← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 93

Sashe 13

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa sai yaba kyau da tsaruwar gidan yake, 蓷aya daga cikin mutanen yadube ni kana yayi gyaran murya sannan ya ce
"Madam komai yayi ko? komai ya miki wannan gidan yayi miki? kokuma mu isa wani gidan?."
kallon sa nayi cikin rashin faminta sai kuma na maida dubana ga Bappa danaji yana fa蓷in
"Duk da dai bataga sauran ba amma ga yanda take ta washe bakin nan ai ba a magana."
da sauri nace "Bappa gidan..". bai bari na karasa ba yace "Gidan ki wannan gidan duk girman ta nakine akwai kuma ire-iren su suna nan".
ido na waro kamar a mafarki nakejin zancen, "Wannan ya miki?". mutumin yakuma jefo min tambayar, kai nashiga gya蓷awa da sauri sai kuma naruko hannun Bappa ina fa蓷in
"Eh wlh yayi-yayi Allah Bappa gidan yamin kyau sosaiiiii".

Dariya Bappa yayi yace "To sake min hannu kada ki 蓳ala".
ai ko sauran mutanen ma suka rika dariyar ganin yan da nake washe baki ina jijjiga hannun Bappa, Naseem da Nasmah dariya suka rikayi suna tsalle jikin Bappa kamar wan da sun san abun da ake.

Mutumin yacigaba da fa蓷in
"To masha Allah wannan side 蓷in shine naki a yanda aka tsara ginin gidan, sauran kuma ke kikasan yan da zakiyi da su, yanzu mu zamu koma mubarki ki huta zamu dawo zuwa gobe, domin sauran baya nai."

Sukayi mana sallama suka fita, suna fita, na dubi Bappa ina waro ido nace
"Bappa wai da gaske wannan gidana?". Bappa yayi murmushi tare da fa蓷in "Da蓷ina da ke akwai shirme." hannu nashiga tafawa ina fa蓷in "Kai wlh gidan nan yayi min mugun kyau." ya ce "To sai ki goyashi kuta yawo tun da dai naki ne." ido na waro tare da sa dariya nace
"Bappa gidan zan goya?." kanshi ya jinjina yana murmushi.
rungume Naseem da Nasmah nayi cikin tsananin farin ciki, sai kuma na sake su.
da sauri nace "Bappa ina su Inna wuro da Fatu?."
yace "Suna can ruga". nace "Bappa shine bakazo da su ba kace su dawo nan suzo mu zauna da su a nan, kaji Bappa."
nafa蓷a ina jijjiga hannun sa, "Kaji Bappa kace su zo". nakuma fa蓷a ganin yayi shiru bai ce komai ba,
yace "A'a HAMDAH su zauna acan zan koma ai nima".
ido nakuma warowa da karfi nace "Bappa ni ka蓷ai za'a barni a wannan gari gudan, da ni ka蓷ai zan zauna a gidannan ai dani daku zamu zauna."
nayi maganar ina nuna cikin parlour'n "Tap Allah bazan iya zama ba dan Allah Bappa kace su dawo nan, wannan gidan ai tsoro zai rika bani ni ka蓷ai a cikin sa, kaji Bappa?."
nafa蓷a ina bubbuga kafafuna a kasa. "To babu damuwa zasu zo amma ba yanzu ba."
na ce "Bappa sai yaushe." ya ce "Bari dai mana a gama Hajiya HAMDAH."
dariya yake bani in naji ance Hajiya HAMDAH, ai ko na washe baki,
yace "To meyasa bakisa hakorin hajji ba acan?."
"Kai Bappa,hhhh to zan sa in na kuma komawa."
"Allah ya kai mu ai kamar yanzu ne shekara zata kuma zagowa Allah ya nuna mana cikin masu rai da lafiya."
yayi maganar yana mikewa tare da cigaba da fa蓷in
"To ni bazanje masallaci gashi ana ta kan kiran sallah, mutumin zo muje muyi sallah".
da sauri Naseem ya mike ya roko hannunsa suka fita.

