← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 93

Sashe 14

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yau asabar hakan yayi dai-dai da kwanaki ukun da zamuyi tafiyar, da sassafe muka 蓷auki hanyar suwa Kano, motoci biyu muka tafi dasu motar mu ni da Naseem da Nasmah dakuma Bappa,sai 蓷aya daga cikin jagororin ke zaune a gefen direba, 蓷aya motar kuma mutane hu蓷u ne a cikin ta suna gaba muna biye da su.
mun isa cikin garin Kano da misalin 茩arfe 12:30pm sai da muka tsaya mukayi sallah kafin muka nufi inda zamu,
gidajen mai muka fara ziyarta kafin asibitoti dakuma kamfanoni.
bamufi awa biyu a cikin Kano ba muka 蓷au hanyar Kaduna a kaduna muka kwana, washegari muka nausa Katsina.

Sati biyu muka 蓷auka muna yawon zuwa garuruwa ganin in da aka zuba ayyuka, masha Allah duk garin da mukaje daga gwamnatin su muke samun tarba da kar蓳a mai muhimmanci, daga karshe muka biyo garin Bauchi,
lokacin da motar mu tashiga cikin Bauchi state, tashin hankalin da nashiga bazai misaltuba, wani irin tashin tsikar jiki da sanyi mai matukar shiga jiki su suka ziyarce ni, wani irin 蓳ari da kakkarwa nasomayi lokaci guda har hakorana suna garuwa da juna, sai kuma wani masifaffen zufa yashiga keto min, hankalin Bappa yayi musifar tashi ganin halin dana shiga lokaci guda,
cikin tsananin tashin hankali jin bakon yanayin daya ziyarce ni lokaci guda tamkar 茩wa茩walwa ta zata fashe jin wani irin abu mai matukar nauyi da kara ya dankare min a kai, kunnuwa na tamkar ana busa wani irin busa mai matukar kara da firgitar wa, da karfi nakai hannuna na toshe kunnuwana cikin matukar jin azabar dake kokarin tarwasa min rayuwa nashiga fa蓷in
"Bappa mu tafi Bappa kace musu kada mu tsaya Bappa mutafi wayyo Allah na".
kaina nashiga juyawa da karfi jin yan da zabar da nakeji na karuwa nan take nanimi tunani na na rasa.
cikin 蓷aga murya ganin numfashi nakokarin barin jikina Bappa yace
"Direba yi hanzari mufita a cikin garin nan yi maza da sauri!".
gudu direba ya kara bai tsaya ba sai da muka fita a garin, gabaki 蓷aya, hankalin kowa yayi masifar tashi ganin halin da nake ciki,
Bappa ko karatun Kur'ani yasoma yanayi yana tofa min, hankali na bai dawo jikina ba har sai da mukabar eriya'n Bauchi gaba 蓷aya.
A hankali narikajin abun da nake jin na sassauta har ya washe.
numfashi Bappa ya sauke tare da saida karatun da yake, kai ya girgiza tare da fa蓷in
"Kai mutum abin tsoro ne Allah kashiga sakanin nagari da mugu akwai hisabi ranan gobe kiyama".
yadubeni da kula yace
"Sannu ko HAMDAH".
kai na girgiza yace "Me kike ji yanzu?". nuna masa kaina nayi da hannu dan shi ke yimin ciwo sosai.
"Zai bari insha Allahu".
yayi maganar tare da bu蓷e tafukan hannunsa yasoma karanto Suratul (Khafi) aya goma na farkon surar ha蓷e da ayatul Qursi'yu ya tofa kana yashafamin a kan. cikin yar da da buwayar Allah naji ciwon kan na sauka.

