← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 93

Sashe 55

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari kamar yanda yafa蓷a motar mu ta hau hanyar Jos, bayan munyi wa su Bappa sallama, kwarai Bappa yaji da蓷in jin cewa gurin Mama mai awara zamu je, yayi ta zuba mana addu'a da fatan isa lafiya, yaku ce mu gaishe ta sosai da sosai.
ni da shi muna gaba Naseem da Nasmah suna baya, dan yaki direba ya biyo mu yace tafiyar family ne dan haka direba yayi zaman sa.
da misalin karfe 2 na rana muka iso cikin garin Jos,
daga nan nafara yi masa kwatance har muka iso Narkuta,
wani numfashi na sauke a bayyane lokacin dana ganni dai-dai kan kwalbatin shigan layin gidan Mama mai awara,
nan take tunanin rayuwa ta ta baya tashiga zuwar min, bazan mance ranar dana zo garinnan ba akan wannan kwalbet 蓷in na zauna har dare, har wasu mutane suka zo amota suna yimin tayin shiga na biyo su,
idanuna na rumtse da karfi ina kokarin mai da hawayen da ya ciko min ido.
muryar sa najiyo a hankali
"Kibar tunanin nan sam bashi da amfani tuna irin haka sai dai ya sanya maka damuwa da 蓳acin rai, ina zamu bi?."
a hankali na bu蓷e idanuna da tuni hawaye ya gangaro min, nayi masa nuni da hannu nace
"Mu mike nan."
a hankali ya sa kai cikin layin, sai 蓷an kalle-kalle nake, garin ya canza anyi sabbin gine-gine,
nayi ta masa nuni da hannu har muka iso kofar gidan Malam Musa, dakyar shima na iya gane wa dan an yiwa gidan fenti ga kuma sabbin gine-ginen daya zagaye su.
kallon sa nayi nace "Ina zuwa bari na shiga na tambayi Zainabu gidan da Mama ta koma sai ta nuna mana muje."
kai ya gya蓷a, na bu蓷e marfin motar na fita.
da sallama nashiga gidan, ga mamaki na wasu mata na gani zaune a cikin gidan suka amsan sallama na karaso ciki, ina ta 蓷an raba ido ko zan ga Zainabu,
na gaida matan suka amsa suna fa蓷in Sannu da zuwa, nace "Yauwa dan Allah Zainabu tana ciki ne?."
蓷aya daga cikin matan tace
"Wata Zainabu?."
nace "Matar Malam Musa." sukace "Au wai ai sun jima da tashi a gidanan na sun koma wata unguwar daban."
da sauri nace "Innalillahi dan Allah wata unguwar suka koma? ko za'a nuna mana ko ayi mana kwatance."
sukace wlh sam basu sani ba, suma haya suke ana gobe zasu tare a gidan su kuma suka bar gidan, sam basu san wata unguwa suka koma ba.
cikin sanyin jiki na juya nayi musu sallama na fita,
jiki ba kwari na shige cikin motar na zauna
duba na yayi yace
"Ya dai tayi miki kwatancen gidan ne?."
kai na girgiza a hankali nace
"Bata nan wasu ne a cikin gidan,kuma wai basu san in da suka koma ba."
wasu hawaye ne masu 蓷umi suka zubo min sai nayi saurin sunkuyar da kaina.
a hankali ya dafa kafa蓷a ta yace
"Kiyi hakuri idan da rai da rabo wata rana zaku ha蓷u."
kai kawai na girgiza, a hankali ya share min hawayen yace
"Ya isa haka na roke ki kada ki sake zubda su ina jin zafin su har cikin dai na, Please na roke ki."
ya ha蓷e hannayen sa biyu.
kai na girgiza masa a hankali na karasa share hawayen.
a sannu yaja motar muka bar gurin.
muna fita bakin layin unguwar,na juya da kallo na ta gabar wato hanyar Bauchi, ya lura da hakan sai ya saka hannu ya juyo da fuska ta a hankali cikin tausasshen lafazi da son sama min karfin guiwa yace
"Zamuje shima idan Abba ya da蓷a huce wa."
yafa蓷i hakan ne kawai dan sama min nutsuwa da kwanciyar hankali,
a can kasan zuciyarsa sa kuwa bayan Bappa ne sukayi masa ca,
"Lallai mutum abin tsoro ne, ka ha蓷a tsihiri da mutuwar ka sabo da kasan duk mai halin irin naka Allah yana musu talala ta hanyar barin su a duniya su shafe shekaru masu yawa,
tabbas akwai hisabi ranar gobe kiyama."
duban sa nayi jin yaja kwafa afili nace
"Ya dai?." kai ya girgiza min da sauri yace "Ba komai ina tunanin tafiyar dake gaban mu ne mukwana a cikin gari kawai, mu huta gobe da safe sai mu juya."
nace "A'a kawai mu tafi."
ya juya ya dubi su Naseem da tuni suka bingire da bacci yace "Sun gaji kiga baccin su nawa, kema kuma nasan kin gaji."
nace "Ni dai mutafi gida kawai."
yace "To shi kenan."
ya haura hanya muka 蓷au hanyar Abuja...
kasan cewar da abincin mu muke tafe bamu sha wani wahalar yunwa ba,
ana kiran sallar magriba muna isa ciki Abuja,
yanayin gosulo da muka tarar bamu shiga gida ba sai bayan sallar isha.