Da sauri na mike inata da蓷a waigen cikin parlour'n inshiga wan 蓷akin in fita inshiga wancan haka narikayi, daga nan kuma naja hannun Nasmah muka haura sama ina fa蓷in
"Bari naje na za蓳i bedroom 蓷in da yafi min."
koda muka haura 蓷akunan duka na shiga kana naza蓳i 蓷aki 蓷aya, nan cikin bedroom 蓷in nabu蓷e bathroom 蓷in sa na shiga mai girma da tsaruwa kamar 蓷akin kwana.
kayan jikina na tu蓳e duk da ban jima da yin wanka ba nacika ruwa cikin basin nashige ciki, lumshe idanuna nayi ina jin da蓷in ruwan na ratsani, najima sosai a ciki kana na wanke jikina da sabulu mai sanyin kamshi da nagani cikin bathroom 蓷in, sannan nafito.
Na sami Nasmah gaban mirror ta 蓷auki janbaki sai murkawa take a bakin ta.
dariya nayi ina fa蓷in
"Oh wannan yarin ya ke kam akwai ki da son janbaki".
itama baki ta washe tana cigaba da kwa蓳ula janbakin a bakin ta.
da sauri na sauka kasa akwatin kayan mu na janyo nadawo 蓷akin, a sannu na isa gaban wardrobe dan na shirya kayan ciki, ina bu蓷e wa ido na ware cikin wardrobe 蓷in ganin kaya ashake a ciki, kama daga kan leshi atamfa material shadda dogayen riguna iri-iri, sai dai ba a 蓷inke suke ba,a hankali na zaro 蓷aya daga cikin dogayen riguna wan da suke jere gefe guda masu kyan gaske, na dawo gefen Nasmah na zauna, kana na sauya kayana da dogon rigar nan...

Tsabar farincikin da nake jin kaina ciki yau bazai misaltuba, muna zaune har su Bappa suka dawo muka sauko parlour'n kasa muna 蓷an ta蓳a hira dakuma kallon tv.
duban Bappa nayi sai kuma kamar an zabure ni na mike ina fa蓷in
"Bappa ina zuwa."
sama na haura in da na aje karamar jakata ta hannu na 蓷auko na bu蓷e jakar naciro wayoyin da jiya aka bani wan da tun da na kunna su nakuma kashewa najefa cikin jakar, dakuma ATM 蓷in da jiya aka bani su a banki, nadawo in da Bappa suke da sauri nace
"Kagani Bappa jiya mutanen nan suka 蓷auke ni sukayi ta kaini bankuna sukayi ta bu蓷e min account, muna dawowa kuma suka bani wa蓷an nan wayoyin ina kunna su kawai Bappa kaga ku蓷in da sukayi ta shigowa kawai ku蓷i sunata shigowa cikin accounts 蓷in".
nayi maganar ina wawwaro idanuna alamun tsantsar mamaki.

Murmushi Bappa yayi irin nasu na manya kana yace "HAMDAH kenan ai ku蓷in kine yake shiga cikin asusun bankin ki, duk wani abun da kikaga yake faruwa duka, duk wa蓷annan mutane dasuke ta zirga-zirga da 蓷awainiya da ke, duk umurnine daga sama, duk kanin su an 蓷aurasu ne jagora akan lamarin, shiyasa kikaga duk wa蓷an nan abubuwa suke faruwa duk abun da kikaga sunyi umurnine, sunce min ma gobe idan Allah yakai mu za'a fara kai ki guraren da akayi ayyuka wato guraren kaddarorin ki, kije ki gaggansu gobe za'a fara tafiya shiyasa sukace kihuta yanzu."
kai na jinjina alamun gamsuwa, ikon Allah abun kamar a mafarki yake zuwar min.
knocking 蓷in da ake ne yasani mike wa nanufi kofar da nafi zaton tanan ake knocking 蓷in, na isa jikin kofar na bu蓷e,
wani nagani tsaye rike da basket har guda biyu a hannunsa, 蓷an risinar da kai yayi alamun girmamawa kana ya 蓷ago yayi min barka da warhaka, na amsa kana yace min order ne daga hotel 蓷in su akace yakawo nan gidan, kai kawai na girgiza kana nabashi hanya yawuce ciki.
dinnig table ya isa ya aje kayan abincin kana yayi mana sallama yafita.
muna nan zaune a parlour sai wajen la'asar mukaje mukaci abincin, daga nan Bappa yakuma fita domin zuwa Masallaci shida Naseem.

