← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 93

Sashe 57

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka suka yi ta nuna farin cikin su kamar zasu saka ni cikin jikin su.
suka rika tambaya ta me nake so, Aunty Rasheedat tace me nake jin kwa蓷a yin sa ta dafa min. nace ba komai.
kan kace me labari ya kara蓷e yan uwa da abokan arziki.
ranar wuni Aunty Rasheedat tayi a gidan sai dare ta koma.
washegari
washegari da sassafe Ahmad yaje gidan su,
yau 拼an gidan sun sha mamakin ganin yan da yashigo da farara hatta Sakeenat yau sai da ya amsa gaisuwar ta.
蓷akin Hajiya Karima ya shige, tana ganin sa ta fa蓷a fuskar ta da murumshi.
ya nimi guri ya zauna bayan sun gaisa ya dube ta fuska 蓷auke da masananciyar farin ciki
yace "Hajiya wani albishir nazo miki da shi."
zama Hajiya Karima ta gyara ta washe baki tana fa蓷in
"To Ahmadu 蓷an Sabil na bada goron kar 蓳ar albashir fari soll."
yace "Hajiya HAMDAH nada ciki Hajiya ashe nima zan haihu?."
wani irin zabura Hajiya Karima tayi, sai da ta zamo bakin kujera ta buga kirji ta waro ido tare da fa蓷in
"Me ne ciki!!?." wani irin murmushu yayi mai kunshe da ma'anoni daban-daban kana yace Hajiya kema kin ji abin a bazata ko? ai nima haka naji abin kamar almara."
dariyar yake tayi sai kuma ta kama kame-kame tashiga fa蓷in
"La..laa..ikon..Ikon.. Allah...to ciki..
ciki, kai masha Allah lallai kuwa wannan shine bazata bayan fidda rai ga samu sai ga samun kuma, kai amma nayi farin ciki naji da蓷i sosai, ashe zanga jika na, kai Allah yayi albarka yaraba lafiya, Eh Allah ya raba lafiya."
"Amin amin." yafa蓷a yana mike wa tsaye yace
"To Hajiya ni zan koma."
tace "To a gaida gida a gai da min me cikin."
yace to kana ya sa kai ya fita..
yana fita Hajiya Karima ta saki wani uban ajiyar zuciya tabigi kirji tace
"Tab蓷ijam ciki!? kenan hakan na nufi Ahmad zai haihu yasami magajin dukiyar sa, wato wannan shigiyar yarin yar tana kokarin zuguza min shiri shine har da yin ciki, bayan ban ta蓳a kawo hakan cikin lissafi na ba, nasawa raina bazai haihuwa ba shine zata zo ta yi kokarin haihuwa masa, ina bazai yiwu ba da sakel wlh!...."

Acan cikin garin Bauchi

Abba ne da Ummi tafe cikin mota a hanyar su na komawa gida bayan dawo war su daga asibiti dubiyar wata 拼ar uwar Ummi da ba lafiya,
suka biya ta gidan mai domin su sha mai,
tun daga farkon shiga gidan man layi ne har cikin gidan man,
Abba da yake kokarin sako kan motar sa cikin gidan man ya蓷an yi jim yana bin layin da ido.
Ummi tace "Abba'n Fauzan wannan layin idan muka shiga ai sai mukai kisan dare ma layin bai iso kan mu ba, duba fa gamasu garaku da suke acikin motoci sannan ga su motocin kansu, yaushe za'a basu har a bamu."
Abba yace
"Gaskiya kam bari mu koma gida kawai nasa direba yafito ya sha man ko ba a nan ba, tun safe ake layin nan motoci sai da蓷a zuwa suke zamu 蓳ata lokaci kam muje gida kawai."
Ummi tace "To in ban da mutane ma ga wasu gidajen mai da yawa wa蓷an da naga babu ko layi wasu bai fi mota biyu zuwa uku ba, baza su je can susha man ba sai suzo nan suyi tayin layi haka."
Abba yace "To ai sauki ake so shiyasa ake wa gidan man layi, ai ba nan ka蓷ai ba idan da zaki zaga garin nan kiga gidan mai me irin sunan wannan gidan man zakiga layi kamar haka koma fin haka,
man su na da sauki sosai kuma litar su na da kyau,
an ce wai mai gida jen man ne tace a rika sai da shi a farashin da yanzu suke sai dawar shiyasa duk gidajen man ta zakiga irin wannan layin."
kai Ummi ta jinjina ta 蓷aga kan ta tana duban sunan gidan man. tace
"*HAM'NAS CO PETROLEUM NIGERIA LIMITED* wato mace ce mai gidan man?".
Abba daya juya akalar tafiyar tasu izuwa gida yace "Eh mace ce."
tace "Lallai tayi kokari Allah yasaka mata."
Abba ya amsa da amin amin.
suna isa gida motar SALEEM na shigo wa, w kusan tare sukayi parkin suka fito,
ya tako ya zo in da suke ya shiga gaida su,
suka amsa cike da kuwala Ummi ta蓷an zuba masa ido nan da nan ta hango 拼ar karamar ramar da yayi, ta dube shi da kyau sannan tace
"SALEEM baka da lafiya ne kam?."
kai ya girgiza batare da yayi magana ba.
tace "Ai ho nazaci baka da lafiya ne dan naga ka蓷an fa蓷a ka蓷an."
Abba yace
"Wata kila hidimar office ce ta sashi a gaba kin san shima yana sa haka idan ka rasa nitsuwar ka."
Ummi tace "Haka ne Allah yasa mu dace."
suna nan tsaye motar Abbu yashi gidan, koda ya gyara parking yafito duk kanin su gaishe sa sukayi ya amsa, in da ya amsa gaisuwar SALEEM a sama-sama kana yayi gaba Abba ya bi bayan sa.
SALEEM kuwa motar sa ya shige yabar idan, Ummi kuma ta wuce side 蓷in ta.

