da can daga in da nake.
ganin gari yayi haske kuma har zuwa lokacin security basu zo da Ahmad kamar yadda Bappa ya fa蓷a ba.
gashi duk kiran wayar sa da nake baya 蓷agawa,
na saka musu kuka nace ni sam zan tafi zanje da kaina gidan.
wayar Bappa ce tayi kara, ya 蓷aga tare da yin sallama.
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un."
abun da Bappa ya furta kenan, zumbur na mike tsaye ina kallon Bappa, Bappa ya kawar da kansa tare da sauke wayar a kunnen sa, yayin da la蓳蓳an sa ke motsawa alamun salati yake.
蓳ari jikina ya soma murya na rawa nace
"Bappa mene ne wa yayi maka waya?."
kai ya girgiza yayin da idanunsa suka kawo kwalla, sai ya kawar da kansa daga kallo na yace
"Babu komai je ji sa babban mayafi ki zo sai muje gidan Ahmad 蓷in kawai tun da har yanzu basu zo ba."
ya dubi Inna Wuro yace
"Je ki rakata tasa mayafin."
sai ya sauya harshen sa izuwa fulatanci yayi mata magana cukin harshen fulatanci,
Inna Wuro ta saki salati tana dafe kirji, sai kuma tayi saurin sauke hannunta a kirjin sabo da maganar da Bappa ya kuma mata da fulatan ci, ta ruko hannuna yayin da hannunta ke 蓳ari ta janyo ni muka haura sama.
muna shiga muka tadda su Naseem duk sun farka, tace na cire hijabi da kayan baccin da ke jiki na na sa wani kayan.
jiki a sanyaye yayin da hawaye ke bin fuskata nayi kamar yanda tace, nasaka babban hijabi, kana ta ruko hannun su Nasmah ni kuma na 蓷au Ahmad karami muka sauko kasa.
tun kan mu karaso parlour'n kasa su Mama suna ganin mu kowa ya shiga sun kuyar da kai suna share hawayen su cikin dabara sai kowa ya mike da sauri akayi waje gaba 蓷aya.
da sauri na 蓷aga murya nace
"Kukan me kuke yi?."
da sauri Bappa yace
"Kuka kuma sam ba wan da yayi kuka a cikin mu."
cikin rawar murya da kuka ke son kwace min nace
"Na ganku da idona na, ganku kuna kuka ku fa蓷a min kukan me kuke yi?."
Mama tayi murmushi wan da yafi kuka ciwo tace
"A ina kuma HAMDAH mu sam bamuyi kuka ba muje direba yana jiran mu."
ta ruko hannuna muka karasa fita waje...
koda muka iso parking lot Bappa yace su Zulai su zauna da su Naseem a gida.
a tsakiya suka sani Mama da Inna Wuro, Ahmad karami na rike a hannu na, Bappa kuma ya zauna a gefen mai zaman banza, direba yaja muka fita.
ina zaune shiru hawaye na zuba a idona na, ido na kurawa titi ganin mun 蓷au wata hanyar daban ba hanyar gidan Ahmad ba.
a bakin wani katon asibiti direba yayi hon, aka bu蓷e masa ya sakai ciki ya faka motar muka fito, asibitin zagaye yake da sojoji da 拼an sanda, can na hango Abba Bashir yana sunkuye da alamar kuka yake, wasu mutane na tsaye a kansa. Inna Wuro ta kar蓳i Ahmad karami dake hannuna, Mama kuma ta ruko hannuna gam ta janyo ni muka nufi cikin asibitin.
da kyar nake iya 蓷aga kafafu na da sukayi min mugun nauyi,
maganar Mama na jiyo tana fa蓷in
"Ba a ja da ikon Allah duk abun da kaga ya sami bawa da sanin ubangiji, Allah kuma baya barin wani dan wani yakan kuma jarabci mutum ta ko wace hanya domin ya gwada imanin sa,
yana da kyau mu kasan ce masu kar蓳ar kaddara mai kyau ko mara kyau aduk san da tazo mana,
Allah yafi mu son bayin sa duk son da muke musu, hakuri kuma shine magani nasan ki da hakuri da iya kar蓳ar kaddara ina fata yau ma ki kasan ce a haka, kice Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un kici gaba da nanata shi cikin ranki."
"Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un鲁."
nafa蓷a da karfi har sau uku dai-dai lokacin da muke sakai cikin parlour'n asibitin, Mama ta da蓷a rike hannuna gam jin yan da ilahirin jikina ya蓷au ki 蓳ari tace
"A hankali zaki fa蓷a ko a cikin ranki ki nusu HAMDAH."
muna shiga jami'an tsaro suka dakatar da mu suka ce mu tsaya anan, wani soja ne ya fito daga cikin wani room yakaraso in da muke yace "Zata iya shiga yanzu."
