← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 93

Sashe 71

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 10 min read

A 蓳angaren Na'ima kuwa
zaune suke a gaban sabon bokan su, sun na蓷e kafa gaban sa kamar masu niman gafara,
sun kura ido suna kallon yan da yake ta wani surkullen sa, yayi zane kan kasa ya bubbuga ya share ya kuma zana wa.
bokan ya 蓷ago ya dube su yace "Zata mutu mutuwar wulakanci amma aljanun da zamu tura su sun ce suna bukatar jini rakuma kosassu guda goma kafin suje suyi ai kin."
kirji Raliya ta buga tace
"Rakuma guda goma kosassu ayanzu fa ku蓷in ko wani 蓷aya zai kai miliyan uku."
bokan yayi wani irin dariya yace "Bazaku iya ba ku tashi ku tafi."
da sauri
Na'ima ta gyara zama tace "Boka zamu iya."
wayar ta ta 蓷aga taduba balance 蓷in account 蓷in ta taga babu wani yawa sosai dan duk ta gama basa ku蓷in.
ta yi masa transfer 蓷in duka ku蓷in zuwa account 蓷in shi, kana ta aje makullin motar da tazo da shi a gaban sa tace
"Asai da motar a ha蓷a da ku蓷in idan basu kai ba zan nemo cikon,
ni dai dan Allah boka ayi min kokari bana so a sami matsala, a iashe ta kawai shine samin kwanciyar hankali na, ko bacci mai da蓷i bana samu yanzu."
boka yace "An gama mabi da matsala yau za'a sai da motar idan ku蓷in ya cika, da daddare za'a bawa aljanu jinin rakuman a daren nan zasu kashe tai, dan kuma bai cika ba zamu neme ku."
suka mike suna ta zuba masa godiya a motar Raliya suka fito saga cikin dajin..
suna tafe Raliya ta juyo ta dube ta tace
"Aminiya amma yanzu idan boka yace a kawo ciko a ina zaki samu cikon?."
Na'ima tace "Agurin SALEEM ai da ma daga gurin sa suke fita, zan sa a 蓷auke Ameer a nimi ku蓷in fansa a gurin sa dai-dai ku蓷in siyan rakuman, idan ya bayar sai na bawa boka cikon ku蓷in narike sauran."
dariya Raliya tayi tace
"Kai Aminiya da蓷ina da ke kwakwalwar ki na ja, idan aka sace 蓷an sa kam ai da gudu zai kawo ku蓷in babu gargada."
Na'ima tayi wani murmushi mai cike da tarin makirci....

Abuja
Kullum a cikin lissafin tafin watannin ukun da Ummi tace na kara kafin nazo nake, sai nake ganin lokacin yayi min nisa. da kyar naga wata biyu yayi.
kullum idan muka yi waya da Ummi sai na ce mata
Allah Ahmad yayi wayo sosai yayi kwari nace kuma bari taji dariyar sa, sai nayi ta masa wasa yayi ta kyalkyalewa da dariya nace taji shi ko.
tace taji amma dai na bari na cikita wata 蓷ayan tukun..
idan Ahmad yaji muna waya da Ummi yarika yimin dariya kenan sai yace wai Ummi ta fiso na zauna na kula da su..
ranar da wata 蓷ayan nan ya cika, tun da na farka da asuba ban kuma iya komawa bacci ba,
a kwatunan kayan mu na sauke wa蓷an da na shirya su tun sati 蓷aya daya wuce.
ranar Ahmad baya gida na, na kira sa a waya nace kasa mu fa mub gama shiri, yace na jira sa gashi nan zuwa.
ina zaune a parlour ya shigo su Nasmah suka rungume sa suna yi masa oyoyo, sai da ya 蓷aga ko wannen su sama kafin ya dire su yana bin su da dariya.
in da na ke ya karaso ya 蓷auki Ahmad karami dake kan kafata yarika cillashi sama yana kwalkwale dariya,
ganin yan da ya shagala da wasa da yaron yana kuma biyewa su Naseem da suke taya sa wasa wa yaron, na turo baki gaba
nace "My rana fa zatayi kana so muyi tafiyar dare ne."
zama yayi gefe na tare da manna min kiss a kumatu yace
"Kyakkyawa ta ki bar tafiyar nan yau."
ido na waro nace "Me ne!?."
janyo keken da ake saka Ahmad karami a ciki yayi yasaka sa ciki kana ya tura sa gefe ai ko da gudu su Naseem sukayi kansa suna yi masa wasa yana ta 蓳alle musu da dariya.
janyo ni jikin sa yayi ya sakalo hannayen sa ya zagaye ni da shi,
a hankali cikin tattausan lafazi yace
"Ki saurare ni kiji abin da zan fa蓷a, ai tafiyar ba naki ke ka蓷ai bace har da ni da su Bappa,jibi ina da wani zaman da zamu yi kuma mittin ne mai muhimmanci, nayi miki al茩awari idan mukayi mittin jibi washegari zamu tafi."
