← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 93

Sashe 30

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga can waje nake jiyo muryar su Bappa ina kokarin mike wa suka turo kofar, Bappa na gaba Inna Wuro Faty Yakubu da Sule direban su Bappa, suka shigo.
hankali tashe Bappa yake fa蓷in
"Subhanalillahi garin yaya me ya same ta haka?."
dai-dai nan suka karaso bakin gadon da Nasmah take kwance.
Bappa ya leko fuskar ta yana cigaba da fa蓷in
"Amma ta farfa蓷o ko."
Ahmad ya ce "Eh ta farfa蓷o yan zu dai bacci take."
"Masha Allah, kaji ikon Allah ko yarin ya tabar gida lafiya sai kuma ga ciwo, kai sannu Nasmah."
Inna Wuro ta fa蓷a tana shafa kanta. Bappa ya dubi Ahmad yana fa蓷in
"Sannu Ahmad sannu fa da kokari Allah ya saka da alheri."
murmushi yayi kana suka
shiga gaisawa, bayan gaisuwa da jajen abun da yafaru Bappa ke fa蓷in
"Wai haka kawai ta suma kuma me likita ya ce ke da mun ta?."
Ahmad da idanun sa ke kan Nasmah dake ta baccin ta har yanzu kana ya ce
"Typhoid ne har yayi mata (C) da mamaki ace wai ciwo irin haka har yayi yawa a jikin yaro irin haka ba'a sani ba, har yakai matakin da zai iya sumar da ita wai duk ba'a sani ba."
Bappa ya ce "Ikon Allah amma kuwa abun da mamaki, wai da ma bata da lafiya ne HAMDAH? ko irin zazza蓳i a tsatstsayen nan ne take?."
ya karasa maganar yana duba na. da sauri ganin yan da wannan Ahmad 蓷in yake taso ya mai da alhakin ciwon ta kaina.
na ce "Lafiyar ta lau bata kuma zazza蓳i a tsatstsaye."
"Kuma bata ta蓳a ce miki wani gurin ta na ciwo ba, yaro ke nan Allah sarki kuma kema baki ta蓳a lura da yanayin ta ya sauya ba."
cewar Inna Wuro, tayi maganar cikin jimami da alhinin ciwon nata.
"Babu wani alamar da na ta蓳a gani na ciwo tattare da ita, kuma bata ta蓳a cemin wani gurin ta na ciwo ba, in ban da shekaran jiya da nake
kwance kai na na ciwo ita ma tazo ta ce min kanta na mata zafi, kuma nasan a lokacin 蓷in dan nima na ce kai na nayi min ciwo ne shi yasa ita ma ta fa蓷a."
nakarasa maganar ina 蓷aga hanci sama dan ganin yan da 蓷an shishshigin nan keta wani girgiza kai. da sauri na mai da idanuna kan sa jin yana fa蓷in
"Ashe dai ta ma fa蓷a miki bata da lafiya amma bakiyi serious a kai ba, dan ta fa蓷i kan ta na zafi lokacin da naki yake ciwo sai ya zama nata karya ne?,
taya za'ayi ki fahimci hakan tun da baki da wayon sanin haka."
ido na waro baki bu蓷e jin yakuma jifata da kalmar rashin wayo,wai shin wannan mutumin me yake jin kansa ne,shi ji yake yafi kowa wayo kowa yi masa kallon rashin wayo yake?.
a kufule na bu蓷i baki zanyi magana, Bappa ya katse ni da fa蓷in
"Ai shi yaro idan ba lura kayi da yananin saba wani 蓷an bashi da azancin fa蓷ar abun da ke damin sa, ko da yana jin wani gurin sa na ciwo, sai dai in kai ka gane hakan daga yanayin sa na yau da kullum, kirika lura da yanayin su tanan zaki rika fahimtar ciwon su,
Allah sarki da gaske kan nata nayi mata ciwon ne sai tace yana yi mata zafi, Allah yabaki lafiya Nasmah."
Amin duk aka amsa da shi, baki na tura gaba muna ga蓷a ido dashi na murgu蓷a masa baki, wani murmushi ya sake sai da dimple 蓷in sa suka bayyana,ya mai da idanunsa kan Nasmah yayin da fuskarsa ke nan 蓷auke da murmushin nan.
ido na 蓷an kurawa fuskar sa wan da dimple ya da蓷a kawata shi. baki na ta蓳e ina mai 蓷auke idanuna a kansa...