Washegari da safe kamar yan da mutanennan suka ce zasu zo suka iso,
suna zaune a parlour nikuma ina ciki domin kimsa su Naseem, ina gama kimsasu muka sauko nan muka 蓷unguma.
yau munsha yawo kaman kaman domin kuwa tundaga unguwar muka fara, wani gida mukaje sakanin sa da蓷an rata da gidan da muke ciki, sannan muka wuce wasu unguwanni biyu duk kanin su da gidaje 蓷ai-蓷ai, wan da an gama musu komai suna kulle,suka nunnuna min dakuma tabbacin nawa ne, nasha mamaki kwarai daganin manyan gidajen wai kuma a matsayin nawa.
daga nan wani tsalelen gidan mai muka je tun daga can nahango ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) wan da aka rubuta da manyan harufa a saman gidan man, tunga nesa zaka iya hango shi 蓳aro-蓳aro.
idanuna na lumshe tare dayiwa Ubangiji buwayi gagara misali tasbigi a kasan raina kana na bu蓷e,

Mun zaga gidan man na yaba da tsarin sa kwarai yana rufe ne ba'a fara aiki da shi ba,
daganan kuma wasu gidajen man mukaje har guda uku duk masu 蓷auke da ( *HAM'NAS Co Petroleum Nigeria LIMITED* ) daga nan muka kuma zuwa asibitoci suma masu 蓷auke da sunan ( *HAM'NAS International HOSPITAL* )
suma asibitotin guda uku a gurare daban da ban manyan gaske, sai dai duk a kulle suke anzuba kayan aiki komai da komai acikin su sai dai ba'a fara ai ki da suba.
daganan kuma makarantu da kamfanoni muka nufa duk kanin su da tambarin *HAM'NAS* International School Of Science's And Technology, *HAM'NAS Store Complex's su ma duk ba'a fara ai ki da suba. sai kuna masallatai manya guda uku anzuba komai a ciki suma ba'a fara amfani da su ba.

Zuwa yanzu kam nidai komai ganin sa nake kamar almara nafara yarda kan cewa komai da gaske ne, sai yamma muka dawo gida, mun dawo a gajiye suke fa蓷a min cewa muhuta nan da kwana uku sai mu fara tafiya guraren kaddarorin dasuke garurruwa nesa da nan, nace to Allah ya kaimu..

Damin Bappa narikayi nace nidai yasa su Inna wuro da Fatu suzo kafin mutafi nan da kwanan ukun,
yace a'a abarsu tukun ba yanzu ba,
haka dai dole yasa direba yaje ya taho da su dan na tubure a la dole sai an kawo su, ko da direba zaije 蓷auko su nace yace musu kada suzo da komai, dan cikin side 蓷in dana matsawa Bappa sai ya zabi 蓷aya daga cikin side 蓷in gidan wan da zasu zauna ciki, akwai kaya komai na bukata sai suzo suyi amfani dashi abun da babu sai a karo musu kamar kayan sawa shi da babu a sauran side 蓷in.
hakan kuwa a kayi ranar da su Inna wuro sukazo murna kamar nayi yaya, suma agefen su ba'a magana, na rungume Fatu inata murna, tarika 蓷aukar su Naseem cikin tsananin farincikin kuma ganin su.
a ranar ma Uncle Mahmoud yazo har da matarsa da yaran su, dan su anan Abuja suke gun ai kin sa.
nan muka wuni da su wunin ranar yayi min da蓷i matuka, sai narika jin su tamkar wani 蓳ari ga ahalina,
ganin su ya蓷an rage min kewa da begen family na.
Chapter 13 · 0% Book details