kai na langwa蓳ar gefe zan yi magana yace
"Kar kice komai kika iya jiran wata uku kwana uku ne zai gagara iye kyakkyawa ta?."
yadda yayi maganar a marairaice tare da langwa蓳ar da kansa gefe,
sai ya bani dariya murmushi nayi nace
"Amma Allah kwana ukun nan kam idan yazo babu fashi."
yace "In Allah ya yarda."
kai na girgiza nace "To Allah ya kaimu."
da蓷a rungumo ni yayi yana fa蓷in
"Amin Amin." ganin yana shirin ha蓷e bakin mu nayi saurin kawar da kaina gefe, nace
"My yarannan fa suna nan." ido ya kashe min yace "Su da suke wasan su hankalin su baya nan."
fuska ta ya juyo tare da ha蓷e bakin mu, idanunsa a kan yaran garin hankalin su na kokarin dawowa kanmu sai ya zare bakin sa ya sake ni,
ya mike yana fa蓷in
"Kuzo muje musha ice-cream."
ya 蓷auki Ahmad karami ya dube ni yace
"Madam muje ko."
a sannu na mike kasan cewar da mayafi a jikina muka nufi gurin mota.
ya bu蓷e wa su Naseem gidan baya suka shiga, kana ya mai da marfin ya rufe sannan ya matso ya bu蓷e min gefen mai zaman banza, sai da na shiga kafin ya miko min Ahmad karami.
kana ya zaga ya hu蓷e driver seat ya shiga, yana kokarin ta da motar da sauri wani security ya iso,ya蓷an leko gefen da nake cike da girmamawa yace
"Barkan ku da warhaka."
Ahmad ya ce yauwa, yace "Madam dama wata ce ta zo, wai tazo niman taimako ne ansan da zuwan ta ne."
kai na girgiza nace
"Okay bari idan muka fita wajen sai a taimaka mata."
yace to ya juya da sauri mai gadi ya wangale get muka, Ahmad ya ja motar muka fito a hankali.
matar tana 蓷an raku蓳e a gefe kallon ta nayi saga sama har kasa, gaba 蓷aya kayan jikin ta sun ko蓷e hatta hijabin jikin ta tagefe duk a yayyage, silifas 蓷in kafar ta ya cinye kusan rabib kafar ta a kasa yake, tana rungume da bakko a hannunta.
Ahmad yayi hon da 蓷an sauri ta nufo in da muke,
ido na kurawa matar,
da sauri na kai hannu na mussuke idanuna da kyau na zuba su a kanta, dai-dai lokacin da ta karaso jikin motar tagefen da nake tana fa蓷in
"Alhaji Hajiya a taimaka min da ko ku蓷in mota ne na koma garin mu."
wani irin waro ido nayi da karfi na furta
"Mama!". ta 蓷ago da sauri ta na duba na,
juyo wa nayi gun Ahmad ina fa蓷in
"My ita ce Mama mai wara ita ce wlh."
sai kuma na juyo in da take ganin tana bina da kallon rashin sani nace
"Mama baki gane ni bane nice fa HAMDAH ce fa Mama."
da sauri na 蓷ago Ahmad karami na 蓷aura kan kafar Ahmad na bu蓷e marfin motar da sauri na fita.
ido ta kura min tana nuna ni da yatsa murya na rawa tace
"HAMDAH kece HAMDAH kece haka ke kika zamo haka HAMDAH?."
rungume ta nayi a tare muka fashe da kuka cikin muryar kuka nace
"Nice Mama, Mama nayita niman ki har na 蓳ata."
ita ma tace "Nima nayi ta neman ki HAMDAH ashe darabon ganawa."
Ahmad ya fito daga cikin motar, na sake ta tare da share hawaye na na nuna mata shi nace
"Mama miji na ne shi." murmushi tayi tana share hawaye tace
"Shine SALEEM?." kai na girgiza mata. Ahmad da take ta binmu da murmushi yace "Sannu Mama." tace yauwa.
tace "Ina Naseem da Nasmah?." nace "Gasu nan cikin mota."
Ahmad ya bu蓷e musu suka fito na kamo hannun su na kawo su gaban ta nace
"Ga Mama wacce tasha 蓷awainiyar ku tun kuna ciki."
hannunsu ta ruko tana fa蓷in
"Masha Allah Naseem Nasmah kune kuka girma haka."
Naseem da ya washe baki yace
"Ai Daddy yace mun gima ga kanin mu a hannun Daddy ni Yaya Naseem ne."
dariya dukan mu kayi, Mama ta dubi Ahmad karami da ke rike a hannun Ahmad sai washe baki yake kamar wan da yasan abun da ake fa蓷a,
tace
"Masha Allah kanin ku kenan yaya sunan sa?."