Muna nan cikin 蓷akin kiran sallar azahar ne yasa su Bappa fita dan zuwa masallaci, har da shi, yarage daga ni sai Inna Wuro da Faty.
Inna Wuro ta shiga toilet 蓷in cikin 蓷akin ta yi al'wala tafito tace da ni naje nima nayi muje masallacin cikin asibitin muyi sallah, tun da ga Faty in muka dawo sai itama taje tayi... muna isa masallacin ana idar da sallah, su mazan suka koma ciki mukuma muka shige cikin masallacin.
ko da muka idar muka koma ciki, abakin gadon na kusa da Nasmah in da 蓷azu yake nan yanzu ma yake zaune.
zaman mu baifi da minti 20 ba akayi knocking 蓷in kofa, Yakubu dake tsaye ta kusa da kofar yabu蓷e.
wasu maza guda biyu suka shigo niki-niki da kayan abinci duk kanin su sanye da rigonan irin na ma'aikatar hotel.
cikin girmamawa suka shiga gaida Ahmad kana suka gaida 拼an cikin 蓷akin, suka dire manyan basket 蓷in dasuka shigo dashi, nan suka shiga zuba abinci suna mikawa kowa, da mamaki nake kallon su dan nidai a sani na ban bada umurnin kawo abinci daga wani hotel ba.
maganar 蓷aya daga cikin mutanen naji ya na fa蓷in
"Gashi hajiya." 蓷ago idanuna nayi daga kan wayar da nake natsawa na dube shi, plt 蓷in abinci yake miko min, kai na girgiza tare da fa蓷in
"Nakoshi."
"A'a me kikaci HAMDAH nasan tun fitar ki ba abin da kika ci."
cewar Bappa yana duba na.
"Bana jin yunwa." nafa蓷a ina mai da idanuna kan wayar. "Zama da yunwa bashi da amfani wan da gashi komai yazo da sauki kici abinci itama bakiga tana baccin ta ba, sauki ce ke samuwa cikin bacci insha Allah."
Inna Wuro ta ce "Insha Allahu kuwa lafiya nata kan samuwa."
ni dai ban kuma cewa komai ba,
plt 蓷in abincin suka mikawa Faty dake kusa da ni.
wani 蓷an ma dai-dai cin basket daga cikin wa蓷an da suka shigo da su, abincin cikin sa na musamman shi suka zuba masa suka mika masa hannu ya daga tare da fa蓷in
"Akarawa kowa yaci."
Bappa da yakai loman abinci yaha蓷i ye ya ce "A'a Ahmad ai wannan ma ya ishe mu maza kar蓳i ka ci wannan ya ishe mu haka ga abibci nan idan bamu koshi ba duk zamu kara, Allah ya saka da alkhairi an gode sosai Allah yakara bu蓷i."

Jin yan da Bappa yake ta zuba masa godiya yasa nasan cewa shi yayi odar abincin, baki na ta蓳e a raina nake fa蓷in
"Sai kace ance masa bamu ci abinci bane ko yunwa ke damin mu."
wayar sa ce tayi kara yamike yafita batare da ya kar蓳i abincin ba,
Bayan sa nabi da kallo
"Gulma shi da yasa a kawo dan tsabar gulma shi ne yaki ci to da waya mai da mayunwata."
Faty dake daf da ni ta juyo tare da fa蓷in
"Adda HAMDAH me kika ce?."
"A'a bada ke nake ba da wancan 蓷an gulmar nake."
"Wafa?." ta fa蓷a tana kallon wa蓷an da suke cikin 蓷akin.
"Ba kowa." na fa蓷a ina mai da idanuna kan waya.
tun da ya fita bai dawo ba ganin ya jima sosai bai dawon ba yasa nayi tunanin ya tafi ne, gara ma ya tafin 蓷an shishshigi.
har wajen la'asar muna nan zaune Nasmah bata farka ba zuwa lokacin kam bakin gadon na dawo na zauna. akai-akai likitoci ke zuwa duba ta, tun bayan fitar sa.
ana kiran sallar la'asar su Bappa suka fita bayi Inna Wuro ta shiga ta 蓷auro al'wala tafito ta shinfi蓷a sallayar da nasa Yakubu ya 蓷auko a mota, ina nan zaune kusa da Nasmah da har lokacin take ta kan bacci, ido na tsura mata gaba 蓷aya yanzu na kagu ta farka. na 蓷au alwashin duk likitan da yakuma zuwa zai saka wani allura cikin drip 蓷in dake shigan ta zan hana, dan na lura kamar shi ke da 蓷a sata cigaba da baccin. ban tashi ba har sai da Faty ta idar da nata sallar, kana nashiga toilet 蓷in room 蓷in bayan nayi al'wala nazo na gabatar da salla.
ko da na idar ina nan zaune kan sallayar ina lazumi,da sauri na 蓷ago kaina jin Inna Wuro tana fa蓷in
"Nasmah kin farka ne?."
da sauri na mike ganin tana 蓷an motsa hannun ta, da sauri Inna Wuro dake gefen ta ta roko hannun nata da aka mata karin ruwa da shi take ta kokarin 蓷aga shi,
cikin hanzarin na iso bakin gadon ina fa蓷in
"Nasmah Nasmah tashi kada ki sake komawa baccin nan."
a hankali ta bu蓷e idanun ta na bin cikin 蓷akin da kallo.
sannu Inna Wuro da Faty suka shiga jera mata.
蓷aya hannun ta na roko da murmushi ganin idanun ta wasai naci gaba da fa蓷in
"Sannu Nasmah kan naki ya dai na yi miki zafin?."
fuska ta kwa蓳e sai kuma ta fashe da kuka.
"Subhanallahi yi hakuri kinji Nasmah yi shiru kinji idan kikayi kuka kan zai ci gaba da yi miki zafin fa yi shiru abin ki."
Inna Wuro ta fa蓷a da alamun rarrashi.
kai na gya蓷a tare da fa蓷in
"Eh kin ji yi shiru abin ki Nasmah." sautin kukan nata takuma karawa tana ta kokarin fizge kannulan da ke hannun.
da sauri ya turo kofar ya shigo , cikin hanzari ya iso bakin gadon. ta gefen da nake ya tsaya tare da ruko hannun ta da hannuna ke kai, da sauri na 蓷auke hannuna dan yan da ya sauke hannu nasa kan nata sai da ya ta蓳a nawa hannun.
蓷an matsawa nayi ganin yan da mukayi daf da juna.
"Shiiit ya isa haka bar kukan nan."
ya fa蓷a yana shafa kanta kana ya 蓷ago wayar sa ya daddanna ya kai kunnen sa "Na shigo." yayi maganar yana sauke wayar.
kan ta yaci gaba da shafawa yana kuma cigaba da fa蓷in
"Yi shiru bari azo a cire miki wannan abun ki huta."
Chapter 30 · 0% Book details