koda ya gyara parking na bu蓷e marfin motar na fito,
ina saka kafata kasa naji wani jiri ya fisge ni, da sauri na dafa jikin motar, har yafita ya zaga ya蓷au ki Naseem da Nasmah ina dafe da jikin motar,
yazo in da hake yana gyara rukon su yace
"Muje ko?."
a hankali na mike tsawo na yayi gaba nabi bayan sa a hankali ina jin yan da jirin yake ta cigaba da fizgata, a haka muka shiga ciki direct sama ya haura, niko a parlour'n kasa na zube kan kuje ra, tare da kife fuskata jikin pillow'n kujera, na rumtse idanuna da karfi jin juwan nada蓷a fisga ta.
ya kai su 蓷akin su ya kwantar da su kana ya sauko kasa yazo in da nake ya zauna kusa da ni.
yasa hannunsa ya 蓷ago ni yana fa蓷in
"Shi yasa nace mukwana a cikib Jos sabo da nasan zaki wahala, kika ce sai dai mu juyo, kin ga irin ta ko."
murmushin karfin hali nayi dan yanayin da nake jin yana son wuce tunani nace
"To baga shi mun dawo ba, ai mun huta basai goben mun yi ta tunanin kuma hawa hanya ba"
Yaruko lips 蓷ina yace "Wannan baki da duk abin da aka fa蓷a sai yakawo hujja".
dariya nayi nace "To ai rainon ka ne."
shima dariyar yayi yace
"Au haka zaki ce."
gira na 蓷aga ina murmushi. gefen fuska ta ya shafa kana ya ruko hannuna yace
"Taso na taimaka miki mu haura ki wasa ruwa zaki ji karfin jikin ki."
a hankali na蓷an yunkura ya 蓷ago ni ya mikar da ni, idanuna na 蓷an rumtse kana a hankali nashiga 蓷aga kafata, yana tallafe da ni har muka haura sama.
a bakin gado ya zaunar da ni kana ya shiga taimaka min na rage kayan jikina,
ya kuma ruko hannuna muka muka shiga bayi wankan ma sai da ya taimaka min gaba 蓷aya jikina ba kwari ga jirin nan yaki bari na, ga masifaffen ciwon kai.
muna fita daga bayin doguwar rigar bacci kawai na zura na haye gado.
bakin gadon ya zo ya shafo gefen fuskata a hankali na bu蓷e idona na zuba masa yace
"Kyakkyawa ta tashi ki蓷an ci wani abu mana zaki da蓷a jin karfin jikin ki."
kai na girgiza a hankali na mai da idanuna na rufe, ya hayo gadon ya kwanta tare da janyo ni kijin sa, a hankali bacci ya 蓷auke ni...
can cikin dare jikina yaha蓷a zafi rau sai 蓳ari nake,ina da蓷a shigewa cikin jinin sa,
da sauri yabu蓷e idanunsa ya da蓷a rungumo ni jin yan da jikina ya 蓷au zafi yamike da sauri yana fa蓷in
"Subhanalla kyakkyawa ta zazza蓳i ne haka Innalillahi."
gaba 蓷aya ya ru蓷e yarika rungume ni yana yimin sannu, ya 蓷ago ni yana fa蓷in
"Taso muje asibiti jikin ki yayi zafi sosai."
kaina na kwantar a kirjin sa na rirrike sa a hankali nace
"A'a dare yayi sosai kada muje zai sauka zuwa safiya."
a ru蓷e yace "A'a kyakkyawa ta kijin ki yayi zafi sosai muje kawai."
duk yan da yaso mu tafi naki fir.
yana zaune ina rungumo a jikin sa a haka gari ya waye.
da asuba ya kaini bayi da kansa yayi min wanka a daddafe nayi al'wala shima yayi, bai barni na taka da kaina ba ya 蓷auko ni ya fito da ni,
ya shinfi蓷a mana sallaya a zaune nayi sallar in da shi kuma ya ja mana sallar.
muna idar wa na sulale kan sallayar.
shiko da sauri ya mike yaje ya 蓷au wayar sa yakira family Dr su, yace yazo yanzu yayi masa kwatancen gidan.
kana yazo ya 蓷aga ni a kasa ya mai dani kan gado.
batare da 蓳ata lokaci ba Dr ya iso, ya bada umurnin a barsa ya shigo,
har cikin parlour'n sama ya bashi umurnin shigo wa,
kana ya shigo ya saka min hijabi kan rigar baccin da yake jikina, ya 蓷ago ni ya tallafo ni jikin sa muka fito parlour, ya zaunar dani kan kujera kana shima ya zauna kusa da ni,
a hankali na kwantar da kaina jikin hannun kujera, ina jin Dr yana tambayar me ya sa me ni,
yace masa tafiya mukayi jiya mun wuni a kan hanya,muna dawo wa shine zazza蓳i ya rufe ta.
Dr ya 蓷anyi rubuce-rubuce kana ya蓷a go yace "Baza a bata magani ba sai anyi mata test." Ahmad
yace "To." kana ya dube ni yace
"Bari a ja jinin ki ayi test dan asan maganin daya dace da kisha ki warke da wuri ko kyakkyawa ta."
yayi maganar yana 蓷an jan hijabin jikina ya 蓷an tattaro shi yaciro hannuna ya ruko hannuna.
Dr ya taso yaja jinina kana ya tafi.
in da aka ja jinin yarika mulmula min a hankali,
shiru nayi ina kwance cikin kirjin sa, a haka bacci ya fara fizgata,
ganin haka sai ya gyara zaman sa da kyau ya gyara min kwanciya ta cikin jikin sa.
nan da nan bacci ya 蓷au ni...
Chapter 55 · 0% Book details