Ko da muka shiga jahar plateau state, farkon shiga garin Jos NARKUTA. wasu zafafan kwalla ne suka gangaro kan fuskata tuno da Mama mai awara, da sauri nayi yinkurin yin magana a tsaya amma abun mamaki sai naji harshe na yayi min mugun nauyi gaba 蓷aya jikina ya sake babu alamar karfi tattare da ni, abun da na fahimta tun lokacin da nayiwa Bappa maga shigar mu Bauchi zan kuma wata maganar naji na kasa, har kuma yanzu ina jin yanayin...
da daddare muka shiga Abuja, da kyar da taimakon Bappa na iya sauka cikin mota muka shiga ciki.
Inna wuro ta firgita da ganin yanayi na, ko da Bappa yayi mata bayanin abun da ya faru, hankalin ta yayi masifar tashi, yace ta taimaka min naje na kwanta, shikuma yafita can ya dawo da 蓷an karamin 茩warya da magani a ciki yabawa Inna wuro yace
"Kibata tasha babu komai insha Allah zata ware garin ne kwatakwata basa so tashiga sai dai tayi nesa da shi sun mance cewa Allah baya bacci".
Inna wuro tace "Ikon Allah wannan irin shiga sakani sai sakayyar Ubangiji".
ko da Inna wuro ta bani maganin inasha bada jimawaba bacci ya蓷auke ni, ranar a kaina ta kwana, Fatu kuma tana tare da su Naseem a 蓷aya 蓷akin dake kusa da nawa.
washegari kuwa cikin yarda da buwayar Allah namike garau...
muna tare a parlour ni Inna wuro Fatu dan har lokacin basu koma side 蓷in suba, labarin garuruwan da mukajejje narika basu ina washe baki da fa蓷in
"Allah Inna wuro bakuga abubuwan yan da sukayi kyau ba kai har da garin da ban ta蓳a zuwa ba".
nayi maganar ina washe baki, dariya suka rika min, nan
Bappa yashigo ganin jikina shima yazauna mukayi ta hira....

bayan kwana biyu

Mutane biyu daga cikin jagororin nan suka zo su da wasu mata guda biyar sukace na zama a cikin su wan da zasu rika yi min ai ki,
mata ne irin wan da suke karkashin paundation, irin wa蓷an da mazajensu suka sake su dakuma wan da mazajensu suka rasu, akan 蓷auke su ai ki irin gidajen masu ku蓷i 蓷in nan, a cikin su na za蓳i guda uku dasukafi kwanciya min a rai, kana nace zan gwada ai ki da su.
蓷aya na 蓷auke ta a matsayin mai kula da su Nasmah dakuma kula da tsaftar side 蓷in,
na biyun kuma mai girka abibci, sai kuma 蓷ayar na turawasu Inna wuro ita zata rika kula da tsaftar side 蓷in su dakuma girkin su.
nan suka kuma gabatar min da masu maza wan da nazo nasame su a cikin gidan, direba sai mai baiwa fulawa ruwa shi zai rika wanke mota, sai mai gadi dakuma mai kula da tsaftar farfajiyar gidan gaba 蓷aya.
mun zauna da su na 蓷an wani lokaci na fahimci mutane ne masu kirki da rukon amana.

Haka rayuwa tacigaba da tafi, tuni akayi bikin bu蓷e masana'antu da masallatan nan manyan shuwagabannin Nigeria sun halacci torurrukan sun kuma bada gudummawar su kwarai da gaske wajen ganin an 蓷ibi ma'aikata masu inganci.

Bayan wani lokaci

Tuni aka damkamin ragamar duk wasu kaddarori na ni nake bada umurnin ayi da kuma kar ayi, har kuma yanzu muna tare da jagororin nan su suke sanya ido kan ganin komai yatafi dai-dai.
tuni nasa aka baiwa Fatu uniform a 蓷aya daga cikin makarantu na, dan dama acan rugar ma tana karatun ta tacigaba a nan.

Zaune nake a parlour ina dudduba jerin sunayen mata da matasan da nasa a 蓷iba, a karkashin paudasion 蓷ina domin basu tallafin wasu ku蓷a蓷en da zai jamusu jari domin dogaro da kai na tura da ku蓷a蓷en tallafin izuwa asusun *HAM'NAS* paudasion.
a hankali na mike tsaye tare da yin mika ha蓷e da salati, wayoyina na tattara ha蓷e da sabuwar system 蓷ina, na haura sama,
kan bedside na ajiye su kana na haye gado dan bacci nake ji, ina so nayi baccin kafin su Naseem su shigo dan suna can side 蓷in su Bappa.
har na kwanta na tuna da akwai maganar da nake so muyi da Bappa kan wani Company na murza karfe da ake gina shi a Lagos,
mikewa nayi na fita dan ina so muje ziyarar gani da ido acikin satin nan.
da gudu Nasmah ta shigo tana fa蓷in
"Mommy kin ga Naseem ko jai camin jiji".
Naseem shima dagudun yashigo yana binta da abun yana dariya, Fatu na biye da su tana dariya da fa蓷in "Naseem kabari kar ka sa mata".
da sauri nakarasa sauka kan step na rungumo Nasmah dake falfala gudu kamar zata kife kasa nace "K.......!鈽?
Chapter 14 · 0% Book details