Parlour'n da su Abbu suke zama su蓷an tattauna nan suka wuce, suka zauna suna 蓷an tattauna lamuran su.
Abbu ne yamai da hankalinsa kan TV yana sauraran labaran almuru da ake gudanar wa a wannan lokacin, in da ake sanar wa kan manyan masu ku蓷i da suke bada taimako da tallafi ga marasa karfi, jinjina kai yayi jin ta in da taimakon ya fito yace
"Kai wannan matar Allah dai ya saka mata wlh tana da kokari sosai, ko wancan satin ma naji kalar taimakon da tayi na dubban nin 蓷arurruwan ku蓷i ga mara sa karfi,
in dai za'a cigaba da samin irin su a Nigeria ai kasar mu zata cigaba ba 蓷an ka蓷an ba,
dubi yan da take ta bada mai kamar kyau ta a cikin gari Allah dai ya kara mata bu蓷i."
Abba ya amsa da "Amin amin ai Yaya ko yanzu ma bakaga layin da ake yi a gidajen manta ba irin su kuma kullum bu蓷e suke gani ba ci baya ba."
Abbu yace
"Kwarai da gaske Allah ya da蓷a bu蓷a mata."
hirar suka cigaba da yi har sai da aka kira magriba kafin suka nufi masallaci.
bayan sallar isha da Abbu ya tafi side 蓷in Mamie hirar matar yayi ta mata da irin kokarin da take,
sukayi ta sanya mata albarka da dukiyar ta.....)

Abuja

Zaune muke a parlour ni da su Naseem Aunty Rasheedat tayi sallama da kaya niki niki a hannun ta, Zulai da Talatu na biye da ita 蓷auke da wasu kayan,
ta Suka dire shi sakiyar parlour,
na dube ta da蓷an mamakin ganin ta da manyan laidadi nace
"Sannu da zuwa Aunty Rasheedat."
tace "Yauwa HAMDAH ya nauyin jiki?."
murmushi kawai nayi dan nidai bana jin wani nauyin jiki cikin da bai girma ba ake tambayar nauyin sa.
zama tayi gaban kayan kana ta shiga ciro su cikin manyan laidodin kayan baby ne kala-kala a ciki ha蓷e da kayan wasa,
da gudu su Nasmah suka je in da take Naseem daya 蓷ago wani abin wasan baby yace
"Mamy kin kawo mana ne?."
Kuma tun sa ta ja tace
"A'a zan kawo muku naku wannan na baby'n ciki ne, baku san Mommy zata samo mana yaro ko yarin ya ba."
tsalle sukayi cike da murna suna fa蓷in
"Yeee Mommy zata samo mana yaro."
Nasmah ta dubi Aunty Rasheedat ta dafa kafa 蓷ar ta tace
"Mamy yaushe Mommy zata samo mana?."
yatsun ta shida ta nuna mata tace
"Saura wata haka ta samo nama."
tsallen murna tayi tazo in da nake da gudu tace
"Mommy guda haka zaki samo mana yaro."
ido na waro ganin ta 蓷aga yatsun ta biyar tana yimin nuni da su nace
"Akuya ce ni."
dariya Aunty Rasheedat da Talatu da Zulai sukayi, Talatu tace
"Ai ba akuya ka蓷ai suke haifan biyar ba idan Allah ya nufa sai kiga an haifo biyar 蓷in."
kai na girgiza nace "Ba amin ba wlh."
dariyar suka kuma.
Aunty Rasheedat tace "Muna so ko goma ne ma Allah yakawo su masu albarka."
ido na kuma waro wa ina fa蓷in
"Lallai ma."

茒akin kayan wasan su Naseem tasa su Sulai suka kwashe kayan da tazo dashi, suka kai cikin 蓷akin suka jibge shi a gefe.

Bayan wata 蓷aya.........!

Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:57 - Ummi Tandama馃槆: 27

Tun daga ranar da Ahmad yasami labarin ina da ciki, bai sake barina nayi wani abu da kaina ba.
ko wan ka baya bari na nayi shi yake yi min da kansa, ko naki nace ya bar ni nayi da kai na sai ya ce
bai isa na janyo masa a sara ba, shi da kan sa zai min.
koda six yake da ni a hankali yake bi da ni.
tun da Dr ya bashi shawarwari game da cikin kan abincin da zan rika ci,sabi da lafiya ta da ta abin da ke cikin. shike nan ya hana ni sakat da cin abinci.
a rana sai yabani naci abinci kusan sau goma, dan yanzu idan ya bani naci anjima ka蓷an zai kuma kara min.
yanzu kullum muna tare da shi ko yana gida na ko baya gida na,
idan yana gidan sa da sassafe zai zo bazai koma ba kuma sai dare.
washegari kuwa zai kuma dawowa da sassafen...
Chapter 57 · 0% Book details