Nasmah tace "Ahmad."
nace "Mama mu shiga ciki."
tana rike da hannun su Naseem muka shige cikin gida, Mama ta rika bin katafaren gidan da kallo tana jinjina kai.
a parlour'n kasa muka zazzauna, Ahmad cikin girmamawa yashiga gaishe ta da taya mu murnar kuma ha蓷uwa, ya dube ni yana murmushi yace
"Yau maganar Mama ya kare ko." dariya nayi ina 蓳oye fuska ta a jikin ta.
kira ce ta shigo wayar sa ya mike yafita yana fa蓷in sai ya dawo.
da kaina na fita naje side 蓷in su Bappa na sanar musu da zuwan Mama mai awara.
a tare muka shigo parlour'n da su.
sunyi farin ciki kwarai da gaske ha蓷uwar mu da ita, cikin yanayin damuwa Mama ta dube ni tana fa蓷in
"HAMDAH ke da na ce miki ki jira ni ina dawowa shine kika tafi."
nace "Mama nayi ta jiran ki da banga kin dawo ba shine nace zan biki kawai, a hanyata na tafi Yola na shiga motar 蓷an yankan kai."
ido Mama ta ware tabuga kirji tace
"茒an yankan kai kuma?."
kai na gwa蓷a kana asannu na shiga bata labarin abun da ya faru daga lokacin da na shiga motar 蓷an yankan kai 蓷in nan har zuwa rana mai kamar ra yau.
mama ta rika hawaye cike da tausayawa halin da muka shiga bayan ta,
da ga bisa ni kuma tarika murmushi jin nasarorin da na samu bayan wuyan da muka sha.
nace mata na zo Jos domin neman ta wacce nake da tabbacin zan sami labarin ta wajen su wato Zainabu da mijinta Malam musa mai maganin macizai, na tarar da sun tashi a gidan dan dana sansu.
Mama tace "Nima lokacin da nadawo dan da 蓷auke ki mu tafi na tarar da bakya nan, nayi tunanin naje Bauchi ko kin koma gun iyayen ki ne, nayi tunanin ban san ta in da zan fara niman ki ba tun da bakara min gari bane,
haka na koma Yola nayi ta rayuwar kunci 蓷an gonar gado na da nake gadara da shi matar yaya na ta saida wai gadon 拼a拼an ta ne."
kwalla ta share kana ta cigaba da bani labarin rayuwar da ta fuskanta a can, da kuma abun da ya kawo ta ganinnan, tace niman ai ki tazo yau satin ta guda kenan, bata sami ai kin ba duk gidan da ta shiga wasu su kore ta wasu kuma suce basa bukatar 拼ar aiki suna da su,
haka tayi ta kwana a kan titi shine ta fara yawon bara dan ta sami ku蓷in mota ta koma Yola taje ta karasa rayuwar ta acan.
rungume ta nayi tare da fashe wa da kuka, mukayi ta kuka.
su Bappa ne suka yita bamu baki har mukayi shiru,
kana Nappa yayi ta kwararo addu'a yace
dama duk abun da yayi farko zaiyi karshe Allah ya tsayar mana haka.
duk kanin muka amsa da amin amin, sai da sukayi hira sosai da Mama mai awara kafin suka koma side 蓷in su...
蓷akin da Ummi ta zauna na kai Mama nace tashiga bayi yayi wanka,
tare muka shiga na nunnuna mata in da zatayi amfani da bathroom 蓷in kafin na fita.
waya nayi a *HAM'NAS* Store Camplex
nace a kawo min manyan dogayen riguna ha蓷e da atamfofi da mayafai da takalma marasa tudu, nafa蓷i lambar takalmar da kuma adadin yawan kayan da nake so.
batare da 蓳ata lokacin ba motar ShopRite 蓷in ta iso, da kaya niki niki cikin babbar jaka.
na shiga da shi cikin 蓷akin da Mama take, lokacin har tayi wanka tayi salla tana zaune a kan sallaya,
a gaban ta na aje jakar na zazzage kayan, na cire atamfofin gefe nace ta kwada dogayen rigunan ko zasu yi mata in basuyi ba aje a canzu.
ta gwada zukayi mata Mama ta rika samun albarka tana hawaye.
na kira tela yazo ya ganta kana ya 蓷ibi zannunwan ya tafi da su,bayan na sanar masa cikin kwana biyu nake bukatar su...
muna zaune da Mama a parlour bayan mun gama cin abincin dare na kira Ummi bayan mungaisa nace
"Ummu ga Mama mai awaran da nake fa蓷a miki wacce ta rike ni tamkar ke da kika haife ni."
Ummi tayi ta murna tace na bata wayan su gaisa, nace to tare ma zamu zo.
bayan sun gaisa Ummi tashiga zuba mata godiya,
Mama tace ai ba ita ka蓷ai bace Mama ta itama Mama ta ce.
Ummi taji da蓷i kwarai da gaske tayi mana fatan isowa Bauchi lafiya...
bayan kwana biyu tela ya kawo 蓷in kin Mama, na ha蓷a na shirya mata wasu daga cikin kayan cikin 蓷an madaidaicin akwati..
Chapter 71 · 0% Book details