Bappa ya dube ni cikin rauni yace
"Kullu nafsin za'ikatulmaut duk mai rai mamuci ni, muma bamu da tabbacin zamu iya kaiwa nan da dakika 蓷aya, Allah yayi wa Ahmad rasuwa ki daure kiyi masa addu'a."
wani irin dimm haka naji kunnuwa na sunyi min mugun nauyi jiri ha蓷e da bakin duhuwa ya gilma min,
kallon bakin Bappa nake domin tabbatar da abun da yake fa蓷a dan ni dai a yanayin da nake jin kaina ciki da yan da maganar tazo min a sama sai ji da gani nake kamar ba gaskiya bane, bakina kuma yayi min mugun nauyi na kasa iya furta komai.
sojan yace
"Madam bismilla sai hakuri fa."
yayi maganar yana nuna min hanya Inna Wuro ta mika min Ahmad karami, kana sojan yayi gaba na bisa a baya ina jan kafata da kyar.
muna isa jikin kofar room 蓷in ya mur蓷a handle 蓷in ya shiga, kana ya蓷an ja gefe ya bani hanya na sako kai na ciki.
kana ya mai da kofar ya rufe, sojoji ne tsaitsaye cikin room 蓷in ha蓷e da likitoci,
ido na kurawa kan gadon da nake hango mutum kwance an lullu蓳e shi daga sama har kasa, jikin a bun da aka lullu蓳e sa da shi da 蓷igo 蓷igon jini tagurin kirjin sa da gefe da gefen cikin sa.
wani dake tsaye ta gurin kansa ga dukkan alama babbane dan da zaran yayi magana sai sauran jami'an tsaron su sara masa.
ya 蓷aga hannu tare da yi min alama dana karaso, a hankali naja kafafu na zuwa bakin gadon, ya dube ni tare da fa蓷in
"Allah ya baki hakuri mun kira ki ne abisa cika masa burin sa na karshe, kiyi hakuri bamusan rai zaiyi halinsa ba tun a daren jiya yanemi da a kira ki sai dai ganin halin da yake ciki yasa muka kasa iya ai watar da hakan burin mu kawai likitoci su samu nasarar ku蓳utar da shi daga halin da yake,ga wannan a hannunsa muka samu bayan cikawar sa, ko da muka duba sai muka ga a kanki yake maganar shine muka neme ki kafin mu 蓷aga shi a nan mu damka miki sakon sa a hannun ki."
ya mika min takarda wan da gefe da gefen takar dan duk da 蓷igon jini,
hannu na na 蓳ari na kar蓳i takardan na dunkule shi cikin hannuna.
mutumin ya dubi nakusa da shi yace
"Ku bu蓷e mata shi ta gansa." ya yaye abun da aka rufe shi da shi daga kansa zuwa wuyan sa.
da gaske Ahmad ne a kwance wan da tun 蓷azu ban gaskata abun da suke fa蓷a min ba sai gani nake kamar ba gaskiya bane.
wani irin tsalle zuciya ta yayi tamkar zai faso kirji na yafito,yayin da ilahirin jiki na ya 蓷auki 蓳ari.
a hankali nashiga jan kafata ina da蓷a matsowa bakin gadon yayin da idanuna ke kan fuskarsa, yana kwance idanunsa a rufe yayin da fuskarsa ke bayyane da kayataccen murmushin sa, tam kar akirasa ya amsa.
kai na shiga girgizawa nashiga kokarin motsa la蓳蓳a na, na mika hannu izuwa jikin sa, nashiga girgiza shi tare da sakin kuka mai ta蓳a zuciya cikin muryar kuka sosai tamkar numfashi na zai fita nashiga fa蓷in
"My bana son irin wannan wasan!, My kafarka dan Allah kadai da min irin wannan wasan,ka tashi mana nice fa gimbiyar ka kyakkyawar ka, ka tashi ka gani gani ga Ahmad 蓷an ka 蓷an da ka fara samu a duniya, shin ka mance alkawarin da ka min da bakin ka kace min bazaka ta蓳a bari nakara yin kuka ba, kar kayi min haka kar ka tafi ka barmu dan Allah My dan Allah ka tashi so kake Ahmad ya zamo maraya, ka bu蓷e idanun ka ka fa蓷a min kalmar da kake fa蓷a min kullum kana sona nima ina son ka My ina sonka ina sonka My, My ka tashiiiiiiiii kar ka mutu dan Allahhhhhhhhh!!!."
kuka yaci karfi na sai kawai na kife kansa tare da 蓷aura Ahmad karami a kansa na saka fuskata kan nashi nashiga goga fuskata cikin nashi ina wani irin kukan danake jin ina ma ace yanzu nima na mutu na bishi, Ahmad karami ya saki kuka yana cakumar sa...
mutumin da ya sa aka bu蓷e min shi ya girgiza kai tare da share kwalla, kana yace
"I'm so sorry Madam hakika muma munji 蓷acin rasa gwarzon jami'in sirri kamar Ahmad, sai dai abun farin ciki duk da bulet har uku da suka same sa a gurare daban-daban wan da ko da ace harbi 蓷aya ne bazai iya ta蓳uka komai ba, amma da bulet 蓷in a jikin sa ya kashe mutane biyar yayi wa biyu mummunar raunin da bazasu iya morar raruwar su ba, hakika wannan abun alfahari ne, Allah ya baki hakuri."
sukace na tashi a 蓷aga shi fir naki sai ma da蓷a kankame shi da nayi.
da kyar babban sun ya iya janye ni a jikin sa,ina mike wa a jikin sa sai ji nayi tamkar an fisgo ni sai kawai na yanki jiki na zube a gurin nan take hankali na yabar jiki na ban kuma sanin abun da ake ciki ba....
Chapter 82 · 0% Book details